Me shirin gwamnati na rage farashin man fetur ya ƙunsa?

Fetur
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da miliyoyin ƴan Najeriya ke kokawa da tsadar rayuwa, gwamnatin tarayya ta sanar da wani sabon mataki na rage wa jama'a raɗaɗin hauhawar farashin fetur.

Matakin, wanda zai yi aiki na tsawon kwana 30, zai bai wa masu sayen fetur a gidajen man mallakin NNPCL damar samun fetur a farashin mai rahusa domin, wanda gwamnatin ta ce ta yi domin rage yanayin da tashin farashin man ya jefa ƴan ƙasar.

Sai dai sanarwar ta haifar da muhawara mai zafi a tsakanin ƴan ƙasar, inda gwamnati ke jaddada cewa ba tallafin mai ba ne ta dawo da shi, wasu na ganin sabon tsarin bai da wani babban bambanci da tallafin da aka soke a watan Mayun shekarar 2023.

A wani ɓangaren kuma, wasu na ganin kawai za a lasa wa mutane zuma ne a baki, sannan a koma gidan jiya, a daidai lokacin da wasu ke tunanin ba dole ba ne a ci moriyar lamarin domin za a riƙa samun dogon layi.

Yadda za a aiwatar da tsarin

A cewar ministan kuɗin Najeriya, Taiwo Oyedele, NNPCL ta amince ta haƙura da ribar da take samu daga dillancin fetur na tsawon kwana 30.

A aikace, idan NNPCL ta sayi ko ta shigo da fetur kan N1,300 a lita, za ta sayar wa masu amfani da shi a wannan farashin ko kusa da shi ba tare da ɗora ribar da take sakawa a baya ba.

An bayyana cewa masu motocin haya da sauran masu safarar jama'a za su zama cikin waɗanda za su fara amfana da tsarin, domin gwamnati na fatan hakan zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma rage matsin tattalin arziki ga iyalai masu karamin karfi.

A takardar bayanin da ma'aikatar kuɗi ta fitar, ta yi bayanin cewa rangwamen da NNPCL ke bayarwa ya bambanta da tallafin mai.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewarta, tallafi yana faruwa ne idan gwamnati ta biya wani ɓangare na kuɗin fetur da ya kamata mai saye ya biya, kuma kuɗin yana fitowa ne daga asusun gwamnati.

Amma a wannan karon, gwamnati ta ce NNPCL ce kawai ta rage nata ribar kasuwanci. Wato kamar yadda wani babban kantin sayar da kaya zai iya rage ribarsa domin janyo ƙarin kwastomomi, haka NNPCL ta yi.

Bayanin gwamnati ya nuna cewa NNPCL tana sayen fetur daga Matatar Dangote da wasu matatun a farashin kasuwa.

Daga nan sai ta ƙara nata ribar dillanci kafin ta sayar wa masu amfani.

Amma a sabon tsarin, ana nufin wannan ribar ta dillanci ce za a rage ko ma a cire gaba ɗaya na wani lokaci. Hakan zai sa farashin da mai saye zai gani a famfo ya ragu ba tare da gwamnati ta kashe kuɗaɗe ba.

Ya bayyana cewa idan kuɗin shigo da ko samar da litar fetur ya kai N1,300, NNPCL zai sayar da ita kan wannan farashin ba tare da ƙara wani riba a kansa ba. Wannan, a cewarsa, wata dabara ce ta rage wa jama'a wahala ba tare da mayar da ƙasar tsarin tallafin mai da ya janyo kashe maƙudan kuɗaɗe daga baitul malin gwamnati ba.

Tsarin naira 1,350 a lita

Baya ga rangwamen da za a bayar a gidajen man NNPCL, gwamnatin tarayya ta bayyana wani shirin da ta ce zai taimaka wajen tabbatar da daidaiton farashin fetur.

