ICG ta yi kira ga ƙasashen Sahel su yi sasanci da JNIM
Ƙungiyar International Crisis Group (ICG) da ke Sanya idanu kan rikice-rikice a duniya ta buƙaci gwamnatocin mulkin soja a ƙasashen Mali da Nijar da kuma Burkina Faso su buɗe tattaunawar siyasa da ƙungiyar JNIM mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaeda.
Ƙungiyar ta ce cimma yarjejeniya ta hanyar tattaunawa ita ce zaɓi mafi inganci ga ɓangarorin da ke rikici da kuma miliyoyin al'ummar yankin Sahel da tashe-tashen hankulan suka shafa.
Ƙungiyar ICG ta bayyana cewa warware rikicin ta hanyar sulhu da tattaunawa na iya taimakawa wajen rage asarar rayuka da kuma wahalhalun da fararen hula ke fuskanta a yankin.
Cikin wani rahoto da ta fitar, ICG ta ce faɗaɗar ayyukan ƙungiyar JNIM da tasirinta a yankin ya ƙara bayyana a fili, musamman bayan hare-haren da ta kai ranar 25 ga Afrilu kan manyan birane bakwai na Mali, waɗanda suka yi sanadin mutuwar Ministan Tsaron ƙasar, Janar Sadio Camara, tare da jefa hukumomin riƙon ƙwarya cikin wani hali da rahoton ya bayyana da ‘’matsi’’.
Rahoton ya ƙara da cewa JNIM na kira a fili da a hambarar da gwamnatocin mulkin soja na ƙasashen Sahel, tare da neman goyon bayan masu ilimi da shugabannin siyasa da ke gudun hijira.
ICG ta ce JNIM ta faɗaɗa ayyukanta daga sansanoninta da ke Mali zuwa ƙasashen Burkina Faso da Nijar, kuma yanzu da alama tana ƙara karkata hankalinta zuwa ƙasashen yammacin Afirka da ke gabar teku, musamman Benin da Togo.
Zuwa yanzu dai hukumomin ƙasashen uku basu mayar da martani ba game da wannan kira.
Amma wani bayani daga ƙasashen na cewa suna ci gaba da matsa mata lamba ta fuskar soji ga ƙungiyar, inda suka mayar da hankali kan kare manyan birane tare da ƙoƙarin rusa shigayen da ƙungiyar ke kafawa don farmakar ayarin motocin dakon man fetur a yankin.
To sai dai a cewar ICG samun nasara ta hanyar ƙarfin soja na ƙara rasa tasiri cikin fiye da shekara 10 na rikicin.
Kan haka ne ta buƙaci gwamnatocin mulkin sojan su shiga tattaunawa da JNIM, tare da ci gaba da matsin lambar soji a lokaci guda.
Ƙasahen na yankin uku sun jima suna fukantar matsalar ayyukan ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, wani abu da suke kafa hujja da shi a lokacin juyin mulkin sojin ƙasashen.
Bayan juyin mulkin sojin ƙasashen sun kori dakarun ƙasashen waje da ke yaƙi da masu ikirarin jihadi a ƙasashen, wani da masana tsaro ke alaƙanta da ƙaruwar ayyukan ƙungiyoyin a yankin.