KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 23/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Birtaniya za ta fara amfani da AI domin gano cutar kansar mama

    Birtaniya za ta fara gwaji mafi girma a duniya da ke amfani da fasahar AI domin taimakawa wajen gano cutar kansar mama.

    Ana gayyatar mata kusan 700,000 domin su shiga wannan gwaji.

    Za a yi amfani da fasahar AI wajen duba sakamakon hotunan sassan jiki (X-ray), domin ganin ko za ta iya inganta gano cututtuka da wuri tare da rage nauyin aiki kan ma'aikatan kiwon lafiya.

    Farfesa Fiona Gilbert na daga cikin jagororin gwajin, wadda kuma ta ce suna da yaƙinin cewa fasahar za ta taimaka wurin inganta kaifin basirar ma'aikatan lafiya kuma za a iya gano masu cutar kansa da dama.

    Kansar mama na daga cikin cutuka mafiya yawa a tsakanin matan Birtaniya.

  2. Jirgin yaƙin Rasha ya fashe a tekun Libya

    ..

    Gwamnatin yankin Libya ta bayyana cewa an samu fashewa a cikin wani jirgin ruwan yaƙi na Rasha a birnin Benghazi.

    Ana zargin harin jirgi mara matuƙi ne aka kai kan jirgin ruwan, sannan ta ƙara da cewa daga baya an kai hari kan wani jirgin ruwan kasuwanci mai ɗauke da tutar Malta.

    Mutane goma ne suka jikkata sakamakon fashewar da ta faru a jirgin na Rasha, kuma jirgin ruwan mai suna Merkury—ya kusan nutsewa.

    Ba a bayyana ko su waye ke da alhakin kai hare-haren ba.

    Sai dai ana cewa ƙwararrun 'yan Ukraine masu sarrafa jiragen sama marasa matuƙa suna aiki a yammacin ƙasar Libya.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Litinin, Mande tushen aiki da ko da nasara na tsoronki kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniyar ke ciki.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa a shafukanmu na sada zumunta.