Robertson na daf da zama na biyu da zai yi wa Scotland wasa 100, Scotland
Andy Robertson na dab da zama mutum na biyu da zai buga wasa 100 a tawagar Scotland a karon farko cikin fiye da shekaru 150 a tarihin ƙwallon ƙafar ƙasa da ƙasa.
Kyaftin ɗin tawagar ƙasar zai kai wannan adadi na wasanni 100 a karawar Nations League a ranar Asabar da za ta fafata da Arewacin Macedonia, yayin da yake ƙara matsowa kusa da karya tarihin wanda ya fi kowa yawan wasanni a Scotland.
Tun bayan da Gordon Strachan ya ba shi damar fara buga wa Scotland wasa a shekarar 2014, lokacin da yake matashin ɗan wasa mai tsaron baya daga hagu a Dundee United, Robertson ya kasance muhimmin ɗan wasa a tawagar ƙasar, inda ya haskaka a wasannin ƙwallon ƙafar Scotland.
Babban ɗan wasan Scotland, Kenny Dalglish, shi ne mutum ɗaya tilo da ya taɓa saka rigar tawagar Scotland da buga wasa sama da 100 fiye da Robertson.
‘King Kenny’ har yanzu shi ne ke kan gaba da wasa102, amma abokinsa na iya zarce shi a watan Nuwamba idan ɗan wasan mai shekara 32 ya buga dukkan sauran wasannin Nations League da Scotland za ta yi a bana.
Ya dace cewa Robertson ne zai karya wannan dogon tarihi, ganin yadda shi da Dalglish suka kulla abota a lokacin da Robertson yake taka leda a Liverpool.
Sai dai Dalglish ba ya son hakan, domin yana son ake ta tunawa da shi a kan wannan kwazon, yadda sunansa ba zai bace ba.
To sai dai kuma Dalglish zai samun kwanciyar hankali da cewa tarihin ƙwallayen da ya ci, wanda suka kai 30 da yin kafada da Denis Law, yana da nisa sosai ga na Robertson.
Sai dai daga cikin ƴan wasan da suke ci gaba da buga tamaula a yanzu, John McGinn yana da tazarar wasanni takwas tsakaninsa da Robertson a jerin waɗanda suka fi yawan wasanni a tarihin Scotland. Hakan na nufin ƴan wasan Scotland da za su buga wasa 100 jimilla za su kai uku nan ba da dadewa ba.