Ma'aikatun bogi huɗu da aka gano a Najeriya a 2026

Adeniyi Adeyemi Matthew da George Buchi Nwabueze

Asalin hoton, X/Multiple

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A Najeriya an sake bankaɗo wata hukumar bogi yayin da har yanzu ba a gama da batun wadda aka bankaɗo tun farko ba, wadda a yanzu batun yake kotu.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumar yaƙi da rashawa da laifuka makamantan haka (ICPC) ta sanar cewa ta sake gano wata ma'aikatar ta bogi.

A cikin watan Yuli ne wani abu mai kama da almara ya faru a Najeriyar, inda taƙaddama ta ɓarke bayan da aka gano cewa wata ma'aikatar bogi mai alaƙa da fadar shugaban ƙasa ta riƙa wanzuwa har ma an ware mata kuɗi a kasafin kuɗi na tarayya.

Sai dai da alama har yanzu abin da ya faru a watan Yuli soman-taɓi ne, inda tun daga wancan lokaci ake ci gaba da gano wasu ma'aikatun na bogi.

Ga jerin ma'aikatun da aka gano ya zuwa yanzu:

Ofishin tsarawa da bunƙasa kayan da ake haɗawa a cikin gida

Wannan ita ce sabuwar hukuma ta baya-bayan nan da hukumar ICPC ta bankaɗo wadda a turance ake kira "National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office".

Ita wannan hukuma na iƙirarin cewa tana ƙarƙashin ɓangaren tattalin arziƙi ne na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, kuma aikinta shi ne tallata kayan da ake haɗawa a Najeriya.

Wani bayani da aka wallafa a shafin intanet na hukumar ya ce "an ƙirƙiri shirin bunƙasa kayan da ake haɗawa a Najeriya ne lokacin taron bunƙasa tattalin arziƙi tsakanin Najeriya da Singapore a shekarar 2006.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An amince da hukumar a hukumance ƙarƙashin jagorancin Ambasada Chike Alex Anigbo (MNI), kuma Majalisar zartarwar tarayya ta amince da hukumar a shekarar 2017.

Hukumar ta lissafa jerin wasu mutane matsayin masu tafiyar da al'amura da wasu jami'an tsare-tsare na shiyyoyi uku, sai jami'an tsare-tsare na jihohi 20, yayin da shi kuma George Buchi Nwabueze yake a zaman jami'in tsare-tsare kuma shugaban hukumar na ƙasa.

Shugaban hukumar ICPC, Dr Musa Adamu Aliyu wanda ya sanar da gano hukumar, ya ce "an bai wa wannan hukuma ofishi a cikin ginin ofishin sakataren gwamnatin tarayya ba bisa ƙa'ida ba".

ICPC ta zargi wani mutum mai suna George Buchi Nwabueze a matsayin wanda ke yaɗa ayyukan hukumar tare da haɗin gwiwar wasu manyan ma'aikatan gwamnati a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar ƙasar.

"An gano wanda ake zargi da ƙoƙarin yaɗa ayyukan ma'aikatar na amfani da sunaye huɗu waɗanda duk suna da alaƙa da sunansa na asali," in ji shugaban ICPC.

Shugaban na ICPC ya ce wannan sabuwar hukuma da aka gano, an bankaɗo ta ne ƙarƙashin binciken da ake yi na hukumar bogi ta farko da aka gano.

Bayan sanarwar da ICPC ta bayar a ranar Juma'a, hukumar ta ce shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin kama Nwabueze da kuma dakatar da manyan sakatarorin gwamnatin tarayya uku daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Ba kamar hukumar PFIPC da aka bankaɗo ba a farko, ita wannan hukumar babu wasu rahotannin da ke nuna cewa an ware mata wasu kuɗi a kasafin tarayya.

Sai dai mutum da ICPC ke nuna wa yatsa game da hukumar tsarwa da bunƙasa kayan da ake samarwa a Najeriya, ya fito ya bayyana cewa yana da halastacciyar takardar ba shi muƙamin.

Takardar da George Buchi Nwabueze ya wallafa a shafinsa na Instagram ta ce an naɗa shi muƙamin ne a kan ƙa'ida.

Takardar na ɗauke da kwanan watan 3 ga watan Oktoban 2026, inda take ɗauke da maudu'in: 'Naɗi a matsayin jami'in tsare-tsare na ƙasa kuma shugaban ofishin shirin kayan da haɗa a Najeriya'

Haka na takardar na ɗauke da sa hannun wani babban sakataren gwamnatin tarayya a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Takardar ta nuna cewa naɗin ya fara aiki ne a hukumance daga watan Yulin 2025 zuwa wa'adin shekara biyar.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a Instagram

Majalisar bunƙasa zuba jari da bayar da gudumawar ƙasashen waje

Hukumar bogi ta farko da aka gano ita ce Majalisar bayar da shawara kan tattalin arziƙi ta ofishin shugaban ƙasa da zuba jari da kuma bayar da gudumawa daga ƙasashen waje (PFIPC), wadda ke ƙarƙashin shugabanta Adeniyi Adeyemi Matthew.

Tun a farkon wannan wata ne ICPC ta fara bincike bayan ɓullar hukumar ta bogi da shugabanta Mista Adeniyi.

An zargi Mista Adeyemi da yin takardar bogi wadda ta ba shi damar buɗe asusun ajiye a banki mai ɗauke da sunan hukumar ta bogi.

Lamarin ya kai ga cewa majalisar dokokin Najeriya ta amince ta yi bincike kan zargin da aka yi na cewa an ware wa hukumar naira biliyan 1.302 a kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026.

Hukumar ta ICPC ta ce a binciken da ta gudanar babu shaidar da ke nuna cewa an tura wa hukumar kuɗi daga asusun gwamnati.

Haka nan ICPC ta ce an gano cewa hukumar ba ta da wata madogara a hukumance daga Majalisar Dokokin Tarayya ko kuma daga ofishin shugaban ƙasa.

Shugaban ICPC lokacin da yake miƙa wa shugaban Najeriya Bola Tinubu rahoto kan bincike game da hukumar bogi

Asalin hoton, @icpcnigeria/X

Hukumar FIPA da PPP

A lokacin da ake bincike kan hukumar PFIPC da aka bankaɗo a farko, an kuma gano wasu hukumomi guda biyu waɗanda ke da alaƙa da Adeniyi Adeyemi.

Hukumomin su ne Hukumar bunƙasa zuba jari a yankin Abuja, babban birnin Najeriya, wato FCT Investment Promotion Agency (FIPA) da kuma Hukumar bunƙasa zuba jari ta ƙasashen waje da kuma haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da ɓangaren masu zaman kansu, wato Foreign Investment Promotion Agency and Public Private Partnership (FIPA-PPP).