Manyan ayyuka da gwamnatin Tinubu ke iƙrarin yi a arewacin Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Martani na ci gaba da baibaye kalaman shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda wanda ya bayyana cewa arewacin ƙasar ne ya fi cin moriyar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Farfesa Yilwatda, a wani taron ƙwararrun jam'iyyar APC da aka yi wa taken "hisabin gwamnatin Tinubu', da aka gudanar ranar Laraba a Abuja, ya ce arewacin Najeriya mafi cin gajiyar romon dimokraɗiyya ta fuskar tattalin arziƙi.

"Waɗanda za su fi cin gajiyar wannan tattalin arziƙi su ne yankin Arewacin Najeriya, domin yanzu za su riƙa kasuwanci da ƙasashe maƙwabta, su yi hulɗar kasuwanci da Nijar, da Chadi, da Burkina Faso, da Sudan ta Kudu, da Arewacin Kamaru, da Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. Saboda haka, Arewa ce za ta zama sabuwar cibiyar kasuwanci mafi muhimmanci a Najeriya," in jni Yilwatda.

To sai dai BBC ta tuntuɓi Abdul'aziz Abdul'aziz ɗaya daga cikin mataimakan shugaba Tinubu dangane da ayyukan da ake yi wa arewacin da za su ɗaga likkafar yankin.

Ayyukan manyan tituna

1) Babbar hanyar mota ta Sokoto zuwa Badagry

Babbar Hanyar Sokoto zuwa Badagry wani katafaren aikin hanya ne mai tsawon kilomita 1,068, wanda aka tsara da hanyoyi masu faɗi da layuka da dama domin haɗa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya kai tsaye da gabar Tekun Atlantika da ke Legas.

An fara tunanin aiwatar da wannan aiki tun shekaru da dama da suka gabata, amma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ce ta sake farfaɗo da shi tare da ƙaddamar da aikin a hukumance a watan Oktoban 2024.

An kiyasta cewa jimillar kasafin kuɗin dukkan matakan wannan aiki, wanda zai ratsa jihohin Sokoto, Kebbi, Neja, Kwara, Oyo, Ogun da Legas, za ta haura tiriliyan 10 naira (₦10tn) idan aka kammala shi gaba ɗaya.

2) Titin Sokoto–Gusau–Funtua–Zaria

Babbar Hanyar Sokoto zuwa Gusau zuwa Funtua zuwa Zariya wani muhimmin titin sufuri ne na gwamnatin tarayya mai tsawon kilomita 750, wanda ke haɗa jihohin Sokoto, Zamfara, Katsina da Kaduna a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Hanyar na taka muhimmiyar rawa wajen sauƙaƙa safarar kayan amfanin gona, inganta kasuwanci tsakanin jihohi, da kuma ƙarfafa haɗin kai da zirga-zirga a tsakanin yankunan da ta ratsa.

3) Babbar hanyar Kano-Maiduguri

Babbar Hanyar Kano zuwa Maiduguri (Kano-Maiduguri Road) wata muhimmiyar hanyar tarayya ce da ke haɗa jihohin Kano, Jigawa, Bauchi, Yobe da Borno a Arewacin Najeriya.

Hanyar tana daga cikin manyan hanyoyin sufuri da kasuwanci a ƙasar, domin tana sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.

Haka kuma, tana da muhimmiyar rawa wajen safarar kayan amfanin gona, bunƙasa kasuwanci, da ƙarfafa alaƙar tattalin arziƙi tsakanin al'ummomin da ke yankunan da ta ratsa.

4) Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano

Babbar Hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano wata katafariyar hanya ce da aka tsara domin inganta zirga-zirga da harkokin kasuwanci tsakanin Babban Birnin Tarayya Abuja da manyan cibiyoyin tattalin arziƙi da ke Arewacin Najeriya, wato Kaduna da Kano.

Hanyar na daga cikin muhimman ayyukan more rayuwa da ake sa ran za su rage lokacin tafiya, sauƙaƙa jigilar kayayyaki da mutane, da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin yankunan da ta ratsa.

