Mahaifin da ya tsinci labarin mutuwar ƴarsa a Facebook

    • Marubuci, Nomsa Maseko, Eleanor Smallwood and Thuthuka Zondi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Ekurhuleni
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 8

Tuku Nkosiyaphantsi ya gano cewa an kashe 'yarsa ne ta hanyar wani saƙo da aka wallafa a Facebook.

Lamarin ya faru ne a watan Agusta. Ya daɗe bai samu damar tuntuɓar Okuhle mai shekaru 27 ba na tsawon wasu kwanaki, duk da cewa ba sabon abu ba ne a gare shi idan sun ɗan jima ba tare da sun yi magana ba.

Sai dai a wata Asabar, wasu maƙwabta biyu suka kira Tuku suka shaida masa cewa sun ga a Facebook an wallafa cewa ƴansanda na neman Okuhle bayan an ba da rahoton ɓatanta. Sun kuma ga hoton wata mata da ta yi kama da Okuhle tana cikin mummunan hali bayan an ji mata raunuka.

"Da na kalli hoton, na fahimci cewa mutumin da ke cikin hoton ya riga ya mutu. Da na sake dubawa sosai, sai na gane cewa Okuhle ce," in ji Tuku mai shekaru 50.

Bayan ganin hoton, Tuku ya kira wani jami'in ɗansanda da ya sani. Jami'in ya tabbatar masa da cewa matar da ke cikin hoton an kashe ta ne, sannan aka jefar da gawarta a kusa da wani kogi a garin Kokstad, cibiyar noma da ke lardin KwaZulu-Natal a gabashin Afirka ta Kudu.

Lokacin da ya ga gawar, ya lura cewa an yi mata mummunan rauni, kuma fuskarta ta lalace ƙwarai sakamakon duka da aka yi mata.

Okuhle ta bar yara biyu masu shekaru tara da uku, kuma tana karatun injiniyan gine-gine.

Tana ɗaya daga cikin mata 581 da aka kashe a Afirka ta Kudu tsakanin watan Yuli da Satumba, a cewar Hukumar Ƴan Sandan Afirka ta Kudu.

Gaba ɗaya, an samu kashe-kashe 5,590 a wannan lokaci, adadin da ya ragu da mutum 204 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar da ta gabata.

Sai dai ba a san ko adadin matan da aka kashe ya ƙaru ko ya ragu ba idan aka kwatanta da shekarun baya ba, saboda ƴansanda sun daina fitar da alƙaluman kisan kan jinsi tsawon wani lokaci, kuma yanzu ne suka sake fara wallafa irin waɗannan bayanai.

Afirka ta Kudu na daga cikin ƙasashen da ke da mafi girman yawan cin zarafin mata da kisan mata saboda jinsi a duniya, wato kashe mace ko yarinya da gangan saboda jinsinta.

Shugaba Cyril Ramaphosa ya yi alƙawarin gudanar da binciken tsaro a kowace ƙaramar hukuma domin gano wuraren da ke da haɗari ga mata da kuma magance matsalolin, tare da ƙara yawan jami'an tsaro a yankunan da suka fi fuskantar irin wannan barazana.

Ga Tuku, hakan na nufin gudanar da nasa binciken kan kisan ƴarsa.

Watanni da dama bayan an kashe Okuhle, ya ce har yanzu ba a kama kowa ba.

Tuku ya yi imanin cewa ƴansanda sun gaza duba hotunan kyamarorin sa ido (CCTV) na wani ginin gwamnati na yankin, waɗanda watakila za su iya nuna waɗanda Okuhle ta kasance tare da su a ranar da ta ɓace. Ya ce ana goge irin waɗannan bayanan bidiyo duk bayan kwanaki bakwai.

BBC ta nemi jin ta bakin Hukumar Ƴansandan Afirka ta Kudu kan zargin, amma har zuwa lokacin wallafa rahoton ba a samu amsa ba.

A cewar wani rahoto na shekarar 2024 da Majalisar Binciken Kiwon Lafiya ta Afirka ta Kudu ta fitar, adadin shari'o'in kisan mata da ba a warware ba na ci gaba da ƙaruwa.

A wannan shekarar, Amnesty International ta bayyana cewa Hukumar Ƴansandan Afirka ta Kudu tana fama da ƙarancin kayan aiki, rashin wadatattun kayan aiki da horo, lamarin da ke hana ta mayar da martani yadda ya kamata da kuma da tausayi a lokutan da ake binciken laifukan cin zarafin mata da na jinsi.

Tuku ya ce yanzu yana ƙoƙarin nemo hotunan kyamarorin sa ido (CCTV) tare da bibiyar mutanen da suka san ƴarsa, domin samun wasu bayanan da za su taimaka wajen gano waɗanda suka aikata laifin.

