Me ya sa Atiku da Buhari 'suka raba kan 'yan Kannywood'?

An wallafa

Mun zabo hotunan wasu daga cikin 'yan Kannywood da ke goyon bayan Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wadanda ke mara wa tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar baya a fafutukar da suke yi wajen ganin sun ci zaben 2019.

Sani Musa Danja
Bayanan hoto, Sani Musa Danja shi ne kan gaba a cikin 'yan Kannywood da ke jam'iyyar PDP kuma yana goyon bayan Atiku Abubakar
Kannywood
Bayanan hoto, A yayin da Adam A Zango ke goyon bayan Shugaba Buhari...
Nasiru Horo Dan-mama
Bayanan hoto, ...an hango yaronsa, Nasiru Horo Dan-mama, yana tallata tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar
Malam Aminu Saira na tare da Buhari...
Bayanan hoto, Malam Aminu Saira na tare da Buhari...
Shi ma Bashir Nayaya(dama) ya ce 'Sai Atiku!', ko da yake ba a san inda Sarki Ali Nuhu ya sa gaba ba
Bayanan hoto, ... shi kuwa Bashir Nayaya(dama) ya ce 'Sai Atiku!', ko da yake ba a san inda Sarki Ali Nuhu ya sa gaba ba
Kannywood
Bayanan hoto, Fati Washa na cikin 'yan Buhariyya!
Fati Muhammad ta dade da soma yi a Atiku yakin neman zabe
Bayanan hoto, Fati Muhammad ta dade tana tallata Atiku
Kannywood
Bayanan hoto, ...Amma Ado Gwanja ya ce kuri'arsa na wurin Buhari
Maryam Booth na cikin manyan jaruman Kannywood da ke goyon bayan Atiku Abubakar
Bayanan hoto, ...ko da yake Maryam Booth ta ce sai ta tabbatar Atiku ya zama shugaban Najeriya