Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa

Wannan shafi na kawo muku labaran wasanni da kasuwar 'yan wasanni ta duniya daga nan BBC Hausa daga 24 zuwa 30 ga watan Agusta

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Buhari Fagge

  1. Ina makomar Mykhailo Mudryk a Chelsea

    Chelsea ta daina kallon Leeds United a matsayin wurin da za ta tura Mykhailo Mudryk a matsayin aro a halin yanzu.

    Leeds na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefe, bayan da Chelsea ta yi watsi da tayin farko da kulob ɗin ya gabatar domin karɓarsa aro.

    Sai dai Leeds ba ta da niyyar yin gaggawar kulla yarjejeniya kan sharuddan da take ganin ba su yi mata daɗi ba.

    Mudryk kuma na samun tayi daga wasu ƙungiyoyin Premier League da kuma kulob-kulob a Turai, ciki har da Strasbourg, wanda ke cikin ƙungiyoyin da abokan hulɗar Chelsea ne.

    Kasuwar musayar 'yan wasa ta Premier League za ta rufe ranar Talata, 1 ga Satumba.

  2. Ferran Torres ya fara wasa a PSG da ƙafar dama

    Gwarzon dan wasan Kofin Duniya Ferran Torres ya farke wa PSG ƙwallaye biyu da aka ci ta 2-0, inda ya taimaka mata ta tashi canjaras da Rennes a wasan farko na Ligue 1.

    Torres mai shekaru 26, wanda ya ci ƙwallon nasara lokacin da Spain ta doke Argentina a wasan ƙarshe na Kofin Duniya, ya koma PSG daga Barcelona kan kuɗi kimanin fam miliyan 42.7 a ranar 15 ga Agusta.

    Kocin PSG, Luis Enrique, ya sanya Torres cikin wasa a mintina 45 na biyu bayan ƙungiyarsa ta shiga hutun rabin lokaci tana fuskantar barazanar shan kaye.

    Tsohon ɗan wasan Manchester City ya maye gurbin wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or, Ousmane Dembele, kuma nan take ya zama gwarzon PSG bayan ya ci ƙwallaye a mintuna na 71 da 82, wanda ya taimaka wa zakarun Faransa kauce wa abin kunya.

    PSG ta buga wasa mara armashi a mintina 45 na farko, inda Sebastian Szymanski ya ci wa Rennes kwallon farko a minti na tara. Daga baya Esteban Lepaul ya ƙara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

    Sai dai Rennes, wadda ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na shida, ta kasa riƙe wannan nasara yayin da Luis Enrique ya yi amfani da ƙwararrun 'yan wasan da ke kan bencin PSG.

    Tun farko dai an shirya PSG ta fara kare kambunta ne a gida a birnin Paris, amma an sauya filin wasan zuwa Brittany saboda matsananciyar zafi da kuma lalacewar da filin wasan PSG ya yi.

    PSG na neman lashe kofin Ligue 1 karo na shida a jere a wannan kakar, tare da burin lashe kofin Champions League karo na uku a jere.

  3. Barcelona ta ce 'yansanda sun yi amfani da karfi kan magoya bayanta

    Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zargi 'yan sanda da yin amfani da karfin da ya wuce kima kan magoya bayanta a lokacin wasan da ta doke Elche da ci 5-0 a ranar Lahadi.

    An ga bidiyoyi a shafukan sada zumunta da ke nuna rikici tsakanin 'yan sanda da magoya bayan yayin da suke kokarin shiga filin wasa na Estadio Martinez Valero da ke Elche.

    Barcelona ta bayyana cewa, babu wata hujjar daukar matakin yin amfani da karfi wajen kama daya daga cikin magoya bayanta.

    Haka kuma Barcelona ta zargi 'yan sanda da kwace tutocin 'Estelada' daga hannun magoya baya; tutocin da masu goyon bayan samun 'yancin yankin Catalonia ke amfani da su, kuma galibi magoya bayan kungiyar ta Barca ke dagawa.

  4. Rikicin Crystal Palace da Mateta na kara dagulewa

    Sabon salo a rikicin da ke tsakanin Jean-Philippe Mateta da Crystal Palace, wanda a 'yan kwanakin nan ya kasance tamkar tafiyar jirgin ƙasa mai cike da sauye-sauye, ya sake jefa makomar ɗan wasan a kulob ɗin cikin tambaya.

    Bayyanawar da BBC Sport ta yi ranar Asabar cewa Mateta na jayayya cewa shekarar ƙarshe da ke cikin kwantiraginsa da Palace ba ta da inganci, tare da matakin da ya ɗauka na kai ƙarar gaban wata kotun sulhu mai zaman kanta ta Premier League da kuma sauraron ƙara a Fifa, ya ƙara sanya lamarin ya zama mai jan hankali yayin da kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ke gab da rufewa.

