Najeriya ta musanta zarge-zargen cewa ita ko ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta Ecowas sun goyi bayan wani yunƙurin juyin mulki da ake zargin an yi a ƙasar Nijar mai maƙwabtaka da ita.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa zarge-zargen da ke yawo da su a shafukan sada zumunta “ba su da tushe bare makama, kuma wani yunƙuri ne na yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan Najeriya.”
Sanarwar ta biyo bayan zargin da wani kyaftin ɗin rundunar sojin Nijar ya yi cewa wasu gwamnatocin ƙasashen waje, ciki har da Faransa, Chadi da Côte d’Ivoire, da kuma mutanen da ke da alaƙa da hambararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum, sun shirya tsoma baki cikin wani rikicin da ya faru a wani sansanin soja a birnin Niamey makon da ya gabata.
Kyaftin Roger Gabriel, kwamandan Bataliya ta Farko ta Sojojin Saman Nijar, ya kuma yi zargin cewa shugaban ƙasar Benin, Patrice Talon, ya samu amincewar Ecowas domin shiga tsakani.
BBC ta tuntubi gwamnatoci da mutanen da aka ambata a zargin domin neman bayani.
Faransa ta ƙi cewa komai kai tsaye, amma ta shaida wa BBC cewa duk wani matakin tura sojojinta ƙasashen waje ana yin sa ne tare da haɗin gwiwar ƙasashen abokan hulɗarta.
Babu dai wanda ya tabbatar da wannan zarge-zargen da Kyaftin Gabriel ya yi, sannan kuma bai gabatar da wata hujja ba a bainar jama’a da za ta tabbatar da ikirarinsa ba.
Dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar ta yi tsami tun bayan da sojoji suka karɓi mulki a watan Yulin 2023 tare da hamɓarar da Mohamed Bazoum.
A lokacin, Ecowas ƙarƙashin jagorancin shugaban Najeriya na wancan lokaci, Bola Ahmed Tinubu, ta yi barazanar amfani da ƙarfin soja idan gwamnatin mulkin soji ba ta dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya ba. Hukumomin sojin Nijar sun yi kakkausar suka ga wannan barazana, lamarin da ya ƙara lalata dangantakar ƙasashen biyu.
Daga baya Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar takunkumi, amma ƙungiyar ta cire su a shekarar 2024. Tun daga wannan lokaci Nijar ta fice daga Ecowas tare da Mali da Burkina Faso, kuma ƙasashen uku masu mulkin soja sun kafa nasu ƙawancen yankin.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce ƙasar ta kasance tana adawa da duk wani canjin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba.
“Najeriya ba za ta taɓa goyon bayan karya doka ko sauyin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba a ko’ina, komai wanda yake da hannu ko ƙasar da abin ya shafa,” in ji sanarwar.
Ta ce tuni an fayyace matsayar Najeriya a wata sanarwa da aka fitar a ranar 30 ga Agusta bayan rikicin da ya faru a sansanin soja da ke Niamey.
“Najeriya na kallon duk wani sauyin gwamnati da ba bisa tsarin mulki ba da matuƙar damuwa. A matsayinta na maƙwabciya mai alaƙar tarihi, ‘yan’uwantaka da al’adu da Nijar, Najeriya ba ta fatan komai sai zaman lafiya, tsaro, dimokuraɗiyya da ci gaba ga Nijar, yankin da kuma Sahel baki ɗaya.”
Ma’aikatar ta ce Najeriya na ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan matsayar Ecowas da Tarayyar Afirka na kin amincewa da karɓar mulki ta hanyar juyin mulki.