Man City ta ɗauki Ndiaye daga Everton kan fam miliyan 65
Manchester City ta ɗauki ɗan wasan gefe Iliman Ndiaye daga Everton a yarjejeniyar da ta kai fam miliyan 65.
An kammala cinikin ɗan wasan na Senegal mai shekaru 26 a ranar ƙarshe ta kasuwar musayar ƴan wasa, inda aka biya fam miliyan 60 tare da ƙarin fam miliyan 5 idan har aka cika wasu sharuɗɗa na musamman.
''Na yi ta ƙokari tsawon rayuwata domin samun irin wannan dama," in ji Ndiaye, wanda ya amince da kwantiragin shekara biyar a filin wasan Etihad.
Ndiaye ya buga wasanni 74 tare da zura ƙwallaye 21 a Everton tun bayan komawarsa daga Marseille a shekarar 2024.
Tottenham ta cimma yarjejeniya da Everton kan batun Ndiaye a daren Juma'a, a daidai lokacin da ake ganin kamar Richarlison zai koma Everton ɗin a wani cinikin daban.
Sai dai, majiyoyi sun bayyana cewa Richarlison bai cimma yarjejeniya kan sharuɗɗan kwantiraginsa da tsohuwar ƙungiyarsa ba, lamarin da ya sa Tottenham ta kasa ci gaba da cinikin Ndiaye.