A shekara nawa ya kamata matasa su yi aure?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Kai tsaye, ba za a iya cewa akwai wani takamaiman shekaru da aka ƙayyade da mutum ya kamata ya yi aure ba, ko ta fuskar al'ada ko zamantakewa.
Wasu dai na cewa idan mutum ya kai wasu shekaru bai yi aure ba, zai iya fara yin wasu "ɗabi'u da ba a gane musu ba" ko kuma lafiyar ƙwaƙwalwarsa ta iya fuskantar matsala.
Sai dai abin da ya fi muhimmanci shi ne mutum ya duba yanayin rayuwarsa, musamman ta fuskar tattalin arziki da shirye-shiryen da yake da su na ɗaukar nauyin iyali.
Masana zamantakewa da lafiya sun yi amanna cewa matashi ya kamata ya yi aure ne lokacin da ya cika wasu muhimman sharuɗɗa.
Ga wasu daga cikin abubuwan da ya kamata matasa su duba kafin yanke shawarar yin aure:
Wadatar tattalin arziki

Asalin hoton, alameen.ng/IG
Yana da matuƙar muhimmanci matashi ya fahimci hanyar samun kuɗin shigarsa, musamman ga namiji.
Dr Bashir Achida, masanin tattalin arziki a Jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce ya kamata mutum ya kasance yana da halastacciyar hanyar samun kuɗi, ko da kaɗan ne, da zai iya ciyarwa, tufatarwa da samar da mazauni.
Ya ce hakan zai taimaka wa matashi wajen sarrafa abin da yake samu cikin hikima, ba tare da almubazzaranci ba, tare da samun dabarar kashe kuɗi cikin tsari.
Ko da yake akwai matasan da iyaye ko 'yan'uwa ke ɗaukar nauyinsu wajen aure, Dr Achida ya ce bai kamata matasa su dogara kacokan da hakan ba, domin ba abu ne mai ɗorewa da zai taimaka wa mutum ya tsaya da ƙafarsa ba.
"Mutum ya kamata ya san cewa [aure] wata rayuwa ce ta daban wadda zai yi da iyalinsa, kuma wasu za su shiga cikinta. 'Ya'yan da za su biyo baya su ma suna da rayuwarsu da ya kamata a shirya musu," in ji Dr Achida.
Ya ce ya kamata mutum ya yi la'akari da abin da zai samu a shekarun da ke gaba, ba abin da yake da shi a yanzu kawai ba, tare da samun hangen nesa kan yadda zai kashe kuɗinsa.
Ya ƙara da cewa yana da kyau matasa su zaɓi abokan zama da za su iya taimaka wa juna, har ma a yanayin da ɗaya daga cikinsu ba ya raye.
Balaga da koshin lafiya
Masana lafiya sun ce da zarar alamun balaga sun bayyana, za a iya cewa jiki ya fara kai wa matakin da zai iya aure cikin ƙoshin lafiya.
Dr Ahmad Sabo na Jami'ar Jos ya ce baya ga alamun balaga yana da kyau ma'aurata su duba lafiyar jini da kuma ƙwayoyin halitta kafin aure, musamman idan suna shirin haihuwa.
A cewar Dr Sabo, wasu daga cikin alamun balaga tsakanin maza da mata sun haɗa da:
- Buɗewar kafaɗun namiji.
- Fara fitowar gemu ko gashin baki.
- Kumburin nono.
- Fara jin sha'awar jima'i.
- Warin jiki na sauyawa.
Dr Sabo ya ce yana da kyau mutum ya san yanayin lafiyarsa da ta wanda zai aura, domin a gano tun da wuri ko akwai wata matsala da za ta iya shafar lafiyar ma'auratan ko 'ya'yan da za su haifa.
Ya kuma ce yana da muhimmanci a duba tarihin iyali, musamman ko akwai cututtuka ko wasu matsalolin lafiya da ake iya gada.
Ta fuskar shekaru
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Yawanci, ana iya cewa daga shekara 18 zuwa sama ne mutum ke fara mallakar cikakken hankalinsa ta fuskar doka da kuma shari'a.
Farfesa Shehu Saleh, kwararre a fannin lafiyar kwakwalwa da tunanin ɗan'adam na Jami'ar Bayero da ke Kano, ya ce ba lallai ne a ƙayyade wata shekara da dole sai mutum ya yi aure ba.
Ya ce babban abin da ya kamata a duba shi ne ko mutum ya balaga, ya mallaki hankalinsa kuma yana da ikon ɗaukar nauyin iyalinsa.
