Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa Atiku ya dage kan mayar da tallafin man fetur a Najeriya?
Batun cire tallafin man fetur na ci gaba da haifar da muhawara a Najeriya gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.
Babban ɗan takara na hamayya, Atiku Abubakar ne ya tayar da ƙurar lokacin da ya sanar cewa zai mayar da tallafin man fetur idan ya lashe zaɓen ƙasar na 2027.
Kalaman na tsohon mataimakin shugaban ƙasar a makon da ya gabata sun ƙara zafafa siyasar ƙasar, lamarin da ya kai ga shugaban Najeriya Bola Tinubu da kansa ya fito ya soki lamirin kalaman na Atiku.
Sai dai a wani kalami da mai taimaka wa Atiku Abubakar kan yaɗa labarai, Kenneth Okonkwo ya yi a hirarsa da wata kafar talabijin ya nuna cewa kamar akwai sassauci kan batun janye tallafi, sai dai Atiku ya yi watsi da kalaman na Okonkwo.
A lokacin da ya ya yi bayani a gidansa da ke Abuja ranar Talata, Atiku ya sake nanata alwashin nasa.
"Zan nanata ɓaro-ɓaro cewa batun dawo da tallafin man fetur da na ce zan yi babu fashi", a cewar Atikun.
Ya ƙara da cewa "cire tallafin man fetur ya jefa mutane cikin talauci fiye da kowane lokaci a tarihin wannan ƙasa".
Me muƙarraban Atiku suka ce?
To sai dai a ƙoƙarin yin ƙarin haske game da bayanin na Atiku, na kusa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar sun riƙa yin wasu kalamai da suka nuna shakku kan batun dawo da tallafin.
Daga cikin irin waɗannan mutane har da mai mara masa baya a takarar 2027 Rotimi Amaechi, da mai taimaka masa kan yada labari Paul Ibe da kuma wani mai taimaka masa kan yaɗa labaran Kenneth Okonkwo.
A lokacin taron ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) a birnin Fatakwal, Rotimi Amaechi, ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC ya ce "Abin da Atiku Abubakar ke nufi ba shi ne kauce wa cire tallafin man fetur ba ko a'a, abin da muke son yi shi ne mu samar da ɗanyen man fetur cikin rahusa ta yadda za a tace a sayar a cikin farashi mai sauƙi ga al'umma'', in ji shi.
Ɗaya daga cikin masu taimaka wa Atiku Abubakar kan harkar yaɗa labarai Kenneth Okonkwo, a nasa bangaren cewa ya yi: "Abin da Atiku Abubakar take magana a kai shi ne cewar man fetur namu ne. Babu wani dalili da zai sanya a ce mune muke samar da ɗanyen mai sannan kuma a ce ana sayar wa al'umma a cikin farashi mai tsada."
Haka nan shi ma wani makusancin Atiku Phrank Shuaibu ya ce: "Abin da Atiku ke son a yi abu ne mai sauƙi kuma a bayyana yake. Yana cewa ne dole ne mu magance ɓarna, kuma idan za a magance ɓarna to dole a kawo sauyi kuma a sauƙaƙa wajen samar da shi. Za mu ƙarfafa gwaiwar samar da fetur a cikin gida, za a ƙarfafa matatu na cikin gida.
Amma a cikin jawabin nasa na ranar Talata, Atiku ya ce „Ƴan Najeriya da dama na ta kira na, suna cewa ɗaya daga cikin masu taimaka min ya fadi wata Magana ta daban game da kalamina kan dawo da tallafin man fetur, to bari na sake fadi ɓaro-ɓaro cewa zan dawo da tallafin man fetur.
''Saboda haka ya kamata a sani cewa ba da yawuna ya yi magana ba".
Me ya sa ake muhawara kan tallafin man fetur a yanzu?
Bayan sama da shekara uku da cire tallafin man fetur, za a yi tsammanin cewa ƴan Najeriya sun riga sun saduda, sun rungumi sabon yanayin da cire tallafin man fetur din ya kawo.
To amma a baya-bayan nan an riƙa yin tambayoyi game da ina kuɗin da aka samu daga cire tallafin man fetur suke?
Najeriya na ci gaba da cin bashi, ƙarin mutane sun faɗa cikin talauci sannan babu wani sauyin a zo a gani a ɓangaren samar da kayan more rayuwa ga al'umma.
Shi ma Atiku Abubakar abin da yake ta nanatawa kenan a jawabansa. "Cire tallafin man fetu rya jefa ƴan Najeriya cikin talauci fiye da kowane lokaci a tarihin ƙasar nan," a cewar Atiku.
