Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun ƴan ƙwallo da ba su taɓa samun jan kati ba
A duniyar ƙwallon ƙafa, samun katin gargaɗi ko jan kati abu ne da ya zama ruwan dare, musamman ga ƴan wasan da suka yi dogon lokaci suna buga wasa a manyan mataki.
Ƙwazon kare ƙwallo, fafatawa mai zafi da kuma matsin lamba na manyan wasanni kan sa ko da fitattun ƴanwasa su faɗa cikin tarkon aikata laifin da zai jawo musu kora daga fili.
Sai dai duk da haka, akwai wasu ƴan wasa da suka yi fice ba kawai saboda bajintarsu ba, har ma saboda yadda suka kiyaye dokokin wasa tsawon rayuwarsu ta ƙwallon ƙafa.
Wasu daga cikinsu sun yi fiye da shekara ashirin suna taka leda, amma ba su taɓa ganin jan kati daga alkali ba.
Abin mamaki ma shi ne, wasu daga cikin waɗannan ƴanwasan sun taka muhimmaiyar rawa a manyan ƙungiyoyi da gasar cin kofin duniya, inda zafin fafatawa ya fi ko'ina tsanani. Duk da haka sun ci gaba da nuna kamun kai, ladabi da fasahar kaucewa yin laifukan da za su iya jawo musu korar kai tsaye.
A wannan rahoto, za mu yi nazari kan wasu daga cikin fitattun ƴan ƙwallon duniya da suka yi ɗaruruwan wasanni, suka lashe manyan kofuna, amma suka yi ritaya ko kuma suka ci gaba da taka leda ba tare da taɓa samun jan kati ba.
Gary Lineker - Ingila
Gary Lineker ɗan wasan gaba ne na ƙasar Ingila, wanda ya kasance ɗanwasan gaba a filin ƙwallo a zamaninsa.
Gary Lineker na daga cikin fitattun masu zura ƙwallo a tarihin Ingila. Shi kaɗai ne a cikin manyan ƴan wasa da ba wai kawai bai taɓa samun jan kati ba, har ma katin gargaɗi ba taɓa samu ba tsawon rayuwarsa ta ƙwallo.
Ƙungiyoyin da ya buga: Leicester City, Everton, Barcelona, Tottenham Hotspur, Nagoya Grampus.
Yawan wasanni: Wasanni 654 na gasa.
Muhimman nasarori: Ya ci ƙwallaye 331 a rayuwarsa, ya lashe kyautar Golden Boot a Gasar Cin Kofin Duniya ta 1986 kuma ya samu lambar yabo ta FIFA Fair Play Award a 1990.
Raúl González - Spain
Ƙasa: Sifaniya
Matsayi: Mai kai hari
Kungiyoyin da ya bugawa wasa: Real Madrid, Schalke 04, Al Sadd da New York Cosmos.
Raúl na cikin manyan taurarin da suka kafa tarihi a Real Madrid. Ya yi suna wajen zura ƙwallaye da kuma jagorantar ƙungiya cikin ladabi da kwarewa. Duk da shiga manyan wasanni da derbin da suka yi zafi, bai taɓa samun jan kati ba.
Yawan wasanni: Sama da wasanni 1,000 na kulob da ƙasa.
Muhimman nasarori: Kofunan Zakarun Turai uku da kofunan La Liga shida tare da Real Madrid.
Philipp Lahm (Jamus)
Ƙasa: Jamus
Matsayi: Mai tsaron baya/Mai tsakiya
Kungiyoyin da ya bugawa wasa: Bayern Munich da Stuttgart.
Philipp Lahm na daga cikin mafiya kwarewa a tarihin masu tsaron baya. Abin mamaki shi ne yadda ya kai ƙarshen rayuwarsa ta wasa ba tare da an taba kore shi daga fili ba, duk da cewa aikin kare baya na buƙatar yawan tunkarar 'yan adawa.
Yawan wasanni: Kimanin wasanni 660.
Muhimman nasarori: Kyaftin din Jamus lokacin da ta lashe Kofin Duniya na 2014.
Andrés Iniesta - Spain
Ƙasa: Sifaniya
Matsayi: Mai tsakiya
Kungiyoyin da ya bugawa wasa: Barcelona, Vissel Kobe da Emirates Club.
Iniesta ya kasance ginshiƙi a nasarorin Barcelona da kuma tawagar Sifaniya ta zinariya. Salon wasansa ya ta'allaka ne kan taka ƙwallo cikin natsuwa da kaucewa rikici, lamarin da ya taimaka masa yin rayuwa mai tsayi ba tare da jan kati ba.
Yawan wasanni: Sama da wasanni 1,000.
Muhimman nasarori: Ya ci ƙwallon da ta bai wa Sifaniya Kofin Duniya na 2010 tare da lashe Champions League sau huɗu.
Michel Platini - Faransa
Ƙasa: Faransa
Matsayi: Mai tsakiya
Kungiyoyin da ya bugawa wasa: Nancy, Saint-Étienne da Juventus.
Platini na daga cikin manyan 'yan wasan tsakiyar fili a tarihin ƙwallon ƙafa. Ya yi suna wajen cin ƙwallaye daga tsakiya da kuma jagorantar tawagar Faransa zuwa manyan nasarori.
Yawan wasanni: Wasanni 655.
Muhimman nasarori: Ya lashe Ballon d'Or sau uku a jere ba tare da taɓa samun jan kati ba.
Karim Benzema - Faransa
Ƙasa: Faransa
Matsayi: Mai kai hari
Kungiyoyin da ya bugawa wasa: Lyon, Real Madrid da Al-Ittihad.
Benzema ya kasance ɗaya daga cikin manyan masu zura ƙwallaye a ƙarni na 21. Duk da tsananin gasa a La Liga da Champions League, ya shahara da kiyaye kansa daga laifukan da ke kaiwa ga kora.
Yawan wasanni: Sama da 649 lokacin da UEFA ta wallafa rahotonta.
Muhimman nasarori: Ballon d'Or 2022 da kofunan Champions League da dama tare da Real Madrid.