A ƙarƙashin wannan tsari, gwamnati tana tattaunawa da masu tace mai da masu shigo da fetur domin a kayyaɗe kuɗin fetur daga matata ko wajen sauke shi zuwa naira 1,350 kan kowace lita.

A cewar Oyedele, idan kuɗin samar da fetur ya haura wannan adadi saboda tashin farashin ɗanyen mai ko canjin kuɗin waje, masu tace mai da masu shigo da shi ne za su ɗauki nauyin giɓin tare da ƙwato abin da suka rasa idan farashin ya sauka a nan gaba.

Ya ce manufar ita ce hana yawan sauye-sauyen farashin da ke jefa masu amfani da kayayyaki da ƴan kasuwa cikin rashin tabbas.

"Ganin litar fetur tana tashi zuwa N1,500 yau sannan ta koma N1,300 gobe yana haifar da rashin daidaito a tattalin arziki. Mafi alheri a samu tsayayyen farashi da mutane za su iya tsarawa kansu rayuwa da kasuwanci."

Shin tallafin mai ne aka mayar?

Ɗaya daga cikin muhawarar da ta fi ɗaukar hankali ita ce ko sabon tsarin yana da kama da tallafin mai ko kuma a'a.

Gwamnati ta nanata cewa ba tallafi ba ne saboda babu kuɗin da za a fitar daga asusun gwamnati domin rage farashin fetur. Amma wasu masana tattalin arziki na ganin cewa idan an hana kamfani samun ribar da ya kamata ya samu domin a rage farashi ga masu amfani, hakan na iya zama wani nau'i na tallafi a kaikaice.

Wasu kuma suna tambayar ko masu tace mai da masu shigo da fetur za su iya ci gaba da ɗaukar asara idan farashin ɗanyen mai ya ci gaba da hawa a kasuwannin duniya.

Sai dai gwamnatin ta ce wannan wani mataki ne na tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi da kuma rage nauyin da hauhawar farashin mai ta haddasa.

Gwamnati ta ce za su fi mayar da hankali ga masu motocin haya, motocin bas da sauran masu safarar jama'a domin tabbatar da cewa rangwamen ya kai kai tsaye ga mutanen da suka fi bukata.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a tantance waɗanda za su fi cin gajiyar tsarin ko kuma yadda za a hana yiwuwar amfani da shi ba bisa ƙa'ida ba.

Wata muhimmiyar tambaya da jama'a ke yi ita ce ko rangwamen fetur zai kai ga rage kudin sufuri.

Duk da cewa direbobi za su iya samun fetur a rahusa a wasu gidajen mai na NNPCL, har yanzu babu tabbacin cewa za su rage kuɗin mota ga fasinjoji, kasancewar zai ta'allaƙa ne da samun man.

Mafitar siyasa suke nema - Atiku

A daidai lokacin da ake tafka muhawara kan sabon shirin, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa Atiku Abubakar, ya yi watsi da shirin gaba ɗaya, yana mai cewa ba mafita ce mai ɗorewa ba ga matsalolin tattalin arzikin ƙasar.

A wata sanarwa da daraktan sadarwar yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, Atiku ya bayyana rangwamen a matsayin wata dabara ta siyasa da aka tsara domin samun karɓuwa a wajen masu zaɓe yayin da zaɓen 2027 ke ƙara karatowa.

A cewarsa, idan har matsalar tsadar fetur ta kasance babbar matsala ga jama'a, bai kamata gwamnati ta gabatar da mafita ta wucin gadi ba.

Ya ƙara da cewa ƴan Najeriya na buƙatar sauƙi mai ɗorewa, ba wani rangwame da zai ƙare bayan wata guda ba.

Batun fetur ya daɗe yana cikin batutuwan da suka fi tayar da hankali a Najeriya. Duk gwamnati da ta yi yunƙurin sauya tsarin farashin mai kan fuskanci muhawara daga ɓangarori daban-daban.