Abin da ya haifar da saɓani tsakanina da matata - Abba Kabir

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A karon farko, gwamnan jihar Kano ya yi ƙarin haske kan wasu kalamai da suka haifar da gagarumar muhawara a arewacin Najeriya.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, Abba Kabir Yusuf ya yi bayani dalla-dalla kan yadda aka samu tangarɗa a zamantakewarsa da matarsa Zainab Musa Kwankwaso, wadda ɗiya ce ga yayan tsohon gwamnan jihar Kano, kuma ɗan takarar mataimakin shugaban Najeriya a jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso.

A ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba Gwamna Abba ya yi wasu kalamai a lokacin wani taron ƴan fansho a babban ɗakin taro na gwamnatin jihar da ke birnin Kano.

Hakan ya biyo bayan raɗe-raɗin da aka riƙa yi cewa gwamnan ya samu saɓani da matarsa, bayan rahoton jaridar Daily Nigerian wanda ya Zainab Kwankwaso ta shigar da ƙara a wata kotu da ke Abuja, babban birnin Najeriya, tana buƙatar a raba aurenta da mijin nata.

Lamarin ya haifar da muhawara ganin irin alaƙar da ke tsakanin gwamnan da mariƙin Zainab, Rabiu Kwankwaso, wanda ya kasance ubangidan siyasa ga Gwamna Abba.

Me ya haifar da rikicin?

Sanye cikin farar babbar riga da jar hula mai tambarin shugaban Najeriya Bola Tinubu, Abba ya ɗan ja lumfashi sannan ya ci gaba da bayani, bayan da wakilin BBC ya tambaye shi: "mene ne bayani kan kalaman da ka furta da ake zargin magana ce game da iyalinka?"

"Irin wannan harka ta iyali abu ne mai matuƙar wahala," in ji Gwamna Yusuf.

Ya ci gaba da cewa: "Ita dai wannan mata, Zainab ƴar wansa ce (Kwankwaso), kuma ya yi masu aure amma ita auren nata bai daɗe ba, daga nan Allah Ya haɗa mu muka yi aure kimanin shekara 20 da suka wuce, kuma muna da yara.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Abubuwa da yawa sun faru, har ta kai ga aka kwashe kaya sannan aka zo aka ɗauke ta daga gidana, kuma duk na yi hakuri ban yi magana," kamar yadda Abba Kabir ya shaida wa BBC.

Daga nan gwamnan ya ƙara da cewa har ya shaida wa yaransu cewa Zainab ɗin za ta dawo gidansa.

"Kwatsam sai ga shi ya sa ta ɗirka ni a kotu, kotun ma a Abuja, ba a Kano ba," a cewar gwamnan.

Ya ƙara da cewa "abu ne babu daɗi".

Ya ce duk da cewa ba zai faɗa wa duniya yadda aka bi wajen ɗauke matar tasa daga gidansa ba, amma yana da shaidu da bayanai dalla-dalla kan yadda lamarin ya faru.

A cewarsa wannan bai kamata ya zama abin cece-ku-ce kasancewa abu ne da aka saba ganin irin hakan.

Lokacin da aka tambaye shi me ya sa ya yi wannan magana a bainar jama'a?

Sai gwamna Yusuf ya ce: "Ai ba ni ne na siyasantar da abin ba, kai yanzu idan aka yi maka haka za ka ji daɗi?"

"A kwashe wa iyalinka kaya ba da sanin ka ba, a zo a ɗauke ta a garkuwa da ita ba da sanin ka ba, a tafi da ita gidan wani, ba da sanin ka ba, sannan kawai sai ka ji cewa ita ce ta kai ka ƙara kotu."

Gwamnan ya ce ana ci gaba da duba lamarin, kuma akwai yiwuwar cewa za a samu maslaha.

BBC Hausa za ta wallafa cikakkiyar wannan hira a shafin BBC Hausa YouTube.

Wace ce Zainab Musa Kwankwaso?

Zainab Musa Kwankwaso tamkar ƴa ce ga tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata, Rabiu Musa Kwankwaso.

Asalin sunata shi ne Zainab Dahiru Musa, sai dai mahaifinta, wanda yaya ne ga tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso, ya daɗe da rasuwa.

A sanadiyyar haka ne Zainab ta taso a gidan Rabiu Musa Kwankwaso har zuwa lokacin da ya aurar da ita.

Ta auri gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, a shekarar 2006, kuma aurensu ya shafe shekara 20 inda suke da ƴaƴa shida.

Ana ganin cewa saɓani ya shiga cikin aurensu ne bayan doguwar taƙaddamar siyasa tsakanin Gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon jagoransa a siyasa, wanda kuma shi ne ke zaman uba ga matarsa, Rabiu Musa Kwankwaso.

Rikicin ya fara ruruwa ne tun bayan da Abba Kabir ya zama gwamnan jihar Kano a shekara ta 2023.

A cewar rahoton jaridar Daily Nigerian, a tsakiyar watan Nuwamban 2026, Zainab ta shigar da ƙarar neman raba aurensu a wata kotu da ke Abuja, inda kotu ta miƙa wa Gwamna Abba sammaci.

Wane ne Abba Kabir Yusuf?

Abba Kabir Yusuf shi ne gwamnan jihar Kano, jiha mafi yawan al'umma da hada-hadar kasuwanci a arewacin Najeriya.

Ya lashe zaɓen gwamna ne a shekara ta 2023, bayan ya sha kaye a shekarar 2019.

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwanksawo ya taka muhimmiyar rawa a nasarar Yusuf a zaɓen 2023, sai dai daga baya sun raba gari.

Komawar da Yusuf ya yi zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ba tare da ubangidan nasa ba ta kawo ƙarshen gomman shekaru da mutanen biyu suka kwashe suna aiki tare.

Mutane da dama sun riƙa zargin gwamnan da 'yin butulci', sai dai a tattaunawarsa da BBC Hausa, Abba ya musanta hakan.

An haifi Abba Kabir ne a ranar 5 ga watan Janairu, 1963 a ƙaramar hukumar Gaya ta jihar Kano.

Tsohon kwamishinan ayyuka a jihar Kano a zamanin mulkin Rabi'u Musa Kwankwaso.

Abba gida-gida ya yi takarar gwamna a jam'iyyar PDP a jihar Kano a shekarar 2019 amma bai samu nasara ba.