Arsenal ta nace wa Osimhen, Liverpool ta tuntuɓi Madrid kan Endrick

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta tuntuɓi Real Madrid kan ɗanwasan Brazil Endrick, mai shekara 20, bayan Brighton ta yi watsi da tayin ɗanwasan gaba na Gambia Yankuba Minteh. (Times - subscription required)

Chelsea na sa ran Aston Villa za ta taya ɗanwasan gaba na Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 25. (Telegraph - subscription required)

Arsenal na nace wa ɗanwasan gaba na Galatasaray da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 27, amma sai idan ɗanwasan ya rage albashinsa da yake nema. (Footmercato - in French)

Newcastle da RB Leipzig sun tutuɓi AC Milan kan ɗanwasan gaba na Faransa Christopher Nkunku, 28. (Fabrizio Romano on X)

Atletico Madrid ta amince ta sayar wa Arsenal ɗanwasan gaba na Argentina Julian Alvarez, amma ɗanwasan mai shekara 26 ya yi watsi da buƙatar inda ya nuna Barcelona ya fi ƙauna. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Sunderland ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 8 kan ɗanwasan DR Congo Jules Ahoka, mai shekara 20 daga Royal Antwerp. (Sky Sports)

Bournemouth na dab da ɗauko aron golan Juventus Michele di Gregorio, mai shekara 29. (Gianluca di Marzio on X)

Ɗanwasan baya na DR Congo Willy Kambwala, mai shekara 21 na dab da zuwa Como daga Villarreal. (Mirror)

Ɗanwasan baya na Crystal Palace da Colombia Daniel Munoz, mai shekara 30, ana alaƙanta shi da Tottenham, amma yana nazari kan buƙatar zuwa Spurs. (Football insider)