Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hausar AI: Nasara ko barazana ga harshen Hausa?
A daidai lokacin da ake ci gaba da tafka muhawara kan makomar ƙirƙirarriyar fasaha ta AI, hankali ya fara komawa kan yanayin yadda ake kallon fasahar na tasiri kan harshen Hausa da makomarta.
Masana dai suna ƙara himma wajen kira ga a rumgumi sabuwar fasahar domin a cewarsu, za ta sauƙaƙa ayyukan yau da kullum, inda a gefe guda kuma ake fargabar za ta raba mutane da aiki.
A cikin ɗan gajeren lokaci, ƙirƙirarriyar fasahar Artificial Intelligence (AI) ta sauya daga abin da aka fi sani da shi a duniyar injiniyoyi da ƙwararru a ɓangaren fasaha zuwa wata aba da ke neman zama ruwan dare gama duniya.
Yanzu, mutum na iya amfani da AI wajen rubutu, fassara, koyon ilimi, samar da hotuna da bidiyo, ko ma tsara ayyukan da zai riƙa yi a kullum. Wannan saurin yaɗuwar fasahar, musamman tun daga shekarar 2023, ya kuma buɗe wata sabuwar muhawara: me AI ke nufi ga harsunanmu, musamman Hausa?
Yayin da AI ke ƙara koyon Hausa daga bayanan da ke intanet, tana kuma fara samar da nata salon magana wanda wani lokaci yake kama da Hausar da mutane suka saba, wani lokaci kuma ya bambanta da ita. Shin wannan alama ce ta raunin harshen, ko kuwa wata sabuwar hanya ce ta bunƙasa shi?
A wata tattaunawa, Farfesa Abdallah Uba Adamu, masani kan harkokin ilimi, sadarwa da fasaha, ya yi nazari kan wannan sauyi, inda ya bayyana dalilin da ya sa bai kamata Hausawa su yi ƙoƙarin guje wa AI ba, sai dai su rungume ta, su koyi yadda take aiki, sannan su taimaka wajen koya mata harshensu da al'adunsu.
A wajensa, tambayar ba ita ce ko AI za ta zo ba—domin ta riga ta zo. Tambayar ita ce: me za mu yi da ita, kuma wane irin tasiri za ta yi wa harshen Hausa da al'ummar da ke magana da shi?
Karɓuwar AI
A cikin ƴan shekarun nan, fasahar Artificial Intelligence (AI) ta sauya daga wani abu da ya fi kasancewa a hannun injiniyoyi da ƙwararrun masu fasahar zamani zuwa wata fasaha da kowa zai iya amfani da ita.
Tun daga shekarar 2023, amfani da generative AI ya ƙara yaɗuwa, inda mutane ke amfani da ita wajen rubutu, fassara, bincike, samar da hotuna da bidiyo, koyarwa, har ma da gudanar da wasu ayyukan yau da kullum.
A cewar Farfesa Abdallah Uba Adamu, wannan ba wani yanayi ba ne da ya kamata mutane su yi ƙoƙarin guje masa, domin ci gaban fasaha ba ya tsayawa saboda tsoron abin da zai iya kawowa.
"Idan kai ka ƙaurace wa fasahar, wasu za su karɓe ta su yi amfani da ita. Don haka gara a rungume ta, a fahimce ta, sannan a yi amfani da ita yadda ya kamata," in ji Farfesa Abdallah Uba Adamu.
Farfesan ya ce AI ta riga ta zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullum, kuma damar da take bayarwa na da yawa. Misali, mutum zai iya tsara AI ta riƙa tura masa tafsirin aya a wani lokaci na musamman kowace rana. Wannan na nuna yadda fasahar za ta iya zama mataimaki wajen ayyukan da mutum ke yi akai-akai.
Sai dai, a wajensa, fasahar ba ta da takamaiman kyau ko rashinsa. Abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda mutum yake amfani da ita.
Ya kwatanta AI da wuƙa: Ana iya amfani da wuƙa wajen dafa abinci da sauran ayyukan gida, amma kuma ana iya amfani da ita wajen cutar da mutum.
