Mutum 30 sun mutu a gobarar tankar mai a Masar
Ma'aikatar lafiya ta Masar ta ce aƙalla mutum 30 ne suka mutu bayan wata motar dakon mai ta kife a wata babbar hanya da ke da cunkoso a birnin Alƙahira, sannan ta kama da wuta.
Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wuta da bakin hayaki na tashi a unguwar Al-Waraq da ke yankin Giza.
An kuma ga ƙananan motocin haya da babura da gobarar ta ƙone ƙurmus.
Ganau sun ce wasu daga cikin mutanen da suka mutu sun maƙale ne a cikin motocinsu, inda ba su samu damar fita ba kafin gobarar ta kama.
Kimanin mutum 20 aka kwantar a asibiti sakamakon ƙone wa da kuma shakar hayaƙi.
Ma'aikatar lafiya ta Masar ɗin ta ce an tura motocin ɗaukar marasa lafiya 39 zuwa wurin da lamarin ya faru a yankin Giza, wanda kuma shi ne yankin da dalar Masar suke.