Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya na da biliyoyin daloli a ajiye, shin hakan alheri ne ga talaka?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
A duk lokacin da aka ambaci cewa wata ƙasa tana da tarin kuɗaɗen musaya na ƙasashen waje, yawanci ana ɗaukar hakan a matsayin alamar ƙarfin tattalin arziƙi ne, inda wasu ke tunanin za su ji daɗi.
A Najeriya kuwa, bayanai sun nuna cewa adadin kuɗaɗen ajiyar ƙasar ya kai sama da dala biliyan 54 a ƙarshen shekarar 2026, wanda shi ne mafi girman adadi cikin kusan shekara 20.
Amma duk da wannan yanayi da tattalin arzikin ƙasar ke ciki na tarin kuɗaɗe a ƙasashen waje, tambayar da ke zuciyar jama'a ita ce: me ya sa rayuwa ba ta sauƙaƙa ba?
A kasuwanni daga Kano zuwa Legas, farashin kayan abinci na ci gaba da hauhawa ne lokaci bayan lokaci. Farashin lantarki, sufuri da haya sun ƙaru, yayin da miliyoyin mutane ke fafutukar biyan buƙatun yau da kullum.
Ƙididdigar cibiyar bibiya tare da nazarin kuɗin kasafi ta Najeriya BudgIT ya nuna yadda ajiyar kuɗaɗen ƙasar ta rika canzawa daga gwamnatoci daban-daban tun daga zamanin Marigayi Umaru Musa Yar'Adua har zuwa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. A wasu lokuta adadin ya ragu ƙwarai, yayin da a wasu lokuta ya haura dala biliyan 40 ko 50.
Sai dai masana tattalin arziƙi na cewa yawan kuɗin ajiya ba lallai ba ne ya fassaru kai tsaye zuwa ci gaban rayuwar jama'a. A maimakon haka, ana kallon waɗannan kuɗaɗe ne a matsayin kariya ga tattalin arziƙin ƙasa daga girgizar farashin mai, matsin lambar musayar kuɗi, ko kuma rage ƙarfin biyan buƙatun ƙasa daga waje.
Ajiyar kuɗin Najeriya a gwamnatoci daban-daban
Bayanan da ke cikin jadawalin BudgIT sun nuna cewa lokacin da Umaru Musa Yar'Adua ya hau mulki a 2007, Najeriya tana da ajiyar kusan dala biliyan 43.48. Amma zuwa lokacin da mulkinsa ya ƙare a 2010, adadin ya sauka zuwa dala biliyan 40.10.
A gwamnatin Goodluck Jonathan, ajiyar ta fara ne da kusan dala biliyan 40.11, amma ta ƙare a 2015 da dala biliyan 29.59. Wannan raguwar na da alaƙa da faduwar farashin ɗanyen mai da kuma matsin tattalin arziƙin da ƙasar ta fuskanta a lokacin.
A zamanin Muhammadu Buhari, ajiyar ta faɗa zuwa dala biliyan 29.44 a farkon mulkinsa, sannan ta tashi zuwa dala biliyan 45.09 a shekarar 2019. Sai dai kafin ƙarshen mulkinsa a 2023 ta sake saukowa zuwa kusan dala biliyan 35.15.
Gwamnatin Bola Tinubu kuwa ta fara da ajiyar kusan dala biliyan 35.09 a watan Mayun 2023, amma zuwa ƙarshen 2026 adadin ya haura zuwa dala biliyan 54.87, wanda shi ne mafi girma cikin bayanan da jadawalin ya nuna.
Mene ne amfanin kuɗin?
A wata hira da BBC Hausa, malamin tattalin arziki a Jami'ar Northwest da ke Kano, Dokta Abdulrazak Ibrahim Fagge, ya bayyana cewa kusan kowace ƙasa a duniya tana ƙoƙarin tara wasu kuɗaɗe ko kadarori da za su zama ginshiƙin tattalin arzikinta.
"Ƙasashe da dama suna ajiye zinare da azurfa, musamman zinare, domin ya zama abin da zai ƙara wa kuɗinsu ƙarfi da daraja," in ji Dokta Abdulrazak.
Ya ce irin waɗannan kadarori ko kuɗaɗen ajiyar ƙasashen waje suna taimakawa wajen tabbatar da amincin tattalin arzikin ƙasa a idanun duniya, musamman ga cibiyoyin da ke bayar da lamuni.