    Duk da cewa Mateta da mashawartansa suna kalubalantar cewa shekarar ƙarshe da ke cikin yarjejeniyarsa ba ta da ɗaurewa a doka, saboda ƙarin shekarar wata zaɓi ce da kulob ɗin ya amince daga cikin ainihin kwantiraginsa na shekaru huɗu da rabi, har yanzu ɗan wasan na ƙasar Faransa yana ƙarƙashin kwantiragi da Crystal Palace.

    Kwanaki kaɗan kafin ya fara wasan farko na Palace a Premier League da Everton, Fifa ta yanke hukunci cewa batun ba ya cikin huruminta.

    Kuma ko da yake ba a bayyana sakamakon hukuncin kotun sulhu mai zaman kanta ta Premier League da aka yi a kakar wasan da ta gabata ba, kasancewar Mateta har yanzu yana ƙarƙashin kwantiragi da Palace na nuna cewa hukuncin bai zai yi masa dadi ba.

  5. Arbeloa da Alonso abokan juna da za su fafata a Premier

    Lokacin da aka tambayi tsohon kocin Liverpool, Rafael Benitez, ko ya taɓa tsammanin tsoffin 'yan wasansa Xabi Alonso da Alvaro Arbeloa za su zama masu horarwa, amsarsa ta kasance kai tsaye ba tare da ɓoye komai ba.

    "Alonso, eh. Arbeloa kuwa, ba sosai ba," in ji shi. "A gare ni, Arbeloa ya ba ni mamaki."

    Kusan shekaru 20 bayan da Benitez ya haɗa su a Anfield, yanzu su biyun za su fafata a matsayin masu horarwa, yayin da Fulham da Arbeloa ke jagoranta za ta karɓi baƙuncin Chelsea ta Alonso a yau Litinin.

    Su biyun sun lashe Kofin Duniya na 2010 tare da Spain, da kuma Kofin Kasashen Turai sau biyu. Haka kuma sun samu nasarori a gasar lig da kofuna na cikin gida bayan sun koma Real Madrid daga Liverpool.

    Sun buga wasa tare har tsawon shekaru bakwai a matakin kulob, kuma sun yi wasa a fili guda sau 262 a matakin kulob da ƙasa. Tun bayan sun daina buga wasa, hanyoyin aikinsu sun ci gaba da kasancewa a haɗe.

    An ɗaga darajar Arbeloa daga Real Madrid B Castilla zuwa babban ƙungiyar Real Madrid domin maye gurbin Alonso bayan da aka sallame shi daga jagorancin katafaren kulob ɗin na Spain a watan Janairun bara.

  6. An sayar da kwallon da Maradona ya ci da hannu £2.5m

    Ƙwallon da Diego Maradona ya zura shahararren ƙwallonsa na Hand of God a gasar cin kofin duniya ta 1986 ya samu mai siya a gwanjo kan kuɗi fam miliyan 2.5.

    Maradona ya yi fice bayan da ya zura ƙwallon da hannu ta wuce mai tsaron raga Peter Shilton a wasan da Argentina ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan daf da na kusa da na ƙarshe.

    Bayan wasan, ya shaida wa manema labarai cewa ya zura ƙwallon ne da kan Maradona, ɗan kuma da hannun uabngiji".

    Daga baya Maradona ya sake zura abin da aka fi sani da "ƙwallon ƙarni" (Goal of the Century) a wannan wasa, inda ya yi yanka 'yan wasan Ingila biyar kafin ya sanya ƙwallon a raga ta hannun Shilton.

    Ko da yake an sayar da ƙwallon kan dala miliyan 3.3, kwatankwacin fam miliyan 2.5 (£2.5m), a wajen bajakolin Heritage da ke Amurka a ranar Asabar, ana sa ran za ta kai kusan dala miliyan 10, wato fam miliyan 7.3.

    Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Reuters kafin gwanjon, Mike Provenzale, wani ƙwararren mai gudanar da gwanjo a Heritage, ya ce: "Wannan abu ne na musamman da babu irinsa. Ana iya cewa shi ne mafi muhimmancin abin tunawa da ya shafi ƙwallon ƙafa da ake da shi a duniya."

    Ali Bin Nasser ɗan ƙasar Tunisiya, wanda shi ne alkalin wasan a 1986, ya karɓi ƙwallon Adidas Azteca bayan kammala wasan kuma ya adana ta fiye da shekaru 30.

    A shekarar 2023, ya rattaba hannu a wata takarda da ta tabbatar da cewa ita ce kaɗai ƙwallon da aka yi amfani da ita a duk wasan, kuma wasu masu bincike da ke zaman kansu sun sake tabbatar da sahihancinta.

    Bin Nasser ya sayar da ƙwallon a shekarar 2022 kan dala miliyan 2.37, kwatankwacin fam miliyan 1.74.

    Sabon mamallakin ya sake fitar da ita gwanjo a shekarar 2023, amma ba a sayar da ita ba saboda tayin da aka yi ba su kai ƙimar mafi ƙaranci da aka tsara ba.

    Rigar da Maradona ya sanya a wannan wasa ita ma an sayar da ita a gwanjo a shekarar 2022 kan fam miliyan 7.1.