Mene ne Ruwan Zamzam kuma daga ina ya samo asali?

Asalin hoton, Getty Images
A ƴan kwanakin nan kusan za a iya cewa ƴan soshiyal midiya da dama daga arewacin Najeriya suna birnin Makka ko Madina a ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umra.
Da dama daga cikinsu kamar yadda suka saba nishaɗantar da masu bibiyarsu a dandalin, haka ma a Makka ko Madina suka rinƙa yin bidiyoyi da hotuna na barkwanci, inda ɗaya daga cikin zolayar mutane da suke yi ita ce "jiki duk Zamzam", abin da ya sa jama'a da dama ke yin tambayoyi kan Zamzam ɗin.
Wannan ya sa BBC yin nazari dangane da wannan ruwa mai albarka da kuma irin muhimmancin da yake da shi ga ɗan'adam.
A ina Zamzam yake?

Asalin hoton, Getty Images
Rijiyar Zamzam na cikin masallacin Harami da ke birnin Makka na ƙasar Saudiyya.
Masallacin Harami shi ne wanda ya fi kowane masallaci girma a duniya, kuma a cikinsa ne Ka'aba yake.
Ana kai ruwan Zamzam mai yawa sosai kullum zuwa birnin Madina domin tabbatar da samar da shi a koda yaushe a masallacin annabi Muhammad.
Miliyoyin al'umma ne suka ɗauki ruwan Zamzam a matsayin ruwa mai tsarki wanda suka yi amannar yana warkar da cutuka.
Ziyartar masallacin wani ɓangare ne na aikin Hajji da Musulmai ke yi, kuma yawanci suna ɗiɓar ruwan domin tafiya da shi gida domin rabawa ga ƴan'uwa da abokan arziƙi.
An yi amannar cewa ruwan Zamzam na da wata baiwa ta musamman kasancewar rijiyarsa ba ta ƙafewa.
Miliyoyin mutane ne duk shekara ke zuwa aikin Hajji da Umra daga dukkan sassan duniya.
Shan ruwan Zamzam ba wajibi ba ne amma sunna ce, wato koyarwa ce ta annabi Muhammad, kuma yawanci mahajjata na shan ruwan Zamzam bayan kammala ɗawafi da kuma bayan kammala sa'ayi.
Haka kuma mahajjata na shan ruwa a duk lokacin da suke buƙata kasancewar an samar da ruwan a kowane wuri a masallacin Makka da na Madina har ma da a otal-otal na biranen domin shan masu Hajji ko Umra.
Me ya sa Zamzam ke da muhimmanci ga Musulmai?

Asalin hoton, Getty Images
Ruwan Zamzam na da mahimmanci saboda tarihinsa a addinance.
A mahanga ta addinin Musulunci, Allah ya samar da rijiyar Zamzam dubun-dubatar shekarun da suka gabata, a lokacin da Allah ya amsa addu'ar matar Annabi Ibrahim - Hajara a lokacin da ya bar ta a cikin rairayin hamada, ita da ɗanta ba tare da abinci ko ruwa ba.
Bayanin hakan ya zo ne a cikin Al-Qur'ani, cikin surah Ibrahim an kuma yi ƙarin bayani kan hakan a cikin litattafan addini da dama.
A cikin hadisin Sahih al-Bukhari, an yi bayanin cewa Hajara ta shiga yanayin da ta riƙa yawon neman ruwa, inda ta riƙa hawa da sauka kan wasu duwatsu biyu wato Safa da Marwa har zuwa lokacin da mala'ika Jibril ya daki ƙasa da duga-duginsa, inda ruwa ya fara ɓulɓulowa.
Fargabar kada ruwan ya ƙare ya sanya Hajara ta riƙa cewa 'zam-zam' da Larabci, hakan yana nufin ruwan ya daina fitowa ya tsaya kada ya ƙare, kuma a nan ne aka samo sunan Zamzam.
Shin Zamzam na samar da waraka?

Asalin hoton, Getty Images
Ko ana samun jabun ruwan Zamzam?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana bai wa mahajjata ruwan Zamzam idan suka kammala ziyarar Makka.
Ana kuma ba masu ziyarar ƙwarin gwiwar tafiya da Zamzam zuwa gida, sai dai hukumomin Saudiyya sun haramta tafiya da shi domin sayarwa.
Duk da wannan mataki da hukumomin ke ɗauka, an samu rahoton sayar da Zamzam ba bisa ƙa'ida ba a Birtaniya.
A watan Mayu, 2011, wani bincike na BBC ya gano yadda aka riƙa sayar da ruwan da ba na Zamzam ba a cikin robobi inda aka maƙala masu sunan Zamzam, lamarin da ya sanya Saudiyya ta ƙara tsaurara matakan tabbatar da samar da Zamzam na asali.
Cibiyar Nazarin Yanayin ƙasa ta ƙasar Saudiyya wadda ke kula da ingancin ruwan rijiyar Zamzam, ta ce ana fitar da shi daga rijiyar ta cikin bututun ƙarƙashin ƙasa domin rabawa a wuraren da ake kai wa, inda ake fitar da dubun dubatar litoci na ruwan.
A 2017, Hukumar kula da ingancin abinci ta Saudiyya ta ce ta lalata dubban kwalaben ruwan zamzam na jabu sannan kuma ta rufe wasu gidajen da ake yin ruwan a wani samame da ta kai a fadin kasar.































