Arsenal da PSG na harin Nusa, Barnett zai tsawaita zamansa a Tottenham

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal ta tattauna da wakilan Antonio Nusa yayin da RB Leipzig ke neman euro miliyan 80 (fam miliyan 67 ) kan ɗan wasan. (Teamtalk)

Sai dai kuma Paris St-Germain, da ke da Desire Doue, da Khvicha Kvaratskhelia da ke jiya ta tsawon lokacin sakamakon rauni da suke fam da shi suma na son siyo Nusa ɗin su ma. (AS - in Spanish)

Liverpool, da PSG, da Real Madrid, da Barcelona na son ɗan wasan Manchester City Erling Haaland, idan City din ta shirya siyar da shi a kaka mai zuwa. (Fichajes - in Spanish)

Ɗan wasan Tottenham Luca Williams-Barnett, 18, na db da sake rattaba hannu kan sabon kwantaragi da ƙungiyar tasa, wanda hakan zai haiar da cikas ga Chelsea da Borussia Dortmund da ke harin ɗan wasan. (Telegraph - subscription required)

Manchester United na son ɗauko sabin ƴan wasan gaba a Janairu mai zuwa wato yayin kakar siyen ƴan wasan, inda sabon kociyan kungiyar Mauricio Pochettino ke son ganin ya samo madadin wasu daga cikin ƴa wasan irinsu Benjamin Sesko, da ke fama da rauni. (Times)

Mai horar da ƴan wasan Chelsea Xabi Alonso na ci gaba da smaun goyan bayan jagororin ƙungiyar, duk da halin da ƙungiyar ke ciki. (Telegraph - subscription required)

Liverpool ta sake shiga wani sabon kwantaragi na tsawaita zaman mai tasaron ragar ta Alisson, da ke son kwantaragin zamansa ya kai har 2029. (Nicolo Schira)

Brighton da Liverpool na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Borussia Monchengladbach Wael Mohya. (Teamtalk)

Sabon mai horar da ƴan wasan Crystal Palace Thomas Frankna dab da yanke hukuci ko zai tsawaita zaman Wilfried Zaha, da kwantaraginsa ya ƙare kuma ya ke a tisaye da Eagles. (Football Insider)

Adrien Rabiot,na dab da shiga wata sabuwar kwantaragi da AC Milan, inda ake sa ran zai zauna a ƙungiyar har zuwa 2030. (Calciomercato - in Italian)