"AI kamar wuƙa ce. Za ka iya amfani da ita a gida wajen sarrafa abubuwa, kuma za ka iya amfani da ita wajen cutar da mutum. Don haka abin da ya fi muhimmanci shi ne manufar da ake da ita wajen amfani da ita," in ji shi.
AI da Hausa
Yayin da AI ke ƙara samun karɓuwa, wani muhimmin batu shi ne yadda take amfani da harshen Hausa. A wasu lokuta, masu amfani da ita kan lura cewa Hausar da AI ke samarwa ba ta yi daidai da Hausar da suka saba ji a yankinsu ba.
Farfesa Abdallah ya bayyana cewa wannan ba abin mamaki ba ne, domin AI tana koyo ne daga bayanan da take samu.
"Koyo take yi. Tana koyo ne bisa abin da ta tarar a intanet. Saboda haka, idan kana ganin kai ɗan Kano ne, wataƙila inda take koya wata Hausar ce daban. Ba zai yiwu ka ce dole ta yi Hausar da kake yi ba."
Ya ce Hausa tana da bambance-bambancen lafazi da salon magana daga yanki zuwa yanki. Don haka, irin bayanan da AI ta samu za su iya shafar irin Hausar da za ta riƙa amfani da ita.
"Inda take koya mata, za ta koya," in ji shi, yana mai bayyana cewa masu amfani da AI ma suna da damar taimakawa wajen inganta harshen ta hanyar gyara abin da take samarwa da kuma ba ta ingantattun bayanai.
Ya kwatanta wannan yanayin da Pidgin, "Yanzu kamar Pidgin ne. A birkice yake, amma ma'ana tana fita."
A cewar Farfesan, bai kamata a mayar da hankali kawai kan bambancin lafazi ko salon magana ba, inda ya ce abin da ya fi muhimmanci shi ne a tabbatar da cewa saƙon da ake son isarwa ya fito fili.
AI da ci gaban Hausa
Farfesa Abdallah ya yi imanin cewa zuwan AI na iya zama wata dama ta bunƙasa Hausa, musamman idan aka yi amfani da fasahar wajen adana da yaɗa bayanan harshen.
"Akwai alheri wajen ci gaban harshe. Ai duk wani abu da ya fito sabo, ci gaban harshe ne."
Ya kuma yi nuni da cewa Hausa tana da dogon tarihi na rubuce-rubuce da tattara bayanai. Daga cikin muhimman ayyukan da suka taimaka wajen adana ilimin Hausa akwai ƙamus ɗin Bargery, wanda ya ƙunshi kalmomi da bayanai kan asalinsu da ma'anoninsu.
A yau, bayanai da dama sun koma intanet, kuma AI na iya samun damar amfani da irin waɗannan bayanai wajen koyon harshe. Wannan, a cewar Farfesa Abdallah, na iya taimakawa wajen ƙara yawan bayanan Hausa da ake samu a duniyar zamani.
Sai dai yana ganin ya kamata a ƙarfafa bambance-bambancen harshen, domin kada wata siga ta Hausa ta mamaye sauran sigogin.
"Muna so a riƙa samun bambance-bambancen domin a raya sauran harsunan. Amma a wajenmu, ma'ana muke fifitawa sama da bambancin."
Lokacin da aka tambaye shi ko akwai tawaya a yadda AI ke furta ko samar da Hausa, Farfesan ya ce bai kamata a yi gaggawar kiran bambancin lafazi da tawaya ba.
Ya yi misalin mutum daga wani yanki da zai iya yin magana cikin salon da wani Bahaushe daga wani yanki ba zai fahimta nan take ba.
"Idan, misali, Bakatsine ya maka magana da ƙyar ka gane, ba za ka ce tawaya ba ce. Haka harshen yake."
A ra'ayinsa, irin wannan ne ya kamata a fahimta game da AI. Idan AI ta yi amfani da wani salo na Hausa da ya bambanta da wanda mutum ya saba da shi, ba lallai ne hakan ya nuna cewa Hausar ba daidai ba ce ba. Wataƙila kawai ta samo wannan salon ne daga bayanan da ta koya.
Haɗarin da ke tattare da AI
Duk da cewa Farfesa Abdallah ya yi nuni da damar da AI ke bayarwa, ya kuma amince cewa akwai abubuwan da ya kamata a kula da su. AI tana iya tattara bayanai daga wurare daban-daban, ciki har da abubuwan da ake wallafawa a kafafen sadarwa.
