Yadda Musulmai ke tayar da ƙura a fagen siyasar Amurka

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

A 'yan shekarun nan, wasu 'yan siyasa Musulmai sun fara samun karɓuwa da tasiri a manyan mukaman siyasa a Amurka, abin da ya janyo muhawara mai zafi tsakanin magoya baya da masu adawa.

Daga ciki akwai ƴar majalisar dokoki Ilhan Omar da magajin garin New York Zohran Mamdani da Mohammed Abdul El-Sayed, wanda ya lashe kujerar Sanata a baya-bayan nan.

Fitowarsu na ƙara nuna yadda Musulman Amurka ke ƙara samun damar shiga a dama da su a siyasar ƙasar, duk da ƙalubalen da suka fuskanta.

To amma me ya sa abin ke zama abin cece-ku-ce?

Daga shakku bayan 9/11 zuwa samun karɓuwa

Bayan hare-haren 11 ga Satumban 2001, Musulman Amurka sun fuskanci zargin wariya da shakku a wurare da dama.

A lokacin, babban ƙalubalen da suka fuskanta shi ne tabbatar da cewa kasancewarsu Musulmai ba ta saɓa wa zama 'yan ƙasa masu cikakken haƙƙi ba.

Sai dai fitowar sabbin shugabannin Musulmai a siyasa na nuna cewa al'ummar Musulmi na samun karɓuwa fiye da yadda lamarin yake a baya, tare da mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi rayuwar jama'a kamar tattalin arziki, lafiya da ilimi.

Shin siyasar Amurka na sauyawa?

Masana na ganin cewa ƙaruwa da tasirin 'yan siyasa Musulmai alama ce ta yadda siyasar Amurka ke ƙara wakiltar bambancin al'ummomin ƙasar.

Sai dai nasarorinsu na ci gaba da janyo muhawara, musamman daga masu adawa da ke ganin wasu daga cikin manufofinsu ko akidunsu ba su dace da alkiblar siyasar Amurka ba.

Duk da haka, fitowar mutane irin su Ilhan Omar, Zohran Mamdani da Mohammed Abdul El-Sayed na nuna yadda Musulmai ke ƙara taka rawa a cibiyoyin iko na ƙasar, lamarin da ke sauya fasalin siyasar Amurka a hankali.

Ilhan Omar

,
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An samu muhawara da dama tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da 'yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Omar, musamman kan batutuwan shige da fice, Musulunci, launin fata, ta'addanci da manufofin harkokin wajen Amurka.

Ilhan Omar, wadda ke wakiltar jihar Minnesota a Majalisar Wakilai ta Amurka, 'yar siyasar Amurka ce haifaffiyar Somaliya kuma tana daga cikin fitattun masu sukar Trump.

A 2019 Trump ya yi baƙaƙen maganganu ga Ilhan Omar da wasu mata uku 'yan majalisar dokokin Jam'iyyar Democrat, dukkansu mata bakake ko masu asalin ƙasashen ƙetare, a shafinsa na Twitter.

Ya ce idan sun isa su koma ƙasashen da suka fito domin su taimaka wajen gyara matsalolinsu kafin su riƙa sukar Amurka.

Wadannan kalamai sun janyo zarge-zargen nuna wariyar launin fata da nuna ƙiyayya daga sassa daban-daban.

Omar ta mayar da martani inda ta zargi Trump da aƙidar fifita fararen fata da kuma rarraba kan al'ummar Amurka.

A wani gangamin yaƙin neman zaɓe da aka gudanar a Greenville, jihar North Carolina, magoya bayan Trump sun fara rera taken "A mayar da ita!" (Send her back!) lokacin da yake sukar Omar.

Ilhan Omar ta fuskanci suka bayan wani jawabi da ta yi inda ta bayyana hare-haren 11 ga Satumba (9/11) da kalmar "Wasu mutane sun yi wani abu".

Ta yi wannan jawabi ne tana magana kan yadda Musulman Amurka suka fuskanci ƙarin zargi, shakku da wariya bayan hare-haren na 11 ga Satumba.

Yan Jam'iyyar Republican a Majalisar Wakilan Amurka sun kada kuri'ar cire Ilhan Omar daga kwamitin harkokin waje mai tasiri na majalisar.

'Yan Republican sun ce matakin ya na da alaƙa da wasu kalamai da Omar ta yi a baya game da Isra'ila, wadanda suka dauka a matsayin masu nuna kyamar Yahudawa.

