Chiesa na shirin barin Liverpool, Haaland zai iya komawa Barcelona

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyoyin Inter Milan da Lazio da Atalanta na zawarcin ɗan wasan gaban Liverpool, Federico Chiesa, mai shekara 28, yayin da ɗan wasan na Italiya ke shirin barin filin wasan Anfield a watan Janairu. (Calciomercato)

Arsenal na da karfin tattalin arzikin ɗaukar Erling Haaland, mai shekara 26, daga Manchester City, amma alamu sun nuna cewa ɗan wasan gaban na Norway ya fi son komawa Barcelona maimakon ƙungiyar ta Emirates. (Teamtalk)

Juventus na ci gaba da nuna sha'awar ɗaukar ɗan wasan baya na gefen dama na Brentford, Michael Kayode, ɗan ƙasar Italiya mai shekara 22. (Gazzetta dello Sport)

Ɗan wasan gaban Barcelona ɗan ƙasar Spain, Dani Olmo, mai shekara 28, ba ya son barin ƙungiyar duk da raɗe-radin cewa Arsenal da Chelsea da wasu ƙungiyoyin gasar Saudi Pro-League na zawarcinsa. (Caughtoffside)

Tottenham da Liverpool na sa ido kan ɗan wasan gefe na Brighton ɗan ƙasar Japan, Kaoru Mitoma, domin yiwuwar ɗaukar sa a watan Janairu; kwantiragin ɗan wasan mai shekara 29 zai ƙare ne a bazara mai zuwa. (Teamtalk)

Ɗan wasan tsakiya mai kai hari na Mexico, Gilberto Mora mai shekara 17, ya fi son komawa Real Madrid ko Barcelona maimakon Liverpool idan ya bar Club Tijuana a shekara mai zuwa. (Football Insider)

Barcelona na sa ido kan ɗan wasan gaba Nicolo Tresoldi, mai shekara 22, wanda aka haifa a Italiya amma yake buga wa tawagar Jamus ta ƴan ƙasa da shekaru 21 wasa, kuma yana ci gaba da nuna bajinta a Club Brugge. (Sport)

Tsohon kocin Manchester City, Pep Guardiola, na shirin halartar wasan da ƙungiyar za ta buga a gasar Champions League da Paris St-Germain a ranar 14 ga watan Oktoba, domin nuna goyon baya ga tsohuwar ƙungiyarsa da ke fuskantar ƙalubale. (Express)