United da Liverpool na son Truffert, Arsenal ta dage kan Alvarez

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ana sa ran Manchester United ta fuskanci zazzafar hammayya daga Liverpool wajen siyen ɗan wasan Bournemouth Adrien Truffert, kan Euro miliyyan 60. (Teamtalk)

Ɗan wasan Brazil da Athletico Paranaense Arthur Dias, na cikin ƴan wasan da ke jan hankalin Barcelona, wanda a baya ya Tottenham ta so ɗaukarsa kan Euro miliyan 18. (Fichajes - in Spanish)

Newcastle United za ta iya yi nasara wajen shiga gaban Nottingham Forest wajen ɗaukar ɗan wasan Lyon Tyler Morton. Inda a yanzu ya ke jan hankalin a Faransa, bayan da ya bar Liverpool a shekarar da ta gabata. (Football Insider)

Liverpool, da Chelsea da Arsenal na sa ido Jarell Quansah, na ci gaba da jan hankalin Bayer Leverkusen. (Caught Offside)

Anan sa ran kyaftin ɗin Arsenal Martin Odegaard, zai bi bayan Mikel Arteta, wajen tsawaita zamansa a wata kwantaragin tsawon lokaci a Emirates. (Teamtalk)

A shirye Arsenal ta ke wajen sake taya Julian Alvarez wajen ganin ta dauko shi nan da watan Janairun mai ziwa, yayin da Atletico Madrid da ɗan wasan suka mayar da hankali ganin ya koma Arsenal ɗin. (Teamtalk)

Tsohon ɗan wasan Real Madrid Dani Carvajal , da kwantaraginsa ya ƙare, ya fuskanci koma baya kan shirinsa na komawa Getafe. (Goal)

Bayern Munich da Borussia Dortmund na harin ɗan wasan Tottenham Luca Williams-Barnett, da ya buga wasan sa na farko a Spurs, yana da shekaru16. (Sun)