Omar ta bayar da hakuri kan wasu daga cikin kalaman da ta yi a baya, amma ta ce an dauki matakin ne saboda manufofin siyasa ba wai saboda abin da ta fada ba.

Ta kuma yi ikirarin cewa ana nuna mata wariya ne saboda ita mace Musulma ce, tana mai cewa ana kai mata hari fiye da sauran 'yan majalisa saboda addininta da asalinta.

Zohran Mamdani

.

Zohran Mamdani, magajin garin birnin New York tun watan Janairun 2026, ya fuskanci cece-kuce da suka shafi musamman batutuwan Isra'ila da Falasdinu, zarge-zargen kyamar Yahudawa, aikin 'yan sanda, da akidar gurguzu da manufofinsa na tattalin arziki.

Mamdani ya kasance mai goyon bayan haƙƙin Falasdinawa kuma ya soki manufofin gwamnatin Isra'ila kan Gaza da Gabar Yamma. Wannan ya sa ƙungiyoyin da ke goyon bayan Isra'ila da wasu 'yan siyasa suka zarge shi da nuna son kai ga Falasdinawa.

Wasu masu suka sun ce kalamansa game da Isra'ila da goyon bayansa ga yunkurin matsa lamba kan Isra'ila sun haifar da damuwa game da yiwuwar kyamar Yahudawa. Mamdani ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa sukar manufofin gwamnatin Isra'ila ba yana nufin ƙin Yahudawa ba ne.

Mamdani ya yi kira da a rage wasu kuɗaɗen da ake warewa ga rundunar 'yan sandan New York tare da ƙara saka hannun jari a fannin gidaje, ilimi da walwalar jama'a. Masu adawa da shi sun ce hakan zai iya raunana tsaro, yayin da magoya bayansa ke cewa zai magance tushen matsalolin laifuka.

A matsayinsa na ɗan siyasar da ke da alaƙa da ra'ayin gurguzu na dimokuraɗiyya (democratic socialism), Mamdani ya yi kira ga ƙarin shiga tsakani na gwamnati a tattalin arziki. Wannan ya sa 'yan Republican da wasu masu matsakaicin ra'ayi a Democrat ke zarginsa da son manufofin da za su ƙara wa gwamnati girma fiye da kima.

Abin lura shi ne cewa ba kawai masu goyon bayan Isra'ila ko 'yan Republican ke sukar Mamdani ba. Wasu masu goyon bayan Falasdinawa ma sun yi masa suka a lokuta daban-daban, suna cewa bai isa ya tsaurara matsaya kan wasu batutuwa ba.

Saboda wadannan batutuwa, Mamdani ya kasance daya daga cikin fitattun 'yan siyasar New York da ke haifar da muhawara tsakanin bangarori daban-daban na siyasa.

Mohammed Abdul El-Sayed

.

Abdul El-Sayed ya zama daya daga cikin fitattun 'yan siyasar Amurka a shekarar 2026. Dan Jam'iyyar Democrat ne, likita kuma tsohon shugaban Hukumar Lafiya ta birnin Detroit.

Yayin da ya kara samun karbuwa a siyasance, ya kuma tsinci kansa a cikin muhawara da cece-kuce da dama da suka sanya shi zama abin tattaunawa a fadin kasar.

Daya daga cikin cece-kucen da suka fi daukar hankali shi ne zargin da wasu 'yan Republican suka yi dangane da alakarsa da kungiyar Muslim Brotherhood ta Masar.

Zargin ya samo asali ne bayan 'yar uwarsa daga uba ta wallafa a shafukan sada zumunta cewa mahaifiyarsu ta taba kasancewa cikin harkokin kungiyar.

Sai dai El-Sayed ya musanta cewa ya taba kasancewa memba, yana mai jaddada cewa babu wata hujja da ke nuna yana da alaka kai tsaye da kungiyar.

Har ila yau, ya fuskanci suka saboda alakarsa da mai sharhin siyasa Hasan Piker, wanda ya shahara da ra'ayoyi masu tayar da kura.

Piker ya taba yin kalamai masu rikitarwa game da hare-haren 11 ga Satumba, inda daga baya ya nemi afuwa. Wasu 'yan Republican da ma wasu 'yan Democrat sun soki El-Sayed saboda karbar goyon bayan Piker, amma dan siyasar ya bayyana cewa ra'ayoyin Piker ba su wakiltar yakin neman zabensa ba.

