Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a ranar Juma'a 28/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. EFCC ta gurfanar da wata mata kan damfarar maniyyata Hajji naira miliyan 62.5

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC), ta gurfanar da wata mata a gaban babbar kotun tarayyakan zargin damfarar maniyyata aikin Hajji naira miliyan 62.5

    Wata sanarwa da EFCC fitar a shafinta na X, ta ce matar mai suna Hauwa Abdulkadir na iƙirarin cewa tana samar da biza.

    Sanarwar ta ce an gurfanar da ita ne a ranar Alhamis, 26 ga Nuwamba, kan tuhume-tuhume guda bakwai da suka shafi karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

    Ana kuma zargin matar da damfarar wasu maniyyata aikin Hajji a watan Maris, bayan gabatar da kanta a matsayin jami’ar da ke kula da takardun tafiye-tafiye.

    Rahotanni sun ce ta karɓi kuɗaɗe masu yawa daga hannun waɗanda abin ya shafa da sunan cewa za ta samar musu da bizar Saudiyya da kuma tikitin jirgin sama.

  2. Hotuna: Yadda zaɓen gwaji ke gudana a jihar Kano

    A can jihar Kano zaɓen gwaji da hukumar zaɓen Najeriya INEC ke gudanarwa, na tafiya cikin tsakani.

    A ziyarar da BBC ta kai wasu rumfunan zaɓe, ta lura cewa jami'an INEC ba su fito da wuri ba.

    Amma daga baya an ci gaba da aikin tantance mutane - kuma an samu fitowar mutane da dama.

    An girke jami'an tsaro domin tabbatar da komai ya tafi lafiya.

  3. Yadda ake gudanar da zaɓen gwaji a jihar Legas

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC, na can tana gudanar da zaɓen gwaji a wasu sassan ƙasar.

    Hukumar ta ce ta ɓullo da gwajin domin tantance irin shirin da take yi na tunƙarar babban zaɓen ƙasar na 2027.

    INEC ta kuma ce gwajin zai ba ta damar gyara wasu kura-kura da za a iya fuskanta da kuma ganin ingancin na'urar BVAS.

    A nan wasu mutane ne ke yin zaɓe a wata rumfa a mazaɓar Popi-Aguda da ke jihar Legas.

  4. Saudiyya ta yi iƙirarin kakkaɓo makamin linzami da Houthi ta harba Riyadh

    Saudiyya ta ce ta harbo wani makami mai linzami da mayaƙan Houthi suka harba zuwa babban birnin ƙasar, Riyadh.

    Tun da farko, kafafen yaɗa labarai na Houthi sun ce Saudiyya ta kai hari kan Sanaa, babban birnin Yemen, inda suka ce mutane 13 sun jikkata sannan harin ya rushe gidaje.

    A wani taron haɗin gwiwar tsaro, Saudiyya da Pakistan da Turkiyya sun yi Alla-wadai da hare-haren Houthi, suna masu bayyana su a matsayin munanan hare-hare.

    Har yanzu dai babu ƙarin bayani daga ɓangarorin biyu kan waɗannan hare-hare.

  5. Manyan biranen Afrika na nutsewa ƙasa cikin sauri - Bincike

    Wani sabon bincike da aka yi amfani da bayanan tauraron ɗan'adam ya nuna cewa wasu daga cikin manyan biranen Afirka na nutsewa cikin ƙasa, cikin sauri fiye da yadda aka yi zato a baya.

    Daga cikin biranen akwai Lagos a Najeriya da kuma Alexandria a Masar.

    Binciken ya ce wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa wannan matsala na faruwa ne a ɗabi'an ce.

    Sai dai wasu da dama daga cikinsu na da alaƙa da wasu ayyukan bil'adama musamman yawan gina rami domin haƙo ruwa da gina madatsun ruwa.

  6. MSF ta ce an kashe mata jami'ai biyu a harin Isra'ila a Gaza

    Ƙungiyar agaji ta likitoci ta Médecins Sans Frontières, wato MSF, ta nemi a yi bincike tare da ɗaukar mataki kan mutuwar ma’aikatanta biyu sakamakon wani harin sama da Isra’ila ta kai kan wani asibiti a Gaza.

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Tedros Ghebreyesus, ya bayyana kashe-kashen a matsayin abin takaici kuma wanda ba za a amince da su ba.

    Wakilin BBC ya ce sojojin Isra’ila sun ce dukkan mutanen mayaƙan Hamas ne da ke aiki a matsayin jami’an tsaron MSF.

    Isra'ila ta koma kai hare-hare a Gaza a baya-bayan nan, inda rahotanni ke bayyana cewa babu ranar da ba a kashe ko da mutum guda a yankin.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da warhaka.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin sanin halin da duniya take ciki, musamman Najeriya da maƙwabtanta.