Rundunar Sojin Saman Najeriya ta ce wani jirgin helikwafta
da aka gani yana sauka a wata gona a Jihar Benue yana dawowa ne daga wani
samame kan mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutane.
Wasu hotuna da ba a tabbatar da sahihancinsu ba da suka
bayyana a intanet sun nuna jirgin helikwaftan na soja a cikin wata gona, inda
rahotannin farko suka ce ya yi saukar gaggawa.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis, Rundunar
Sojin Saman ta ce jirgin ya sauka ne don kauce wa hadari a wani wuri mai
tazarar kusan mil 10 daga sansaninsa, bayan kammala wani samame.
Rundunar ta ce jirgin helikwaftan ya bai wa sojojin kasa
taimako ta sama yayin wani farmaki kan mutanen da ake zargi da yin garkuwa da
mutane a Ogbadigbo, kusa da iyakar jihohin Enugu da Benue.
A cewar rundunar, samamen ya tarwatsa kungiyar da ake zargi
da aikata laifukan, tare da taimaka wa sojojin kasa wajen ci gaba da kutsawa
yankin.
Rundunar Sojin Saman ta ce matukin jirgin ya yi saukar
gaggawar ne a matsayin matakin kariya, bisa ka'idojin tsaro da ake bi bayan
kammala samame.
Sanarwar ta ce jirgin helikwaftan ya koma sansaninsa sannan rundunar
ba ta bayar da rahoton jikkatar kowa ko lalacewar jirgin ba.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa na ci gaba da
kasancewa babbar matsalar tsaro a Najeriya, musamman a arewacin kasar.
A tsakanin Yulin 2025 da Yunin 2026, an bayar da rahoton
sace mutum 7,825 a hare-hare 1,411, a cewar SBM Intelligence, wata kungiyar
nazarin harkokin tsaro da ke Legas.
Jihar Benue da ke
tsakiyar Najeriya ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da suka
shafi kungiyoyi masu dauke da makamai, rikicin manoma da makiyaya,
rikice-rikicen tsakanin al'ummomi da kuma garkuwa da mutane.
Tsakanin Janairun
2024 da Agustan 2025, ACLED ta tattara bayanan afkuwar matsalolin tsaro 406 da
suka yi sanadin mutuwar mutum 1,338 a jihar.
Har ila yau, tashe-tashen hankulan sun tilasta wa dubban
daruruwan mutane barin muhallansu.