A watan Maris na shekarar 2026, wani hari da aka kai kan wata majami'ar Yahudawa ta Temple Israel a wajen birnin Detroit ya haifar da wata sabuwar muhawara.

Bayan ya yi Allah wadai da harin, El-Sayed ya ce "mutanen da suka ji rauni su ne ke janyo wa wasu rauni", yana nufin rahotannin cewa wasu daga cikin dangin wanda ake zargi sun mutu a hare-haren Isra'ila a Lebanon.

Wannan magana ta janyo suka daga masu ganin kamar yana neman ba da uzuri ga harin, lamarin da ya sa daga baya ya nemi afuwa yana cewa ya bayar da bayanin ne a lokacin da bai dace ba.

A lokacin zaben fidda gwani na kujerar Sanatan Michigan na Jam'iyyar Democrat, abokan adawarsa sun kuma zarge shi da raina mata ta hanyar wasu kalaman siyasa da ya yi kan Gwamna Gretchen Whitmer da wasu fitattun mata.

Sai dai El-Sayed ya yi watsi da zargin, yana mai cewa sukar da yake yi tana nufin cibiyoyin siyasa ne da tsarin mulki, ba mata a matsayin jinsi ba.

Matsayinsa kan rikicin Isra'ila da Falasdinu ma ya jawo cece-kuce sosai. Ya bayyana yakin Isra'ila a Gaza a matsayin kisan kare dangi, tare da kira da a kawo karshen tallafin soji da Amurka ke bai wa Isra'ila.

Wannan matsayi ya jawo suka daga kungiyoyin da ke goyon bayan Isra'ila, ciki har da kungiyoyi masu karfin fada a ji da suka kashe makudan kudade wajen yakar takararsa.

Haka kuma, shugaban Amurka Donald Trump ya kai masa hare-hare sau da dama a yakin neman zaben kujerar Sanata na Michigan. Trump ya kira shi "mai tsattsauran ra'ayi na jihadi" tare da nuna shakku kan dacewarsa da kujerar Sanata saboda addininsa na Musulunci.

El-Sayed ya mayar da martani da cewa ana kokarin mayar da addininsa batu a siyasa maimakon a tattauna manufofinsa kan tattalin arziki da jin dadin jama'a.

Duk da wadannan cece-kucen, Abdul El-Sayed ya ci gaba da zama daya daga cikin fitattun muryoyi a siyasar Amurka.

Labarinsa ya hada muhimman batutuwa kamar kyamar Musulmi, rikicin Isra'ila da Falasdinu, siyasar bakin haure da kuma tambayar yadda Musulmai ke samun wakilci a manyan mukaman gwamnati. Ga 'yan jarida da masu bibiyar siyasa, wannan ya sa tafiyarsa ta zama abin kallo da nazari a shekarun da ke tafe.

Dalilan masana kan karbuwar 'yan siyasa Musulmai a Amurka

Farfesa Tukur Abdulƙadir na jami'ar jihar Kaduna ya ce akwai dalilai da dama da suka taimaka wajen sauya siyasar Amurka kan Musulman ƙasar.

Tun bayan harin 9/11 an ta amfani da kafafen yaɗa labarai wajen "ɓata sunan musulunci da Musulmai a ƙasar, to amma ƙarya fure take ba ta 'ya'ya" in ji Farfesa.

"A ƙarni na 21 mutane kan nemi bayanai a wasu wuraren sama da gidajen talabijin ko jaridu, waɗanda a baya aka riƙa amfani da su wajen yaɗa farfaganda, ɓata suna da kuma lalatawa al'uma ƙima.

"Yanzu da soshiyal midiya komai za ka samu yadda gaskiyarsa take ba yadda editoci suka tace suka aiko ba," a cewar Farfesan.

Na biyu kuma in ji masanin ya ce akwai zamani, komai yana sauyawa saboda sauyawar zamani, "Musuluncin da kansa ƙara samun karɓuwa yake tsakanin Amurkawa don haka dole fahimtar yadda yake za ta ƙaru".

Masanin siyasar duniyan ya ce faɗan da Amurka ta ke shigarwa Isra'ila, ya sa da yawan mutane sun dawo daga rakiyar Amurka da Donald Trump da kuma manufofinsa kan ƙasashen duniya.