Haaland na iya barin Man City, Liverpool na harin Jamal Musiala

Erling Haaland
Bayanan hoto, Erling Haaland
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan Manchester City Erling Haaland, na duba yiwuwar barin ƙungiyar a kakar wasannin, yayin da Barcelona ke cikin inda ya ke fatan komawa. (El Nacional - in Spanish)

Liverpool na harin ɗan wasan Bayern Munich Jamal Musiala, idan har ya iya tabbatarda cewar yana da lafiyar da zai buga wasa har zuwa ƙarshan kakkar wasanni. (Football Insider)

Manchester United na zawarcin ɗan wasan Sporting Maxi Araujo, inda ɗan wasan ke son komawa ƙungiyar nan da watan Janairu. (Sport Witness)

Atletico Madrid na son ɗaukar ɗan wasan Ajantina Julian Alvarez, yayin da Paris St-Germain da Arsenal ke harin ɗan wasan. (Teamtalk)

Chelsea na duba yiwuwar sake ɗauko ɗan wsan Jamus Antonio Rudiger, daga Real Madrid a watan Janairu. (Football Insider)

Leeds, da Brentford, da Crystal Palace na zawarcin ɗan wasan Leicester City Bismark Owusu. (Teamtalk)