Shin kuna son sanin lokacin da za ku bar duniya?

.
Bayanan hoto, .
    • Marubuci, Emily Doughty
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Za ku amince a yi muku gwajin da zai iya bayyana ko kuna da yiwuwar mutuwa tun da wuri?

Na amince a yi min gwajin, kuma sanin sakamakon ya sauya rayuwata.

Idan aka ba ku damar sanin ko kuna ɗauke da wata ƙwayar halitta ta gado (gene) da ka iya sa ku kamu da wata cuta da za ta rage tsawon rayuwarku, za ku amince a yi muku gwaji?

Wannan ita ce tambayar da Laura Sides ta fuskanta, bayan an ba ta damar yin gwajin da zai gano ko ta gaji wani nau'in cutar mantuwa ta Alzheimer da ba kasafai ake samu ba, wadda ke iya kama mutum tun yana ƙarami. Mahaifinta ya kamu da cutar ne tun yana ɗan shekara arba'in da wani abu.

Laura ta tattauna da Dakta Sian Williams, mai gabatar da shirin Life Changing na BBC Radio 4, game da shawarar da ta yanke ta yin gwajin, da kuma yadda sanin sakamakon ya sauya rayuwarta.

Laura tana da shekara 21 kacal lokacin da ta fara kula da mahaifinta.
Bayanan hoto, Laura tana da shekara 21 kacal lokacin da ta fara kula da mahaifinta.

Dangantaka ta kud-da-kud da mahaifinta.

Laura ta ce tun tana ƙarama take da kusanci sosai da mahaifinta, domin suna da halaye iri ɗaya.

Ta ce: "Mahaifina likitan iyali ne, kuma uba ne mai tsananin ƙaunar iyalinsa."

Yayin da cutar mantuwa ta Alzheimer ta fara tsananta, Laura ta dakatar da karatunta a jami'a domin ta kula da mahaifinta.

Ta ce: "Mun yi abubuwa da dama masu daɗi tare." Ta tuna da tafiye-tafiyen da suka yi tare, da kuma ƙananan abubuwan yau da kullum da suke jin daɗin yi tare.

Labari mai sauya rayuwa

A lokacin da Laura ta raka mahaifinta asibiti domin ɗaya daga cikin ziyarar da yake kai wa, likita ya gaya mata cewa akwai yiwuwar kashi 50 cikin 100 ita ma ta gaji cutar daga mahaifinta.

A lokacin, hankalinta ya karkata ne kacokan kan kula da mahaifinta, don haka ba ta tsaya tunanin yiwuwar ita ma ta gaji cutar ba.

Mahaifinta ya rasu a shekarar 2009, shekara guda kacal bayan rasuwar mahaifiyarta.

Bayan rasa iyayenta duka, Laura ta ji cewa tana buƙatar barin inda take domin fara sabuwar rayuwa. Ta yi tafiye-tafiye ita kaɗai zuwa ƙasashe daban-daban na duniya, kafin daga bisani ta zauna a Melbourne, Ostiraliya.

Shin ya kamata a yi gwajin ko kuwa kada ta yi?

.
Bayanan hoto, .
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin da Laura take zaune a Ostiraliya, tunanin ko ta gaji cutar mahaifinta ya fara yawan damunta.

A shekarar 2013, ta je wurin wani ƙwararren likita, wanda ya gaya mata cewa akwai gwajin da zai iya tabbatar da kusan kashi 100 cikin 100 ko tana ɗauke da ƙwayar halittar da ke haddasa cutar.

An kuma gaya mata cewa idan aka gano tana ɗauke da wannan ƙwayar halitta ta gado, ana sa ran alamomin cutar za su fara bayyana ne a lokacin da take tsakanin shekara 46 zuwa 48 da haihuwa.

Ta ce: "A lokacin, na ji cewa ban shirya sanin sakamakon gwajin ba tukuna."

Sai dai da ta shiga shekarunta na 30, sha'awarta ta gano gaskiyar abin da ke damunta ta ƙaru.

Kafin a yi mata gwajin, ta shafe tsawon watanni shida tana halartar zaman shawarwari da ƙwararrun likitocin da suka ƙware wajen gano cututtukan da ake iya gada ta hanyar ƙwayoyin halitta.

Ta ce: "Ba kasafai mutum yake samun kansa a cikin wani yanayi da ake gaya masa abin da zai iya faruwa da shi nan gaba tun kafin lokacin ba. Wannan babbar shawara ce mai matuƙar muhimmanci, kuma tana da nauyi sosai."

