Boxing Day: Yadda aka samo sunan ranar washe garin Kirsimeti da asalinta

Xmas: "Boxing Day"
An wallafa

"Boxing Day" - rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti - ta samo asali ne a lokacin mulkin Sarauniyar Ingila Victoria a shekarun 1800.

Ranar ba ta da wata alaƙa da wasan damben boxing da ake gudanarwa a faɗin duniya.

Sunan ya samo asali ne sakamakon ƙunshe kyauta da masu arziki ke yi a cikin akwati kafin su bai wa mabuƙata - 'box' na nufin akwati a harshen Hausa.

Boxing Day a al'adance, ita ce ranar da bayi kan yi hutun aiki sannan su karɓi kyautuka na musamman daga iyayen gidansu.

Haka nan, a ranar ce su ma suke zuwa gida domin bai wa iyalansu akwatunan kyautar.

A yankunan Catalonia na Spain da Ireland na Birtaniya, suna yin bikin ranar ne da sunan "Saint Stephen's Day".

A ƙasashen Turai kuma kamar Hungary da Jamus da Poland da Netherlands, suna kallon Boxing Day a matsayin Ranar Kirsimeti ta biyu.

Kirsimeti: "Boxing Day"
Bayanan hoto, Sarauniyar Ingila Victoria ce a kan mulki lokacin da aka fara al'adar Boxing Day ta bai wa talakawa kyauta a cikin akwati

Tara kuɗi

Su ma coci-coci sun taka rawa wurin ƙirƙirar Boxing Day. Sukan karɓi kuɗi daga masu bauta a tsawon shekara baki ɗaya domin bai wa mabuƙata a lokutan Kirsimeti.

Sukan ajiye kuɗin a cikin akwatuna kafin a buɗe su a Ranar Kirsimeti, sai kuma a bai wa mabuƙata kwana ɗaya bayan Kirsimeti wato Boxing Day.

Sai dai a yanzu ba a fiya amfani da akwatunan ba kamar da.

Xmas: "Boxing Day"

Yaushe ne Boxing Day?

Boxing Day, ita ce rana ta farko bayan Ranar Kirsimeti, wadda ke faɗowa ranar 26 ga kowane Disamba.

Kuma rana ce ta hutu a Najeriya da wasu ƙasashen duniya.

Idan ta faɗo ranar Asabar, akan mayar da hutunta zuwa Litinin ta gaba.

Idan kuma ta faɗo ranar Lahadi, to ranar Talata ne hutun.

Xmas: "Boxing Day"
Bayanan hoto, Wasu masu bikin Kirsimeti kenan a bakin ruwan Elegushi da ke Jihar Legas