Lokacin da BBC ta tambaye shi a farkon wannan watan game da irin ci gaban da Afirka ta Kudu ta samu wajen kare lafiyar mata, Ramaphosa ya ce gwamnati za ta ware ƙarin kuɗi a kasafin kuɗin watan Fabrairu domin yaƙi da cin zarafin mata da na jinsi.

Da yake magana bayan kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomi, Ramaphosa ya ƙara da cewa gwamnati ta ƙara yawan jami'an ƴansanda a cikin shekaru uku da suka wuce.

Ba Okuhle ce kaɗai aka kashe a irin wannan hanya a Kokstad a wannan shekarar.

Tsakanin watan Janairu da Oktoba na wannan shekara, an gano gawarwakin mata biyar da ƙananan yara uku a garin. Duk da haka, an kama waɗanda ake zargi ne kawai a shari'o'i biyu daga cikin waɗannan laifukan.

Sakamakon wannan yanayi, al'ummar yankin sun kafa ƙungiyoyin sintiri a unguwanni tare da ƙayyade lokutan da mata da yara za su koma gida a lokacin hunturu.

Tun daga watan Yuni, ana jan hankalin yara su kasance a gidajensu kafin faɗuwar rana, yayin da ake shawartar mata su koma gida kafin ƙarfe tara na dare.

Kamvalethu Cetywayo mai shekaru 34, wanda ke cikin ƙungiyar kare al'umma, shi ne ke jagorantar wasu maza kusan 15 da ke gudanar da sintiri a wuraren da ake fama da yawan laifuka da daddare. Wannan ya haɗa da wuraren da aka taɓa gano gawarwaki ko kuma inda aka samu rahotannin aikata laifuka.

Da aka tambaye shi yadda yake ji game da taƙaita ƴancin mata da yara ta hanyar waɗannan ƙa'idoji, Kamvalethu ya ce manufar matakin ita ce tabbatar da tsaronsu, kuma ba dole ba ne kowa ya bi shi. Ya ƙara da cewa mataki ne na wucin gadi har sai ƴansanda sun kama masu aikata kisan.

An yi garkuwa da Kgothatso Mojela ne a shekarar 2018 yayin da take kan hanyarta ta zuwa wurin aiki a garin Kempton Park, wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Ekurhuleni.

Tana cikin motar tasi lokacin da direban ya kulle ƙofofin motar sannan ya fara tafiya zuwa wata hanya da ba daidai ba.

Kgothatso ta ce lokacin da ta faɗa wa direban cewa ya kauce hanya, sai ya fara dukan ta da naushi da mari.

Ta ce daga bisani ta tilasta buɗe ƙofar gefen fasinja sannan ta yi tsalle daga motar da ke cikin gudu. Wannan ya jawo mata mummunan rauni a gwiwa tare da lalacewar jijiyoyin idanunta. Wasu jami'an tsaro biyu da suke kusa ne suka taimaka mata.

Kgothatso ta ce daga baya an daure wanda ya kai mata harin bisa wasu laifukan aikata manyan laifuka, ciki har da abin da ya aikata mata. Amma an sake shi a bara. Yanzu kuma, ta ce tana tsoron kada ya sake yi mata illa.

Bayan harin da ta fuskanta, Kgothatso ta sauya wasu abubuwa a rayuwarta domin kare kanta. Daga cikin matakan da ta ɗauka akwai sayen bindigar kwaikwayo domin tsoratar da masu yi mata barazana.

Har ila yau, ta daina yin gudun motsa jiki ita kaɗai, kuma tana tabbatar da cewa tana tare da wani idan za ta gana da kwastoman da ba ta taɓa haɗuwa da shi ba a aikinta.

A watan Satumba, ƴansanda sun shawarci mata a yankin Kempton Park da su guji tafiya ko yin gudun motsa jiki su kaɗai, "musamman a wuraren da ba a cika samun jama'a ba", bayan kashe Elizabeth Moselakgomo, wata uwa mai shekaru 38.

Elizabeth ta ɓace ne a ranar 9 ga Satumba lokacin da ta fita gudun motsa jiki. An gano gawarta bayan kwana uku a kusa da wata babbar hanya mai yawan zirga-zirga a Kempton Park. Gawar na ɗauke da munanan raunuka, kuma an cire wani ɓangare na tufafinta.

Kisan ya girgiza al'ummar masu gudun motsa jiki a Afirka ta Kudu, ciki har da ƴanuwan mata Zonke da Zama Mthethwa. Shekaru tara da suka gabata sun kafa The Pack, wata ƙungiyar mata masu gudun motsa jiki a Johannesburg. Elizabeth ma tana halartar wasu daga cikin shirye-shiryen ƙungiyar.

Bayan wannan lamari, Kgothatso ta bar Kempton Park, kuma yanzu tana zaune kusa da iyayenta a wani yanki na daban na ƙasar.

Mahaifiyarta, wadda fitacciyar mai fafutukar al'umma ce, kwanan nan ta shirya wani tattakin addu'a domin tunawa da matan da aka kashe.