Ta yaya za ki gane cewa jinin da kike zubarwa lokacin al'ada ya zarce ƙa'ida?

Wata mata, an ɗauke ta daga baya daga kugunta zuwa ƙasa, tana cikin bandaki kuma akwai tabon jini a jikin siket ɗinta yayin da jini ke gangarowa a ƙafarta sakamakon al'ada.
Bayanan hoto, Yawan zubar jini lokacin al'ada ba wai kawai yana jawo rashin jin daɗi a jiki da zamantakewa ba, har ila yau yana iya zama alamar wasu matsalolin lafiya kuma yana iya haifar da munanan sakamako idan ba a yi magani ba.
    • Marubuci, Jacqueline Rocheleau
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 9

Tun daga shekara 12 zuwa 13, Michelle Alston ta shafe shekaru tana fama da mummunan ciwo lokacin da take jinin al'adarta na wata-wata, inda a wasu lokuta takan shafe dare a ɗakin malamar jinya da ke makarantarsu tana fama matsanancin ciwo da kuma kwararar jinin al'ada.

"Sun riƙa nuna mini cewa wannan abu ne na al'ada kawai," in ji ta.

"Sun ce mini abu ne da za ki saba da shi."

Takan samu kanta cikin damuwa saboda ba ta iya rayuwa a lokacin al'adarta kamar yadda sauran takwarorinta ke yi.

Sai da ta kai shekaru 40 da haihuwa ne ta fahimci cewa halin da take fama da shi ba shi da alaƙa da shekaru; tana zubar da jini fiye da kima a lokacin al'adarta.

Idan zubar jini lokacin al'ada ya kai matakin da yake shafar ingancin rayuwa, likitoci suna kiran hakan yawan zubar jini lokacin al'ada, kuma wata babbar matsala ce ga lafiya.

Binciken da aka yi a sassa daban-daban na duniya ya kiyasta cewa tsakanin kashi 10% zuwa 30% na matan da suke shekarun haihuwa suna fuskantar yawan zubar jini lokacin al'ada.

Kuma saboda ƙarancin kai rahoto da kuma rashin fahimta gaba ɗaya kan adadin jinin da ya wuce kima, bincike ya nuna cewa akwai yiwuwar lalurar na shafar kusan rabin matan da ke tsakankanin shekarun haihuwa.

Yawan zubar jini lokacin al'ada na iya zama alamar wasu matsalolin lafiya kuma yana iya haifar da mummunan sakamako idan ba a yi magani ba, kamar ƙarancin jini.

Sai dai a kwanan nan ne masu bincike suka fara zurfafa bincike kan tasirin yawan zubar jini lokacin al'ada, domin neman ingantattun hanyoyin gano cutar da magance ta.

Bincike a rumbun ajiye bayanai kan lafiya al'umma na PubMed game da batun jinin al'ada ya gano wallafe-wallafe 400 ne kawai a cikin shekaru goma da suka gabata.

Misali, wallafe-wallafen da suka shafi kalmar "semen" (ruwan da ke tattare da maniyyi) sun haura 15,000.

"Mata na da haƙƙin samun shekaru, idan ba shekaru masu yawa ba, na bincike," in ji Jackie Maybin, likitan mata a Jami'ar Edinburgh da ke Scotland.

Ya za ki gane jinin da ke zuba ya wuce kima?

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ga masu bincike, ana bayyana yawan zubar jini lokacin al'ada da asarar jini fiye da mililita 80 (kimanin rabin kofi ɗaya) a kowane zagayowar lokacin al'ada, ko daskararrun jini da suka fi girman tsabar kuɗi mai girman kwata (kimanin da'irar inci), ko kuma al'adar da ta zarce kwana bakwai.

Amma ga mu, da muke yin al'ada, babu wata daidaitacciyar hanya ko ma'auni don auna zubar jinin al'ada ta hanyar da ake yi a rayuwa ta yau da kullum: yawan zuwa bandaki, yawan canza audugar al'ada (pad ko tampon), ko yawan tabo a tufafin ciki.

Wasu likitoci na ƙoƙarin yin aiki tare da masu fuskantar irin wannan matsala domin tantance yawan jinin da suke zubarwa ta hanyar la'akari da audugar al'ada

Sai dai ba lallai ne wannan ya zama daidai ba, domin audugar al'ada nau'i daban-daban ne, kuma suna da bambanci sosai wajen tsotse jini.

"Wani lokaci marar lafiya ba ta gane cewa yawan jinin da take zubarwa ba na al'ada ba ne kuma ana iya yin wani abu a kai," in ji Adwoa Christy, farfesa a fannin lafiyar mata, haihuwa da kimiyyar haihuwa a Jami'ar California, San Francisco.

.
Bayanan hoto, Zanen an kamfai guda huɗu masu launuka daban-daban da ke da jajayen tabo alamar jini

Sau da yawa jinin Alston kan jiƙa zanenta ko tufafinta, kuma wata rana hakan ya faru a kan wata farar kujera a wani kantin sayar da wayar salula.

