ICPC ta sake bankado wata hukumar bogi a Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wata sabuwar hukumar gwamnati da ake zargin ta bogi ce, wadda hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasar ta gano.
Wannan lamari ya biyo bayan wani makamancin bincike da ya shafi wata hukuma da gwamnati ta ce an gabatar da ita a matsayin hukumar gwamnati, alhali ba haka ba ne.
Hukumar ICPC ta ce hukumar ta National Brands Development and Made in Nigeria Special Project Office tana gudanar da ayyukanta ba bisa ƙa’ida ba daga wani ofishin gwamnati da ke Abuja.
Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ya ce an ware wa hukumar wannan ofishin ne a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ba tare da amincewar Shugaban Ƙasa ba.
Ya bayyana cewa an gano hakan ne yayin wani babban bincike da Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a gudanar, bayan wani rahoto na baya da ya shafi Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda ake zargin ƙungiya ce da ba ta wanzu a zahiri.
A cewar Aliyu, wani mutum mai suna George Buchi Nwabueze ne ya ke tallata sabuwar hukumar, kuma ana zargin yana amfani da sunaye daban-daban.
ICPC ta ce tana binciken yadda aka ba wannan ofishi damar gudanar da ayyukansa daga harabar gwamnati, da kuma ko wasu jami’an gwamnati sun taimaka wajen ba shi damar yin hakan.
Har yanzu ba a bayyana ko Nwabueze ya samu kuɗi daga wannan zargin ba kafin a gano lamarin.
A cewar ICPC, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a kama Nwabueze ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban ƙasar ya kuma bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an gwamnati da ake zargi suna da alaka da hukumar, in ji Aliyu.
A baya dai wani bincike daban da aka gudanar kan Presidential Foreign Intervention Promotion Council, wadda fadar shugaban ƙasa ta ce ba ta bogi ce.an hukumomin da ake zargin na bogi ne.