Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United ka iya rasa ɗaukar Nico Paz,Liverpool na zawarcin Camara.
Manchester United na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke sahun gaba wajen neman ɗan wasan tsakiya na Como, Nico Paz, mai shekara 22. Sai dai samun gurbin shiga gasar zakarun turai na iya kasancewa muhimmin abin da zai yi tasiri a shawarar ɗan wasan na Argentina.(The Athletic - subscription required), external
Sai dai Manchester United na iya fuskantar ƙalubale daga Arsenal, inda rahotanni ke cewa kocin ƙungiyar, Mikel Arteta, na sha'awar ɗauko Nico Paz zuwa filin wasa na Emirates.(ESPN Argentina via Goal), external
Liverpool na fatan kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Monaco, Lamine Camara, mai shekara 22, a kasuwar musayar 'yan wasa ta watan Janairu.Rahotanni sun ce Chelsea na iya janye wa daga fafatawar neman ɗan wasan, bayan da yunkurin da ta yi na ɗaukarsa zuwa Stamford Bridge a lokacin bazarar da ta gabata bai yi nasara ba.(GiveMeSport), external
Everton na sa ido kan matashin ɗan wasan gaba na Cagliari, Paul Mendy, mai shekara 19. Sai dai ɗan wasan na Senegal ya kuma ja hankalin Inter Milan, wadda ita ma ta nuna sha'awar ɗaukarsa.(TeamTalk), external
Manyan ƙungiyoyi irin su Liverpool, Brighton, Bayern Munich da Barcelona na sha'awar matashin ɗan wasa Wael Mohya, kuma za su iya fafatawa wajen ɗaukarsa a bazara mai zuwa.(TalkSport), external
Arsenal ce ke kan gaba wajen neman ɗan wasan gefe na kungiyar Brugge da ƙasar Portugal, Carlos Forbs, mai shekara 22. Sai dai ana sa ran ƙungiyar za ta jira har ƙarshen kakar wasa kafin ta yi yunƙurin ɗaukarsa.(Football Insider), external
Chelsea na sha'awar ɗaukar dan wasan Velez, Simon Escobar, mai shekara 17. Sai dai Brighton ma na neman ɗan wasan na Argentina, wanda ke nufin ƙungiyoyin biyu za su fafata wajen ɗaukarsa. (TeamTalk), external
Brighton na tunanin kawo ƙarshen yarjejeniyar aron ɗan wasan tsakiyar Ingila, Harry Howell, a Leicester City, saboda rashin gamsuwa da ƙarancin lokacin wasa da matashin ɗan wasan mai shekara 18 ke samu. (Football Insider), external