Babbar Hanyar Abuja-Kaduna-Zariya-Kano tana da tsawon kusan kilomita 375.9. An raba ta zuwa sassa uku:

  • Abuja zuwa Kaduna: kilomita 165.5
  • Kaduna zuwa Zariya: kilomita 73.4
  • Zariya zuwa Kano: kilomita 137

5) Titin ratse na Lafiya Bypass

Lafia Bypass da ke jihar Nasarawa wata hanyar ratse ce ta shiga tsakiyar birnin Lafiya da aka gina domin rage cunkoson ababen hawa da sauƙaƙa zirga-zirga ga matafiya masu wucewa ta jihar.

Hanyar ta zama madadin hanyar da ke ratsa cikin birnin Lafiya ga masu tafiya tsakanin Abuja da Makurdi da sauran yankunan gabashin Najeriya.

Manyan ayyukan Lafiya
  • Cibiyoyin Gudanar da Ayyukan Gaggawa a Kano da Sokoto da Katsina.
  • Cibiyar Kula da Masu Mummunan Rauni a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello (ABUTH) da ke Zariya.
  • Cibiyar Ƙasa ta Kiwon Lafiyar Jama'a da Cututtuka Masu Yaɗuwa a Zariya.
  • Asibitin Ƙashi na Kwararru a Maiduguri.
  • Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Kafanchan a Jihar Kaduna.
  • Jami'ar Tarayya ta Kimiyyar Lafiya da Fasaha da ke Tsafe, Jihar Zamfara
Manyan ayyukan a fannin ilimi
  • Jami'ar Tarayya ta Kimiyya da Fasaha da ke Kabo, Jihar Kano.
  • Ƙaddamar da gyare-gyare da ke ƙarfafa bincike da ilimin kimiyya a kwalejin koyon aikin soji ta NDA a Kaduna.
  • Kammala azuzuwa a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya ta Hussaini Adamu da ke Kazaure a jihar Jigawa, ƙarƙashin TETFund da aka ƙaddamar.
  • Gina ɗakunan kwana a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta tarayya da ke Hussaini Adamu da ke Kazaure.
  • Gina ɗakunan kwana na ɗalibai a jami'ar Sa'adu Zungur University, da ke Gaɗau a jihar Bauchi a kan kuɗi naira miliyan 738.96.
  • Samar da wutar solar mai yawan megawatts 2 a Jami'ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Jihar Kano.
  • Gina Tsangayoyin Kimiyya da ɗakunan karatu a jami'ar jihar Nassarawa ta Nasarawa State College of Education, Akwanga
Martanin ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF)

Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta yi watsi da iƙirarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu cewa Arewacin ƙasar ne ya fi cin moriyar ayyukan gwamnatinsa.

ACF ta bayyana ikirarin Shugaba Tinubu a matsayin abin mamaki da ya yi kama da mafarki, kalamai masu nuna rashin tausayi da kuma waɗanda ba su yi la'akari da yanayin da jama'a ke ciki ba.

A ta bakin kakakinta, Farfesa Tukur Muhammad Baba, ƙungiyar ta ACF ta ce yana da wuya a daidaita wannan iƙirari na shugaban ƙasar da hakikanin matsalolin tattalin arziƙi da zamantakewa da ke addabar miliyoyin al'umma a faɗin Arewacin Najeriya.

"Wannan furuci abin mamaki ne ƙwarai, har ma yana nuna rashin la'akari da halin da jama'a ke ciki, kuma bai dace da yanayin ba. Amma wataƙila za a iya yi masa uzuri, domin bai gabatar da cikakkun bayanai ko hujjoji da za a iya tabbatarwa ba, kuma bai bayyana ta wace hanya ko ta yaya Arewa ta fi amfana ba. Wataƙila ma yana nufin Legas maimakon Arewa ne," in ji Farfesa Tukur.

Baba ya ƙara da cewa irin girman talaucin da ke arewacin Najeriya ya saɓa da iƙrarin shugaban na Najeriya.

"Ta yaya za a ce Arewa ce ta fi cin moriya alhali kuwa alamu a fili suke nuna cewa talauci na ƙaruwa a yankin, wanda ya zama yankin da talauci ya fi ƙamari a Najeriya, kuma a kowace rana mutane na ƙara shiga cikin talauci tare da fuskantar matsalolin tattalin arziƙi da sauran ƙalubalen rayuwa?," kamar yadda Farfesa ya yi tambaya.