Waɗannan kalamai nasa da kuma alƙawarinsa na mayar da abin da mutanen Najeriya da dama ke kallo a matsayin 'silar wahalar da suke ciki' ta sanya lamarin ya zama babban abin muhawara a faɗin ƙasar, kuma zai taka muhimmiyar rawa a zaɓen 2027 mai zuwa.
A hukuman, an cire tallafin man fetur ne tun shekarar 2021, lokacin da tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar ɓangaren man fetur a ranar 16 ga watan Agustan 2021, bayan kwashe kimanin shekara 20 ana taƙaddama a kanta.
Sai dai Buhari ya ci gaba da sanya tallafin man fetur a kasafin Najeriya har bayan zaɓen shekara ta 2023, to amma magajinsa Bola Tinubu ya ayyana cire tallafin a ranar farko da ya kama mulki, wato 29 ga watan Mayun 2023.
Ko Najeriya za ta iya mayar da tallafin man fetur?
Wannan lamari abu ne mai sarƙaƙiya kuma tamkar abu ne da "ba zai yiwu ba" in ji wani masanin tattalin arziƙi a Najeriya, wanda bai so a bayyana sunansa ba.
Ya ce ''ba zai yiwu ba" a dawo da tallafin man fetur. Sannan "tamkar fama ciwon da ya riga ya warke ne," kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Ya bayyana cewa idan har Najeriya ta ce za ta dawo da tallafin man fetur to abin zai laƙume mata kuɗi daga naira tiriliyan 12 zuwa 15 a shekara.
"Idan ka duba za ka ga cewa ana sayar da man fetur kan kimanin naira 1,300 a kan kowace lita, idan za ka dawo da farashin man fetur zuwa naira 700 ko 600, yayin da ake shan litar mai kimanin miliyan 40 a rana, za ka ga cewa lissafin ba ƙarami ba ne.
Ya bayyana cewa idan aka kwatanta kuɗin shiga da Najeriya ke samu da kuma makudan kudin da za a kashe idan aka mayar da tallafin, zai zamo abu mai matuƙar wahala ga Najeriya.
Sai dai masanin ya ce akwai hanyoyi da dama da za a iya bi wajen rage tsadar farashin man fetur ɗin wadda ta addabi al'ummar ƙasar.
Mene ne tallafin man fetur na Najeriya?
Tallafin man fetur wasu kuɗaɗe ne da gwamnatin Najeriya ta kwashe gomman shekaru tana cirewa daga cikin aljihunta, waɗanda take amfani da su wurin biyan wani ɓangare na kuɗin da ake kashewa wajen saye da shigar da tataccen man fetur daga kasuwannin duniya zuwa Najeriya.
Gwamnatin na yin haka ne domin kada a sayar wa al'ummarta man fetur a kuɗi daidai da ainihin farashin kowace lita, bayan la'akari da ƙudin da aka kashe wajen ɗawainiyar shiga da man daga ƙetare.
Misali – idan farashin saye da shigar man fetur zua Najeriya daga Belgium yana kamawa naira 700 ne a kan kowace lita, gwamnatin Najeriya kan biya kimanin naira 495 ke nan a matsayin tallafi domin ganin an sayar da lita ɗaya ta man fetur ɗin ga ƴan Najeriya a kan farashin da bai zarce naira 205 ba (idan aka yi la'akari da farashin man fetur ɗin kafin cire tallafi).
Hakan na nufin idan kana da mota wadda tankinta ke cin lita 50, a duk lokacin da ka cika ta kan farashin naira 205 kowace lita, za ka biya mai gidan mai naira 10,250, yayin da ita kuma gwamnati za ta biya naira 24,750 a madadinka.
Wannan ne ya sanya yadda al'ummar Najeriya suka riƙa sayen man fetur ya zama ɗaya daga cikin mafiya sauki a duniya.
Domin kuwa a 2022 yayin da farashin litar mai a Najeriya bai wuce naira 220 ba, a kasar Ghana ana sayar da ita ne a kan kwatankwacin naira 544, a Jamhuriyar Nijar kuma naira 580, a Afirka ta kudu kuma 489, yayin da a Brazil ake sayar da litar kan naira 633 - Kamar yadda yake a cikin wani rahoto na Dr. Ahmed Adamu, masani kan lamurran man fetur a Najeriya.
Saboda haka idan za a yi bayani a sauƙaƙe, cire tallafin man fetur na nufin gwamnati ta daina cire ko da sisin kwabo daga cikin aljihunta da sunan biyan masu shiga da man fetur domin sassauta farashinsa ga al'umma.
Wanda matakin da gwamnatin Najeriyar ta ɗauka ke nan a 2023, lokacin da shugaban ƙasar ya sanar a aikace cewa an cire tallafin.
Sai dai lamarin ya haifar da sauyi a kusan dukkanin ɓangarorin ƙasar, wanda ya sanya ake ci gaba da muhawara a kansa.