Me ke haifar da tsananin ciwon ciki lokacin haila kuma ya hana haihuwa?

    • Marubuci, Vicki Loader
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reportera de Salud, BBC News
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Tun tana da shekara 13, a duk lokacin da al'adarta ke gabatowa, Grace kan sha fama da matsanancin ciwon mara har sai an kai ta asibiti.

Sau da yawa iyayenta kan ɗauke ta a hannu su saka ta cikin mota saboda tsananin radadin da take ji.

Yanzu Grace na da shekara 14 kuma tana zaune a Yorkshire, kimanin kilomita 270 arewacin London.

Ta shafe lokaci mai tsawo tana fama da ciwon da likitoci ba su ɗauka da muhimmanci ba.

"Na ji kamar suna kallona a matsayin yarinyar da ba ta son zuwa makaranta, kuma tana ƙara gishiri a kan abin da take ji," in ji ta.

A wasu lokuta takan jira sa'o'i da dama a sashen gaggawa kafin a duba ta, amma daga ƙarshe a sallame ta zuwa gida tana kuka tare da ƙarin magungunan rage zafi.

Likitoci sun ba da dalilai daban-daban kan abin da ke haddasa mata alamomin da taka ji ciki har da matsalar hanji mai sa ciwo (IBS), ƙari (cyst), damuwa (anxiety), ko kuma cewa "al'ada ce mai tsanani kawai."

"Amma ni na san cewa akwai wani abu fiye da haka," in ji ta.

A cewar Grace, likitoci sun sha gaya mata cewa ba zai yiwu tana fama da cutar endometriosis ba, wata cuta da ba ta da magani wadda ke haifar da raunuka da tabo a gabobin jiki, saboda suna ganin tana da ƙarancin shekaru.

Ta kuma ce an yi watsi da buƙatunta na a yi mata ƙarin gwaje-gwaje domin gano ainihin abin da ke damunta.

Mece ce cutar endometriosis

Cutar endometriosis cuta da ke faruwa lokacin da wani nama mai kama da na cikin mahaifa ya fara girma a wajen mahaifa.

Wannan kan haddasa matsanancin ciwon mara, zubar jinin al'ada mai yawa, gajiya da kuma wasu matsalolin lafiya kuma ba ta da ba ta da magani.

"Ji nake kamar an naɗe cikina da ƙayoyi"

Grace ta ce ciwon marar haila da take fama da shi tun tana shekara 13 yana da tsanani matuƙa, har ta kan ji kamar an naɗe cikinta da ƙayoyi ne kuma kamar ana yaga gabobinta daga ciki, in ji ta.

A wasu lokuta ciwon kan tilasta mata kwanciya a gado na tsawon lokaci. Idan magungunan rage zafin da take da su sun ƙare, akan kai ta asibiti inda ake ba ta maganin morphine domin rage mata radadi.

Haka kuma an taɓa ba ta magunguna irin su co-codamol da tramadol.

Sai dai Grace ta ce tana fargabar kada ta saba da amfani da irin waɗannan magunguna masu ƙarfi.

"Abin tsoro ne, saboda ba na son rayuwata ta dogara da waɗannan magungunan har abada," in ji ta.

Abin da ya fi damun Grace shi ne yadda likitoci ke ƙin yarda cewa matasa mata masu yin al'ada na iya kamuwa da cutar endometriosis.

"Ko ƙwararren likita bai saurare ni ba. Idan shi ma ba zai yarda da ni ba, wa zai yarda?" in ji ta.

Sai bayan da iyalinta suka nemi wani likita daban ne aka tabbatar tana fama da cutar endometriosis, wadda kan haifar da matsanancin ciwon mara, yawan jinin al'ada da gajiya.

A cewar bayanan NHS na Birtaniya, cutar endometriosis tana shafar kusan kashi 10 cikin 100 na mata.

Shahararriyar mai gabatar da shirye-shiryen BBC, Emma Barnett, ta bayyana cewa sai da aka yi mata tiyatar cire mahaifa saboda cutar, duk da cewa ba abin da take so ba ne.

Ƙungiyar Endometriosis UK ta ce cutar na iya kama mace a duk lokacin da ta fara al'ada, kuma kuskure ne a yi tunanin cewa manyan mata kaɗai ke kamuwa da ita.

Jami'ar kungiyar, Faye Farthing, ta ce ya zama dole gwamnati, NHS da ma'aikatan lafiya su inganta ilimantar da matasa game da lafiyar al'ada domin kare makomarsu.

Ƙungiyar ta kuma ce gano cutar kan ɗauki tsawon lokaci.

A matakin farko, musamman ga matasa, sau da yawa ba a iya gano ta ta hanyar gwajin ultrasound.

Sai dai ana ci gaba da samar da sabbin gwaje-gwaje da ake fatan za su taimaka wajen gano cutar da wuri.

Cutar na iya shafar haihuwa

Grace ta ce likitoci sun gargaɗe ta cewa cutar endometriosis na iya shafar ikon haihuwarta. Sun ce akwai yiyuwar ba za ta iya haihuwa bayan shekara 30 ba saboda lalacewar da cutar ta jawo a gaɓoɓin haihuwa.

"An gaya min cewa ina da kusan shekara 15 kacal da zan iya haihuwa, in ba haka ba wataƙila ba zan iya ba," in ji ta.

Likitar mata da yara, Dr Gail Busby, ta ce duk da cewa yawancin 'yan mata kan fuskanci ciwon haila, amma idan ciwon yana hana su zuwa makaranta, motsa jiki ko mu'amala da abokai, ba abu ne na al'ada ba.

Ta ce illar cutar ba ta ta'allaka ga jiki kawai ba, domin tana iya jefa matasa cikin damuwa ko baƙin ciki, tare da hana su more rayuwar ƙuruciyarsu kamar takwarorinsu.

Mahaifiyar Grace, Samantha, ta ce duk da kasancewar akwai tarihin cutar endometriosis a cikin iyalinsu, hakan bai sa gano cutar cikin sauƙi ba.

Ta ce, "Idan ka ga 'yarka tana birgima a ƙasa saboda ciwon mara na haila, ka san cewa ba laille haila bace ta haddasa ta."

Kwanan nan Grace ta yi tiyatar laparoscopy domin cire gurɓataccen naman da cutar ta haifar.

Ana kuma ba ta shawarar amfani da maganin hana ɗaukar ciki mai sinadarin hormone don rage ciwon.

Ta ce tana fatan labarinta zai ƙarfafa sauran matasa su nemi a bincika lafiyarsu idan suna fama da irin wannan matsala.