.
Bayanan hoto, .

Mummunan sakamako

Bayan shafe makonni shida tana jiran sakamakon gwajin, ranar da Laura za ta gano ko ta gaji cutar mahaifinta ta zo.

Ta je asibiti ita kaɗai domin karɓar sakamakon.

Ta ce: "Na gaya musu cewa mu je kai tsaye ga sakamakon."

Sai suka gaya mata cewa:

"Abin baƙin ciki, sakamakon gwajin bai yi kyau ba. Kin gaji ƙwayar halittar da ke haddasa cutar."

Laura ta ce har yanzu tana tuna wannan lokacin, inda ta ji kamar komai ya tsaya cak a gabanta.

Ta ce: "Na zauna ne kawai ina sauraron abin da suke gaya mini."

Abokiyarta, wadda ke jiranta a wajen ɗakin gwajin, ta fashe da kuka da lokacin da ta gan ta. Amma Laura ba ta nuna wata damuwa ba a lokacin.

Sai dai daga baya, yayin da ta fara fahimtar ainihin abin da sakamakon gwajin ke nufi ga rayuwarta, sai damuwa ta kama ta.

Ta ce: "Na ji haushi. Na ji kamar an zalunce ni,"

Rayuwa da sanin wannan gaskiyar

Bayan wani lokaci, Laura ta koma Ingila, musamman domin 'yar uwarta tana shirin haihuwa.

Ta kuma shiga cikin binciken kimiyya da ake gudanarwa domin ƙara fahimtar cutar da kuma gano hanyoyin magance ta.

Ta ce: "Na ji cewa aƙalla akwai wani alheri da zai iya samuwa daga wannan mummunan yanayin da na tsinci kaina a ciki."

A yanzu, Laura tana da shekara 43, kuma saura mata kusan shekaru uku ta kai shekarun da likitoci suka yi hasashen cewa alamomin cutar za su iya fara bayyana.

Ta ce: "Ina jiran ganin abin da zai faru, amma wannan tunanin ba ya hana ni barci da daddare."

.
Bayanan hoto, .

Kalubalen dangantaka

Ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi yi wa Laura wuya shi ne yadda za ta ƙulla sabuwar alaƙa da mutane.

Ta ce: "Shin zan gaya musu gaskiyar halin da nake ciki, ko kuwa in ɓoye musu? Idan kuma zan gaya musu, yaushe ne lokacin da ya dace in yi hakan?"

Ta bayyana cewa a lokuta da dama, bayan ta bayyana wa wasu mutane halin da take ciki, alaƙar da ke tsakaninsu ta lalace.

Sai dai duk da waɗannan ƙalubale, ta kuma fahimci wani muhimmin abu.

Ta ce: "Na fahimci cewa akwai mutanen da za su iya ƙaunata duk da halin da nake ciki."

Burinta na zama uwa

Laura ta ce a kodayaushe tana da yakinin cewa za ta kasance uwa ta gari.

Ta ce: "Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da ban taɓa yin shakku a kansu ba a rayuwata."

Sai dai saboda yiwuwar gadar da kwayar halittar da ke haddasa cutar ga ɗanta, Laura ta yanke shawarar cewa ba za ta haifi 'ya'ya ba.

Ta ce: "Abu ne mai matuƙar wuya a amince da irin wannan ƙaddara."

Samun farin ciki daga abubuwa ƙanana na rayuwa

A halin yanzu, Laura ta mayar da hankali ne kan jin daɗin ƙananan abubuwa na rayuwa da kuma yaba musu.

Ta ce: "Ba za ka ji ina magana kan burin zuwa Grand Canyon ko cimma wasu manyan abubuwa a rayuwa ba."

A maimakon haka, tana matuƙar jin daɗin kasancewa tare da mutanen da take ƙauna, kuma tana daraja lokutan da suke kasancewa tare.

Ta ce: "Ina son yanayi, ina son kasancewa a waje, kuma ina son ruwa."

Ta ƙara da cewa:

"Wataƙila abin da zan faɗa zai yi kama da wata tsohuwar magana da aka saba ji, amma na fahimci cewa a zahiri, ƙananan abubuwa ne suka fi muhimmanci a rayuwa."

Yayin da take tunanin shekarun da ke gabanta, Laura na da fata guda mai sauƙi amma mai ma'ana.

Ta ce: "Ina fatan zan ƙara samun wasu 'yan shekaru masu daɗi a rayuwa… ina shan Champagne da cin kawa (oysters), waɗanda suke cikin abubuwan da na fi so."