Ta ria takura saboda abin da ke faruwa, kuma ta lura cewa tana bukatar amfani da wasu kayan tare jinin al'adar saboda yawan jinin da ke zuba daga jikinta.

An nuna mata cewa fama da ciwon mara mai tsanani da tabon jini a suturarta lokacin al'ada ba wata matsala ba ce.

A wasu yankunan duniya kuma, al'adu da ƙyama da suka shafi al'ada suna munana.

"Ina ganin akwai mutane da yawa a ɓangaren duniya da ba za su yi ƙorafi ba kuma watakila saboda yadda aka ɗauki ciwo a matsayin abu na al'ada da kuma ƙyama, ba sa zuwa ganin likita," in ji Hemantha Senanayake, farfesa a fannin lafiyar mata da haihuwa a Jami'ar Colombo da ke Sri Lanka kuma daraktan Asian Society for Endometriosis da Adenomyosis.

Alston ta jira kusan shekaru 30 kafin wani ya gano matsalarta ta yawan zubar jini lokacin al'ada, kuma ba ita kaɗai ba ce.

Ba alama kaɗai ba ce

Baya ga kasancewarsa matsala da kansa, yawan zubar jini lokacin al'ada galibi alama ce ta wasu manyan matsaloli.

Matsalar na iya kasancewa alama ce ta wata matsala ta daban, kamar matsalar ƙurajen hanji, da ƙarin mahaifa da ciwon kansa da matsalolin jini da lalurar da ke shafar wurin nasa ƙwai na mace da kuma matsalolin yin ƙwai da kuma tsirar wata fata ta daban a gefen mahaifa.

Haka kuma ya zama ruwan dare, ko da yake har yanzu wani bangare ne da ake buƙatar ƙarin bincike a kai, a farkon fara al'ada da kuma lokacin shiga shekaru na daina al'ada, lokacin da canje-canjen sinadaran jiki ke gudana.

Magance waɗannan matsaloli na iya rage yawan zubar jini, amma masana kimiyya har yanzu ba su san daidai yawan jinin da wadannan lalurori ke haddasa zubarwa ba.

"An yi bincike mai yawa kan ƙarin mahaifa, amma ba a yi sosai kan dalilin da ya sa suke jawo yawan zubar jini ba," in ji Maybin, tana mai bayanin cewa ƙarin mahaifa lalura ce wadda ba ta kai kansa ba, wadda ke faruwa a cikin mahaifa.

A gefe ɗaya kuma, rashin magance yawan zubar jini lokacin al'ada na iya haifar da sabbin matsaloli kamar ƙarancin sinadarin iron.

'Iron' wani sinadari ne ne mai muhimmanci wajen kiyaye lafiyar jiki, garkuwar jiki, tsokoki, fata, gashi da farce.

Idan yawan sinadarin 'iron' ya ragu, hakan na iya janyo ruɗewa, jiri, wahalar numfashi da kuma zubar gashi.

Yawan zubar jini na iya haifar da ƙarancin sinadarin iron, wanda ke janyo ruɗewar tunani, jiri, gajiya kuma zai iya rikidewa zuwa ƙarancin jini.

Wata mata tana kwance a kan kujera da alamun gajiya, ta riƙe kanta da hannayenta yayin da idanunta suke rufe.
Bayanan hoto, .

Saboda haka, illolin yawan zubar jini lokacin al'ada na ci gaba har bayan lokacin al'adar kanta: bincike ya kiyasta cewa fiye da kashi 40% na matan da ke fama da yawan zubar jini lokacin al'ada suna kuma fama da ƙarancin sinadarin iron.

Alston ta kasance cikin wannan rukunin: kullum tana jin ɗari kuma sau da yawa tana sha'awar taunawa ko shan ƙanƙara, wata alama ta ƙarancin sinadarin iron mai ban mamaki amma wadda har yanzu masu bincike ba su fahimta sosai ba.

Idan ba a yi magani ba, ƙarancin iron na iya rikidewa zuwa ƙarancin jini, inda ɓargon ƙashi ba zai samu isasshen sinadarin iron don samar da sinadarin haemoglobin da ake buƙata domin jajayen ƙwayoyin jini su isar da iska yadda ya kamata a jiki ba; wani mummunan yanayi da zai iya buƙatar ƙarin jini a wasu lokuta.

A ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, inda zubar jini ke daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da mutuwar mata masu juna biyu, Senanayake ya ce idan ba a magance ƙarancin jini sakamakon ƙarancin iron ba kafin ɗaukar ciki, hakan na iya lalata ƙarfin jiki wajen farfaɗowa daga asarar jini.

Haka kuma yana iya shafar bunƙasar kwakwalwar jariri a cikin mahaifa.

Wani matamaza  yana sauraron wata likita yayin wata ganawa ta asibiti.

Magunguna da gwaje-gwaje

Har yanzu akwai aiki mai yawa da ya rage a yi.

Ko da yake akwai magunguna kan lalurar yawan zubar jini lokacin al'ada, "tabbas ba su isa ba," in ji Erica Marsh.

"Muna da ƙarancin mafita kuma abin na da ban-tsoro."

