Cikin hotuna: Abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya

Ranar Litinin tauraro Sani Danja(dama) ya wallafa hoton ziyarar da suka kai wa gwanman jihar Bauchi, Bala Mohammed( tsakiya) tare da amininsa, Yakubu Mohammed(hagu) domin taya shi murnar yin nasara a kotun koli.
Bayanan hoto, Ranar Litinin tauraro Sani Danja (dama) ya wallafa hoton ziyarar da suka kai wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed (tsakiya) tare da amininsa, Yakubu Mohammed (hagu) domin taya shi murnar yin nasara a kotun koli.
An wallafa
Khadija Mustapha
Bayanan hoto, Ranar Laraba Khadija Mustapha ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta, wato birthday
Ranar Laraba, tauraruwa Rahama Sadau, ta wallafa wannan hoto tare da Adam Zango inda take cewa shi kadai ne Yariman da ta sani a masana'antar Kannywood.
Bayanan hoto, ...A ranar ne tauraruwa Rahama Sadau, ta wallafa wannan hoto tare da Adam Zango inda take cewa shi kadai ne "Yariman da na sani" a masana'antar Kannywood.
...washegari Adam Zango ya wallafa hotonsa da matarsa, Safiya, yana mai cewa "Daga ke sai..."
Bayanan hoto, ...washegari Adam Zango ya wallafa hotonsa da matarsa, Safiya, yana mai cewa "Daga ke..." ba kowa ko?
Ali Nuhu a cikin fim mai suna A Call To Service, wanda aka yi domin wayar da kan masu yi wa kasa hidima a Najeriya
Bayanan hoto, Ali Nuhu a cikin fim mai suna A Call To Service, wanda aka yi domin wayar da kan masu yi wa kasa hidima a Najeriya
Falalu Doraya(hagu) da Nazifi Asnanic
Bayanan hoto, Falalu Doraya (hagu) da Nazifi Asnanic suna tattaunawa. Me suke cewa ne?
Abba Almustapha
Bayanan hoto, Abba Almustapha ya wallafa wannan hoto a shafinsa na Intagram ranar Juma'a inda yake godiya ga Allah bisa samun digiri mai daraja ta biyu
Nuhu Abdullahi
Bayanan hoto, Mene ne ya yi wa Nuhu Abdullahi dadi, a sanya shi kyakkyalewa da wannan dariya?