Hotunan bikin Maulidin Shiekh Ibrahim Nyass a Abuja

Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Dubun dubatar musulmi mabiya darikar Tijjaniyya daga kasashen Afirka daban daban ne suka halarci taron Mauludin Sheikh Ibrahim Nyass a Abuja.
An wallafa
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, An gudanar da taron ne a dandalin Eagle Square da ke tsakiyar birnin Abuja.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Mauludin shi ne karo na 32 da aka gudanar a Najeriya domin tunawa da Sheikh Ibrahim Nyass.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Babban malamin darikar Tijjaniya a Najeriya Shiekh Dahiru Bauchi tare da ministan Ilimi Malam Adamu Adamu wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Maulidin ya kunshi bikin murnar zagayowar haihuwar Shiekh Nyass shekaru 118.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Darikar wadda Wani malami Sidi Ahmad Tijjani ya assasa a shekarar 1784 a Algeria tana daya daga cikin darikun addinin musulunci mafi yawan mabiya a yammacin Afirka.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, An toshe hanyoyi da ke zuwa Babban masallacin Juma'a a Abuja zuwa dandalin Eagle Square saboda maulidin.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Mabiya darikar Tijjaniya sun yi imani da yi wa waliyai hidima da nufin samun kusanci ga Allah da kuma neman samun ceton waliyan.
Mauludin Sheikh Ibrahim Niass
Bayanan hoto, Tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cikin manyan 'yan siyasar Najeriya da suka halarci Maulidin da aka kammala a ranar Asabar.