Yadda Rasha ta taimaka wajen murƙushe boren sojoji a Nijar

Asalin hoton, Niger Presidency
Dakaru masu biyayya ga gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ciki har da dakarun kare fadar shugaban ƙasa, tare da mayaƙa ƴan Rasha da ake kira Russia Corp ne suka daƙile boren da sojoji suka yi a ranar 29 ga watan Agusta.
Rahotanni sun ce wasu dakaru na musamman da aka tura yaƙi da ta'addanci a yankin Tillaberi da Dosso ne suka jagoranci boren.
Ministan tsaro Janar Salifou Mody ya ce wasu 'gurɓatattun' sojoji ne da ba a san ko su wane ne ba suka ƙwace iko da sansanin soji na 101, wanda ke a filin jirgin Diori Hamani, babban filin jirgin sama da ke Yamai, sannan suka ƙaddamar da hare-hare kan muhimman wurare na birnin.
"A ranar 29 ga watan Agusta...gungun wasu sojoji waɗanda suka bijire wa dokokin soji suka kai hari kan wurare daban-daban masu muhimmanci," kamar yadda kafar yaɗa labarai ta gwamnati Tele Sahel ta ruwaito a labaran yamma.
"Ɗaruruwan sojojin da suka fanɗare...sun yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu a sansanin soji na 101 da ke Yamai.
Dakarun tsaro sun mayar da martani nan take suka murƙushe barazanar...An kwashe awanni ana fafatawa a wurare da dama, amma daga ƙarshe sojoji sun yi nasarar shawo kan lamarin."
Majiyoyi na cikin gida sun ce masu boren sun so su kai farmaki a fadar shugaban ƙasar da kuma shalkwatar kafar talabijin ta gwamnati, amma an tarwatsa su, lamarin da ya haifar da rikicin da ya zo ƙarshe bayan da masu boren suka gaza shawo kan sauran dakaru su mara musu baya a ƙoƙarin tuntsurar da gwamnatin Janar Abdourahamane Tchiani.
A ɓangare ɗaya jakadan Rasha Viktor Voropayev ya ce gwamnatin Nijar ce ta buƙaci ɗaukin sojojin Africa Corp domin "murƙushe boren", wanda hakan ya kawo ƙarshen rade-radin da ake yi kan cewa sojojin na Rasha za su tsaya a tsakiya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Hakan na nufin a yanzu Rasha ta yi katsalanda a ƙasashen Sahel (AES) uku a ƙoƙarin kare sojoji masu mulki daga barazanar masu yunƙurin juyin mulki.
An murƙushe boren ne bayan da sojojin da ke kare fadar shugaban ƙasa da dakarun Africa Corp suka sake karɓe iko da sansanin 101.
Babu wani bayani a hukumance kan waɗanda aka kashe to amma an yi amannar cewa an kashe masu boren da dama.
Daga baya kafar yaɗa labaran gwamnati ta Tele Sahel ta ɗora laifin boren kan "fin ƙarfi na Faransa".
Gwamnatin mulkin soji ta Nijar ta sha ɗora wa Faransa laifi kan matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita.
Kafar yada labaran Faransa ta RFI ta ce boren sojojin ya bankaɗo ɓarakar da ke cikin rundunar sojin Faransa, musamman tsakanin jagororin sojojin da kuma ƙananan sojojin da ke fagen daga.
"Wannan wata alama ce da ke nuna cewa akwai rarrabuwar kawuna a dakarun sojin Nijar, inda aka tursasa wa gwamnati neman ɗauki daga abokan ƙawance na ƙasashen waje kafin dawo da lumana.
"Hare-hare biyu da aka kai kan sansanin sojin 101 a watan Janiru da kuma Yunin 2026, ƙungiyoyin mayaƙa na waje ne suka kai su," in ji Bakary Sambe, daraktan cibiyar nazari kan tsaro ta Timbuktu.
"Yanzu an samu lokaci na farko da aka samu fito na fito a tsakanin dakarun Nijar tun bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2023, wanda hakan zai iya zama alama ta rikicin cikin gida a cikin rundunar sojin ƙasar, shekara uku bayan Tchiani ya ƙwace mulki."
Me ya faru ranar Asabar?
Tun a tsakar dare ne aka samu rahotannin harbe-harbe da fashe-fashe a sassa daban-daban na Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.
Wasu mazauna birnin da BBC ta tuntuba sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman Diori Hamani, fadar shugaban ƙasa da kuma wasu sansanonin soji.
Wani mazaunin birnin ya shaida wa BBC cewa: "Tun misalin ƙarfe ɗaya na dare muke jin karar harbe-harbe da kuma wasu abubuwan fashewa."
Wani mutum na biyu kuma ya ce ya ji karar harbe-harben lokacin da ya tashi sallar asuba.
"Har ma mun yi addu'a a masallaci domin neman wa ƙasar zaman lafiya. Samari sun fito ƙofar gida suna tattaunawa kan abin da ke faruwa. Yawancin mutane na cewa 'yan ta'adda ne," in ji shi.
Mazauna birnin sun ce har zuwa wayewar gari ana ci gaba da jin harbe-harbe a wasu sassan Yamai.
Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motocin yaƙi masu sulke da aka tura domin ƙarfafa tsaro a yankunan da ke kusa da filin jirgin saman birnin.