"Idan ƙasa tana da kyakkyawar ajiyar kuɗaɗen waje, masu bayar da bashi za su fi aminta da ita. Amma idan ba ta da waɗannan kuɗaɗe ko sun yi kaɗan, za su yi shakku wajen ba ta lamuni," in ji shi.
Masanin ya bayyana cewa kuɗi ne kawai da ƙasashe suke ajiye domin zama kariya ga tattalin arzikin ƙasar domin shirin ko-ta-kwana.
Alaƙar ƙaruwar kuɗin da tattalin arziki
Sai dai duk da wannan muhimmanci da ake dangantawa da kuɗaɗen ajiyar ƙasashen waje, Dokta Abdulrazak ya yi zargin cewa ƙaruwar ajiyar da Najeriya ke samu a halin yanzu ba lallai ta nuna cewa tattalin arzikin ƙasar ya karfafa ba.
A cewarsa, wani babban dalilin ƙaruwar ajiyar shi ne yadda gwamnatin Najeriya ke tara dalolin da ke shigowa ƙasar maimakon sakin su cikin kasuwar hada-hadar canji.
"Da a ce an bar waɗannan daloli suna shiga kasuwa, Naira za ta samu tagomashi sosai. Wataƙila yanzu ana magana ne kan Naira 800 ko 900 kan dala ɗaya," in ji masanin.
Ya ƙara da cewa gwamnati na da dalilan tattalin arziki da suka sa ba ta son Naira ta yi ƙarfi sosai.
"Gwamnati tana samun mafi yawan kuɗaɗen shigarta ne a dala, musamman daga man fetur. Idan Naira ta yi ƙarfi, kuɗin da za ta samu idan ta sauya dalolin zuwa Naira zai ragu sosai," ya bayyana.
A nasa ra'ayin, wannan ne ya sa ake karkatar da yawancin dalolin da ke shigowa ƙasar zuwa asusun ajiyar ƙasashen waje maimakon a bar su su rage matsin da ke kan Naira.
Ya ce, "Da zarar daloli sun yi yawa a kasuwa, darajarsu za ta ragu. Idan darajar dala ta ragu, Naira kuma za ta ƙaru. Amma gwamnati ba ta son hakan ya faru cikin sauri."
Alheri ne ga talaka?
Masanin tattalin arzikin ya ce akwai bambanci tsakanin abin da gwamnati ke gani a matsayin nasara da abin da talaka ke gani.
"Idan Naira ta samu ƙarfi, farashin kayayyaki zai sauka. Hakan alheri ne ga ma'aikata da masu ƙaramin ƙarfi saboda za su iya sayen abubuwa da yawa da kuɗinsu," in ji shi.
Ya ƙara da cewa raunin Naira na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hauhawar farashi a Najeriya, musamman saboda yawan kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen waje.
"Rashin darajar Naira yana taimakawa wajen tashin farashi. Lokacin da kayayyakin waje suka yi tsada, har kayayyakin cikin gida su ma suna ƙara tsada," ya bayyana.
Dokta Abdulrazak ya yi amfani da kalmar da masana tattalin arziki ke kira money illusion wajen bayyana halin da ake ciki.
"Za ka ga kuɗaɗe suna nan kamar suna da yawa, amma a zahiri ba su da ƙarfin da za su iya aiwatar da ayyukan da ake buƙata. Wannan shi ne abin da muke kira 'money illusion'," in ji shi.
Ya yi nuni da cewa duk da ƙaruwar kuɗaɗen shigar gwamnati, har yanzu akwai manyan ayyukan raya ƙasa da dama da ke kasa samun cikakken kuɗin aiwatarwa.
A ƙarshe, lokacin da aka tambaye shi ko ƙaruwar kuɗaɗen ajiyar ƙasashen waje alheri ce ga talaka, Dokta Abdulrazak ya ce, "Ni a ganina, ba alheri ba ne ga talaka matuƙar ana tara kuɗaɗen ne ta hanyar hana Naira samun daraja da kuma hana farashi sauka," in ji shi.
Ya kara da cewa, "Abin ya fi taimaka wa gwamnati wajen cika wasu manufofinta na kasafin kuɗi fiye da yadda yake amfani kai tsaye ga rayuwar talakan Najeriya."
Sai dai masana tattalin arziki na da ra'ayoyi mabambanta kan wannan batu. Yayin da wasu ke ganin ƙaruwar kuɗaɗen ajiyar ƙasashen waje wata kariya ce ga tattalin arzikin ƙasa, wasu kuma na ganin talakawa ba za su amfana da ita ba matuƙar ba ta haifar da saukin rayuwa, raguwar farashi da karuwar darajar Naira ba.