Abin da Christa Pike ta furta bayan farfaɗowa daga allurar mutuwa
Christa Pike ta miƙe tana iya tattakawa a cikin ɗakin asibiti bayan yunƙurin da aka yi na zartar mata da hukuncin kisa a makon da ya gabata ya ci tura, in ji ɗaya daga cikin lauyoyinta.
Pike, mai shekara 50 a duniya, an yanke mata hukuncin kisa ne bayan ta kashe wata matashiya mai suna Colleen Slemmer tare da hadin gwiwar saurayinta a shekarar 1995.
Pike ba ta mutu ba bayan an yi mata allurar mutuwa har guda biyu a ranar 30 ga watan Satumba. Masana sun nuna matuƙar mamaki kan wannan lamari.
Tawagar lauyoyinta sun ce ta farfaɗo a kan gadon asibiti kuma ta fara magana, inda ta tashi a fusace amma da alamar ruɗani a tattare da ita.
Lauyanta ce a lokacin da ta farfaɗo ta ce “Ku su waye, a ina nake?” kamar yadda ta tambayi malaman jinya da ke a cikin ɗakin.
A tattaunawa da BBC, lauyan Christa, Stephen Ferrel ya ce duk da bai tattauna da ita kai-tsaye ba amma an shaida masa cewa zuwa yammacin Talata ta yi magana kuma tana iya tattakawa a ɗakinta na asibiti.
Ya bayyana cewa babu tabbas kan abin da zai faru gare ta a nan gaba, amma akwai damuwar cewa allurar da aka yi mata na iya illata wani ɓangare na jikinta.
Babu tabbas kan abin da zai zama makomar Pike, bayan da lauyoyinta suka buƙaci a yi watsi da hukuncin kisan da aka yanke mata bayan faruwar lamarin.