"Yanzu duk maganganun da ake yi a kafofin sadarwa tana bibiya, tana tattarawa, tana koya."
Wannan damar na iya zama amfani wajen bunƙasa harshe, amma tana kuma buƙatar a kula da ingancin bayanan da AI ke koya. Idan bayanan da aka samar ba su da inganci, akwai yiwuwar AI ta maimaita kurakuran.
Saboda haka, a cewar Farfesan, ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a mai da hankali a kai shi ne ladabin magana—wato yadda ake amfani da harshe da kuma irin bayanan da ake ciyar da fasahar.
A wajen Farfesa Abdallah, mafita ba ita ce a yi ƙoƙarin hana AI amfani da Hausa ba. Maimakon haka, ya kamata a riƙa koyar da ita da gyara ta a hankali.
"Babu abin da za ka iya yi, sai dai ka riƙa koyar da shi."
Ya ce bai a ce Hausar da AI ke amfani da ita ba a yarda da ita ba. Abin da ya fi dacewa shi ne a riƙa ba ta ingantattun bayanai, a gyara kurakuranta, sannan a taimaka mata ta fahimci nau'o'in Hausa daban-daban.
Wata babbar dama da Farfesa Abdallah yake gani ita ce yadda AI za ta iya taimakawa masu shirya fina-finai da masu ƙirƙirar abubuwan nishaɗi.
A baya, samar da fim yana buƙatar jari mai yawa, sannan mai shirya fim ya fuskanci ƙalubalen samun kasuwa da dawo da kuɗin da ya kashe. Amma zuwan dandamalin intanet kamar YouTube ya sauya tsarin.
Farfesan ya tuna yadda masana'antar shirye-shiryen Hausa ta samu sabon salo bayan zuwan wasu kafafen samar da shirye-shiryen talabijin da fina-finai.
"A da idan aka yi sai na kai wa ɗan kasuwa, su yi ta wahalhalu. Sai Amurka ta zo ta kafa Arewa24, sai suka fara masu dogon zango, sai aka karɓa. Nan da nan sai ga fina-finai."
A yau, mutum na iya samar da abun kallo ya saka shi a YouTube ba tare da dogaro da tsarin tallace-tallacen gargajiya kaɗai ba. Idan aka samu masu kallo da yawa, akwai damar samun kuɗi daga abin da aka samar.
Wannan na iya ba matasa masu basira damar shiga masana'antar ba tare da buƙatar babban jari kamar yadda ake yi a baya ba.
Shin AI zai ƙwace ayyukan mutane?
Farfesa Abdallah ya ce wannan tsoron ba sabon abu ba ne. A duk lokacin da wata sabuwar fasaha ta shigo, mutane kan ji tsoron cewa za ta maye gurbin wasu ma'aikata ko kuma ta rage darajar wasu.
Ya kawo misalin abi lissafi da ake kira 'calculator', inda a lokacin da aka fara amfani da shi a harkar ilimi wasu malamai suka nuna adawa saboda tsoron cewa zai rage ƙwarewar ɗalibai wajen lissafi.
Amma a cewarsa, ba za a iya dakatar da ci gaba saboda tsoron abin da sabuwar fasaha za ta kawar ba.
"Tabbas sabon abu zai kawar da wasu, amma ba za ka ce ba za a ci gaba ba saboda tsoron kawar da wasu."
A ganinsa, AI za ta iya sauya yadda ake yin wasu ayyuka, amma ba lallai ne ta maye gurbin mutum gaba ɗaya ba.
Ya sake yin amfani da misalin dafa abinci. "Misali dafa abinci, ba zai taɓa dafa maka abinci ba, sai dai ya maka kwatance."
Wato, AI na iya taimaka wa mutum wajen sanin abin da zai yi, amma har yanzu mutum ne ke aiwatar da aikin a zahiri a fannoni da dama.
A ƙarshe, Farfesa Abdallah Uba Adamu ya bayyana cewa abin da ya fi burge shi shi ne yadda wasu matasa suke amfani da fasahar da ke hannunsu wajen ƙirƙirar sabbin abubuwa.