"Yadda muka kama mata da ba Musulmi ba da hijabi suna satar yara a Abuja"

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Rundunar ƴan sandan Najeriya ta babbar birnin tarayya, Abuja ta ce ta sake damƙe wasu mata biyu, waɗanda ake zargi da sace ƙananan yara suna sayarwa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron ke ƙorafin yawaitar sace-sacen ƙananan yara a babban birnin tarayyar da ma wasu sassan ƙasar.

An fara kama matan guda biyu ne a shekarar 2025, bisa zargin satar wasu yara huɗu cikin har da ƴan biyu, aka gurfanar da su gaban kuliya, har ma aka yanke masu hukunci, amma bayan wata huɗu sai suka fito.

SP Josephine Ade, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan a Abuja ta yi wa BBC bayani dangane da yadda al'amarin ya faru.

"Suna sa hijabi amma ba Musulmi ba ne"

A farkon makon da ya gabata ne dai rundunar ƴansandan ta ce ta kama matan guda biyu a unguwar Gwagwa da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar birnin Abuja.

"Mun kama su a ƙoƙarinsu na satar wata yarinya mai shekara huɗu mai suna Ummi bayan sun ɗauko yarinyar sun saka ta a cikin hijabi," in ji SP Josephine.

Josephine ta ce matan waɗanda ba Musulmai ba ne suna bin kwararo-kwararo suna ɗaukar yaran da iyayensu suka aika inda suke jefa su cikin hijabi ta yadda ba za a gane ba.

"Sunan ƴanmatan biyu Blessing John da Rose Daniel. Ita Blessing ƴar jihar Benue ce ita kuma Rose ƴar jihar Enugu ce. Kuma dukkan su Kiristoci ne. Amma za ka gan su kullum a cikin hijabi. Sai suka manya-manyan hijabi ta yadda za su saka yaro a ciki ba za a gane ba," in ji SP Josephine.

"Mun kai su gidan yari amma sai muka gan su a waje"

SP Josephine Ade ta ce ba wannan ne karon farko da suke kama su waɗannan ƴan mata ba da zargin satar yara, inda ta ce ko a shekarar 2025 sai da suka kama su bisa zargin satar yara guda huɗu kuma suka gurfanar da su a gaban kotu.

"Da ma su matan shekarar da ta wuce mun kama su bisa satar yara har guda huɗu. Mun kama su ne a lokacin da suka je daukar wasu ƴan biyu. Su sayar da su a birnin Fatakwal a kan naira miliyan 1.5 kowanne yaro."

Mai magana da yawun ƴansandan ta Abuja ta ƙara da cewa bayan gurfanar da su a gaban kuliya ne alƙali ya yanke musu hukuncin zaman gidan kaso inda aka kai su gidan yari na Kuje amma kuma katsam sai ga su sun sake bayyana.

"Da muka kama su yanzu sai muka ai su ne muka tambaye su cewa ba ku ne muka tura ku gidan yari na Kuje ba? Sai suka ce e su ne wai sun yi wata huɗu a ciki sun fita. Ɗaya ma ta ce wai ba ta da lafiya kuma sai aka ba ta damar ta je idan ta warke sai ta koma gidan yarin," in ji SP Josephine.