Mai sayar da ragon sallah da mai kamun kifi cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Wasu daga cikin zaɓaɓɓun hotuna daga Afrika da na ƴan Afrika daga wasu sassan duniya.

Senegal
Bayanan hoto, Yadda aka zana illar haƙar kwalta jikin wata katanga a babban birnin Senegal, kamfanonin Apple da Google da sauransu sun ƙaryata zargin cewa suna amfani da yara ƙanana wajen haƙar kwalta.
Kongo
Bayanan hoto, Cikin wannan zanen kuma an nuna yanayin da ƙasashen Sudan da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo da kuma yankunan Falasɗinawa ke ciki.
Zanzibar
Bayanan hoto, Wata yarinya ɗaliba na karanta harfofi a makarantar su da ke Zanzibar.
Ragon layya
Bayanan hoto, Washegari a jihar Lagos, wani ɗan kasuwa na duba ragon da zai sayar lokacin sallah.
Masar
Bayanan hoto, Lokacin girbin kayan amfanin gona a Wadi El Natrun da ke Masar.
Super Eagles
Bayanan hoto, Mai goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya na farin cikin nasarar da ƙungiyar ta yi a kan takwararta ta Jamaica a Birtaniya ranar Asabar.
Senegal
Bayanan hoto, A ranar ne kuma aka gudanar da bikin Niumi Badiya a iyakar Senegal da Gambia, inda ƴan rawa suka cashe.
Senegambia.
Bayanan hoto, Bikin da ke nuna al'adun yankin ana kiransa da Senegambia.
Sacuur
Bayanan hoto, A ranar ne kuma mutanen tsibirin Joal-Fadiouth suka fito kan tituna don kallon naɗin Sacuur na 25.
Moroko
Bayanan hoto, Wani mutum na nuna bajintarsa kan doki yayin gasar cin kofin Hassan na biyu a Morocco ranar Juma'a.
Eriteria.
Bayanan hoto, A ranar Juma'a yayin da ɗan wasan tseren kekuna ɗan ƙasar Eritrea ya ɗaga wa magoya bayansa hannu kafin a fara tseren Boucles de la Mayenne.
Mai kamun kifi
Bayanan hoto, Mai kamun kifi na gwada sa'arsa a gaɓar tekun Atlantika da ke Casablanca a Moroco.