Hotunan yadda Tsaunin Nyiragongo ya rufta a DRC

An wallafa

Dubban mutane ne suka tsere daga muhallansu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo bayan da wani tsauni ya yi aman wuta kusa da birnin Goma.

Aman wutar da dutsen ya yi ya hankada giza-gizan birnin da ke gabashi, wanda ke da yawan mutane miliyan biyu.

Hoton Tsibirin Nyiragongo ranar 22 ga watan Mayu 2021
Presentational white space

Mutane sun yi ƙoƙarin kashe wutar a lokacin da ruwan ya kwarara ya mamaye wasu ɓangarorin birnin da tituna.

Wani mutum na ƙoƙarin kashe wuta a wani gini bayan aman wutar da aka yi da daren 22 May, 2021 a garin Goma

Ana iya ganin wuta a tsakankanin gine-gine a birnin.

Ruwan wuta na kwararowa daga Tsaunin Nyiragongo

Mazauna birnin sun tsere da katifunsu da sauran kayansu.

Wata mata ƴar Congo ɗauke da kayanta a ka, tana tserewa daga wurin aman wutar na daren 22 ga watan Mayun 2021
Wani mutum ɗauke da akwatinsa a lokacin da zai tsere daga Goma ranar 23 ga watan Mayu 2021

Bayan isa unguwannin da ke wajen birnin da filin jirgin sama da ke gabashi, a yanzu ruwan wutar ya daina kwarara.

Tokar aman wutar ya lulluɓe garin Goma

Dubban ƴan Congo, ciki har da yara da tsoffi sun nemi mafaka a maƙwabciyarta Rwanda a lokacin da dutsen ya yi amai.

A nan suna bacci da kayayyaki a bisa wani titi a garin Gisenyi a iyakar Jamhuriyar Demokuraɗiyyar Congo.

Dubban ƴan Congo, ciki har da yara da tsoffi sun nemi mafaka a maƙwabciyarta Rwanda a lokacin da dutsen ya yi amai.

Tsaunin Nyiragongo na ɗaya daga cikin tsaunuka da ke aman wuta a duniya - inda a nan a ke iya ganinsa dada Tsibirin Tchegera a kan Tafkin Kivu a wajen Goma.

Hoton Tsibirin Tchegera a wajen Goma a kan Tafkin Kivu

Duka hotunan na da haƙƙin mallaka.