"Wannan shi ne muhimmin mataki da mutum ke kaiwa na zama cikakken balagagge mai ikon yanke shawarar kansa da ɗaukar nauyin rayuwarsa," in ji shi.
Masana da dama na ganin shekarun 22 zuwa 27 sun fi dacewa da aure, saboda a wannan lokaci yawancin matasa sun kammala karatu ko koyon sana'a, kuma sun fara natsuwa da iya ɗaukar nauyi.
Sai dai masanin ya ce ba kowane mutum ne da ya kai wannan mataki na balaga ba yake da natsuwar da za a iya cewa zai iya aure ba.
Ya ce: "Ba shekaru ba ne kaɗai ake dubawa, ya danganta da balagar mutum da irin hankalin da ya samu bayan ya kai shekara 18."
Me zai faru idan mutum ya daɗe bai yi aure ba?
Ana yawan cewa idan mutum ya kai wasu shekaru ba tare da aure ba, hakan na iya jawo masa matsalolin ƙwaƙwalwa ko kuma ya sa ya fara aikata wasu ɗabi'u da ba su dace ba.
Sai dai Farfesa Saleh ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da hakan. Ya ce wasu mutane kan kai shekaru masu yawa amma ba su kai matakin da za a ce sun mallaki cikakken hankalinsu ba, yayin da wasu kuma kan nuna natsuwa tun suna ƙanana.
"Ba shekaru ne ke sa mutum ya aikata wasu ɗabi'u ba. Wani zai iya kai shekara 30 amma hankalinsa bai wuce na mai shekara 15 ba," in ji masanin.
Ya ce matsalolin da mutum zai iya fuskanta sakamakon rashin aure sun fi zama kamar irin na damuwa idan ta yi yawa ko kuma yana fuskantar tsangwama daga al'umma.
Ya ƙara da cewa babu wani bincike da ya nuna cewa ƙwaƙwalwar mutum za ta samu matsala kawai saboda bai yi aure ba.
"Wannan zai iya damunka ne kawai kai kaɗai," in ji shi.
A wani ɓangaren kuma, akwai masu ganin cewa jinkirin yin aure na iya haifar da matsalolin maniyyi, kamar taruwarsa ko kuma lalacewarsa.
Sai dai wani bincike da aka wallafa a National Library of Medicine a shekarar 2017 ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa rashin yin aure na dogon lokaci na sa maniyyi ya lalace ko kuma ya hana namiji haihuwa.
Binciken ya bayyana cewa jikin namiji yana da tsarin da ke sabunta maniyyi a kai a kai.
Ya ce yawan kwanaki ko watannin da mutum ya yi ba tare da fitar da maniyyi ba na iya ƙara yawan ruwan maniyyi da ƙwayoyin halittar da ke cikinsa a lokacin da ya fitar da shi.
A cewar binciken, da zarar mutum ya fara saduwa akai-akai, jiki kan ci gaba da sabunta ƙwayoyin maniyyi. Saboda haka, rashin yin aure na dogon lokaci ba ya hana mutum samun haihuwa a nan gaba.
Ga mace ma, binciken ya nuna cewa ƙwayayen haihuwarta ba sa lalacewa saboda rashin yin aure, kuma mace ba ta daina haihuwa don kawai ta daɗe ba ta yi aure ba.
Ilimi da fahimtar zaman zure
A cewar masana halayya, matasan da ke shirin yin aure ya kamata su kasance suna da fahimtar yadda ake tafiyar da rayuwar aure, tare da iya sarrafa fushi da mallakar hankalinsu.
Dr Achida ya ƙara da cewa ya kamata mutum ya san haƙƙoƙin abokin zamansa a kansa, musamman haƙƙoƙin da addini da al'ada suka tanada.
Samun ilimin yadda ake zama da mace ko miji cikin girmamawa, fahimta da mutunta juna na daga cikin muhimman abubuwan da ake buƙata kafin shiga aure.
Shi ma Dr Sabo ya ce ya kamata a yi la'akari da matasan da za su iya sarrafa fushinsu, da kuma waɗanda ke da ɗabi'u masu kyau.
Haka kuma, matasan da ke shirin yin aure su fahimci cewa aure ba nishaɗi kaɗai ba ne. Yana ɗauke da nauyin kula da abokin zama, haƙuri da kuma sadaukarwa.































