Hotunan abubuwan da suka faru makon jiya: Shin Ganduje zai rantse da Alkur'ani?

Peter Ayodele Fayose
Bayanan hoto, Da safiyar Litinin ne hukumar EFCC da ke yaki da masu yi a tattalin arzikin Najeriya ta'annati ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Ekiti Peter Ayodele Fayose a gaban wata kotun birnin Lagos bisa zargin cin hanci da rashawa.
An wallafa
Nasir Elrufai
Bayanan hoto, Ranar Talata, Gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufai ya kai ziyara asibitin St. Gerards domin duba mutanen da suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke a wasu sassan jihar a makon jiya
Ganduje
Bayanan hoto, Ranar Laraba, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yana kallon wasan karshe na cin kofin kalubale da kungiyar kwallon kafar Kano Pillars ta fafata da Enugu Rangers a talbijin...
Jaafar
Bayanan hoto, ...washegari, dan jaridar nan, Jaafar Jaafar, wanda ya fitar da bidiyon da ke zargin Gwamna Ganduje na karbar cin hanci daga wurin 'yan kwangila, ya bayyana a majalisar dokokin jihar Kano domin bayar da ba'asi. Ya sha alwashin rantsuwa da Alkur'ani inda ya kalubalanci gwamnan shi ma ya rantse
...ranar Alhamis din ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon ginin hada-hadar fasinjoji a filin jirgin saman Fatakwal da ke jihar Ribas.
Bayanan hoto, ...ranar Alhamis din ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabon ginin hada-hadar fasinjoji a filin jirgin saman Fatakwal da ke jihar Ribas.
Alhaji Atiku Abubakar
Bayanan hoto, Ranar Juma'a dan takarar shugabancin Najeriya a PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya wallafa wannan hoton a shafukansa na sada zumunta inda ya ce yana sake bibiyar takardun da ke kunshe da kudure-kudurensa na yi wa kasar garambawul, wadanda zai gabatar wa 'yan Najeriya...
Da almurun ranar ne aka karrama taurarin gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bana
Bayanan hoto, ...da almurun ranar ne aka karrama taurarin gasar Hikayata ta BBC Hausa ta bana