Maganin yawan zubar jini lokacin al'ada ya danganta da asalin matsalar.

Idan zubar jinin bai yi tsanani sosai ba, magungunan rage raɗaɗi waɗanda ba sa dauke da sinadarin steroid kamar ibuprofen na iya rage yawan jinin.

Akwai kuma magungunan da ke daidaita sinadaran jiki kamar kwayoyin hana ɗaukar ciki ko na'urorin da ake sakawa a mahaifa, waɗanda suke daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen rage asarar jini lokacin al'ada.

Duk da cewa waɗannan hanyoyin suna da sauƙin samu, akwai abubuwan da kan hana amfani da su, kamar lalurorin da ke iya hana a saka wani abu a cikin mahaifa.

Kwayoyin hana ɗaukar ciki sun yi aiki ga Alston, amma saboda ƙyamar da ke kewaye da su a gidansu, sai da ta manyanta kafin ta iya amfani da su.

Magungunan da ke tasiri ga sinadaran jiki ba sa aiki ga kowa, kuma mutane da yawa suna daina amfani da su saboda abin da suke haifarwa, kamar ciwon nono da sauyin yanayi.

Akwai magunguna marasa hormones kamar tranexamic acid da za su iya dakatar da zubar jinin.

"Matsalar ita ce kusan kamar bandeji ne kawai," in ji Jaffray, "ba sa magance asalin matsalar."

Wata mata da ba a ga fuskarta ba tana tsaye a gaban madubi a bandaki tana riƙe da fakitin kwayoyin hana ɗaukar ciki.
Bayanan hoto, Wata mata da ba a ga fuskarta ba tana tsaye a gaban madubi a bandaki tana riƙe da fakitin kwayoyin hana ɗaukar ciki

Daga baya wani likitan mata ya yi mata binciken hoton ultrasound kuma ya gano wasu abubuwa da ake zargi.

"Ta ce mini, 'Ki manta da magungunan hana ɗaukar ciki. Kina da manyan ƙari guda 7 ko 8 a mahaifarki kuma wataƙila kina da lalurar tsirowar fata a gefen mahaifa,'" in ji Alston.

A sakamakon haka, ta yanke shawarar yin tiyatar cire mahaifa gaba ɗaya.

A gaskiya ma, yawan zubar jini lokacin al'ada na daga cikin mafi yawan dalilan da ke tursasa wa mata cire mahaifa.

Ta gamsu da shawarar da ta yanke, kuma tarihin yawan al'adarta ya ƙare.

Amma aikin cire mahaifa babbar tiyata ce, idan aka yi ta babu batun sauyi, kuma ba za a iya ɗaukar ciki ba har abada.

Ga Maybin, takaici da kunyar da ta ji game da yanayin lalurarta ne suka sa ta jagoranci 'The Missed Vital Sign', wani shirin yin bincike wanda gidauniyar Wellcome Leap ke tallafa wa.

Sunan shirin yana nuna ra'ayin cewa canje-canjen al'ada na iya zama alamar farko ta wasu matsalolin lafiya, wanda ke sa al'ada ta zama wata muhimmiyar alamar ciwo kamar hawan jini, zafin jiki ko bugun zuciya.

A cikin shekaru uku masu zuwa, ƙungiyoyin masu bincike guda 13 za su yi aiki domin rage jinkirin ganowa da magance yawan zubar jini lokacin al'ada.

Wani bangare na wannan aiki shi ne zurfafa fahimtar hanyoyin da ke haddasa yawan zubar jini da kuma musabbabinsa.

.
Bayanan hoto, .

Ta fuskar fasaha, Maybin na ganin faduwa ta zo daidai da zama saboda sabbin fasahohin bincike da ke bayar da damar yin nazarin ƙwayoyin halitta cikin hanzari.

"A baya, ba a yi amfani da waɗannan fasahohi don inganta lafiyar mata ba, kuma ina ganin lokaci ya yi da za a yi hakan," in ji Maybin.

Haka kuma Jaffray ta yi aiki wajen haɗa ƙwararrun likitocin jini a ɓangaren yawan zubar jini lokacin al'ada, tana jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin ƙwararrun jini da likitocin mata.

Sai dai muhimmin bangare na wannan ci gaba shi ne tabbatar da cewa masu fama da yawan zubar jini lokacin al'ada za su iya samun sabbin hanyoyin gano cutar da magance ta.

Masu bincike suna ƙara fahimtar cewa bai wa yawan zubar jini lokacin al'ada muhimmanci a bincike da magani yana da matuƙar amfani wajen taimaka wa mata da duk masu yin al'ada su rayu yadda ya kamata, ba tare da ruɗewar tunani sakamakon ƙarancin sinadarin iron ba, kuma ba tare da hakan ya zama ƙalubale ga karatu ko aikinsu ba

"Dole ne mu ɗauki mata da muhimmanci sosai," in ji Alston.

"Muna buƙatar kulawa mai kyau domin mu samu damar aiwatar da haƙƙinmu na daidaito na kasancewa a wannan duniya."