An kashe mutum huɗu a hari kan tawagar yaƙin zaɓen Omo-Agege

Asalin hoton, Omo-Agege/X
Gwamnatin Jihar Delta ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ƙaramar hukumar Ughelli North bayan wani hari da aka kai wa tawagar yaƙin neman zaɓen tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma ɗan takarar sanata na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) mai wakiltar Delta ta tsakiya, Sanata Ovie Omo-Agege.
Rahotonni na cewa harin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum huɗu tare da jikkatar wasu da dama, ciki har da masu tsaron lafiyar sanatan.
Harin ya faru ne ranar Litinin yayin ziyarar yaƙin neman zaɓe da Omo-Agege ya kai ƙauyen Uduere, inda wasu ƴan bindiga suka buɗe wa magoya bayansa wuta, lamarin da ya haddasa firgici a yankin.
Rahotanni sun ce Omo-Agege bai samu rauni ba, duk da cewa harsasai sun ratsa kusa da kansa lokacin da yake jawabi ga taron da ya taru domin tarbarsa.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu shi ne Moses Anaughe, tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Delta mai wakiltar mazaɓar Ughelli North II, kuma mataimaki na musamman ga Omo-Agege.
Rahotanni sun ce ya rasu ne a Babban Asibitin Ughelli, inda aka kai shi domin kula da lafiyarsa bayan ya samu raunukan harbin bindiga a harin.

