Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda auren wuri, talauci, da rashin tsaro ke hana miliyoyin yara zuwa makaranta a arewacin Najeriya
- Marubuci, Madina Maishanu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Africa
- Aiko rahoto daga, Goronyo, Nigeria
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A duk lokacin da Hadiza mai shekaru 13 ke dakan gero a turmi, takan rera waƙoƙin harufan Ingilishi na A B C D har zuwa ƙarshe. Inda hakan ke nuna irin shauƙin da ta ke da shi na son karatu da kewar zuwa makaranta da ta ke yi a kullum.
"Wasu lokutan nakan yi rubutu a ƙasa, don in rinka tunawa da kuma ƙara ƙwarewa wajen rubuta haruffan," a cewar ta.
Wata rana, shekaru biyu da suka gabata, gungun wasu ƴan bindiga suka kai hari ƙauyensu: "sun kora shanun mu, sun kuma yi garkuwa da wata yarinya, hakan ya sa muka gudu, sai da muka yi tafiya mai nisa babu takalmi sannan muka iya zuwa nan".
Tun bayan nan, take zaune a wani sansanin ƴan gudun hijira da ke Goronyo, kilomita kaɗan daga cibiyarta. Cikin taƙaitaccen lokaci ta fara zuwa makaranta a nan, sai dai ba a jima ba, ta haɗu da wani matashi, inda ta bar zuwa makaranta ta aure shi, ta na da shekaru 13.
"Al'ada ce da aka jima da ita na cewar idan aka aurar da yarinya, karatun ta ya ƙare," a cewarta. Yanzu dai ta na zaune da surukanta, inda take taimakawa wajen kula da gida. Duk da cewar dokokin Najeriya sun hana auren wuri, sai yarinya ta kai shekaru 18, sai dai, ba a kiyaye wannan doka.
Hadiza ɗaya ce daga cikin yara miliyan 19 da basa zuwa makaranta, a cewar wata ƙididiga ta asusun tallafa yara na majalisar ɗinkin duniya wato UNESCO na 2024, inda ya ce ɗaya cikin yara huɗu na ƙananan yara ba sa zuwa makaranta a Najeriya.
Kan wannan matsala ne dai ya sa BBC ta ke ƙaddamar da shirin koyar da yara karatu da harshen hausa, wanda shi ne harshen da aka fi amfani da shi a yankin arewacin Najeriya, da maƙotan ƙasashe irinsu Niger, da Kamaru da Chadi da wasu ƙasashen da ke yankin Yammacin Afrika.
Za ta ringa koyar da darasin Lissafi, da Turanci, da na harkokin fasaha ga yaran da ke yankin Yammacin Afrika, ta kafafen sada zumunta na BBC hausa, da kafafen yada labarai na talabijin da rediyo wato abokan huldar BBC. Mutane da dama a yankin za su ringa samun labarai daga rediyo, kasancewar fiye da rabin iyalai a Najeriya na da ita, a cewar ƙungiyar tallafawa yara ta Save the Children.
Dars na nufin "Darasi" a harshen Pashto da Dari, kuma an fara gabatar da shirin da waɗan nan harsuna a shekarar 2023 a shashen yara na Afganistan da aka hana zuwa Makaranta. Sai na harshen larabci da aka ƙaddamar a watan Fabarerun 2025.
Dalilan da suka sa yara masu yawa basa zuwa makaranta a Najeriya, sun da dama da sarƙaƙiya sossai. Yanzu kamar halin da Hadiza ke ciki, akwai wata yarinya mai sunan Ruqayya mai shekaru 12 da ita ma ke zaune a sansanin ƴan hijirar da ke Goronyon jihar ta Sokoto.
"Na kan ji ba daɗi idan na ga yara na karatu, ko suna zuwa makaranta, yayin da ni ba ni da halin zuwa, " a cewar ta.
A matsayi na na babban ɗiya, a kowacce rana Rukayya kan je itace sannan ta siyar da shi ta haɗa da bara/roko don samun abin da za su ci ita da ƙannaunta.
"In da mahaifi na na nan da rai, da ba zamu shiga wannan halin na yi bara ba," ta na bayani, inda ta ce mutane kan zaulaye ta, amma hakan bai taɓa sawa ta ji ta bari ba, domin kuwa ita ce hanya kaɗai da take samun abun da za su ci.
Ƴan bindiga ne dai suka halaka mahaifinta a shekarar da ta gabata a kan idonta, ta ce ita da sauran ƴan uwanta, suka tsere daga gida zuwa sansanin.
Ita da Hadiza na cikin mutane dubu ɗari shida da saba'in (670,000) a yankin Arewa maso yammaci da arewa, maso tsakiyar Najeriya da matsalar tsaro ya tilasta musu barin mahallansu a cewar hukumar kula da masu ƙaura ta duniya wato International Organization for Migration (IOM).
Wasu daga cikin hare-haren da aka kai mayaƙa da ke ikirarin jihadi ne suka kai su, sai kuma wanda masu garkuwa da mutane da ke kai su, da ke sata tare da kisa inda sun kai hari.
Makarantar da Hadiza ke zuwa a Gornonyo, ita ce makaranta ɗaya tilo da yaran da ke sansanin ke zuwa, sannan mutum 50 suke cusawa a kowanne aji.
Ɗaya daga cikin malaman makarantar Kamilu Sulaiman Jakada ya ce, duk da makarantar tasu kayauta ake ɗaukar yara, amma ƙalilan ne ke zuwa saboda yadda wasu iyayen ke kallon zuwa makaranta sai ƴaƴan masu hannu da shuni, saboda haka suka zaɓi tura su nemo kuɗi don samun abun da za su ci.
Ya ce makarantar ba ta da isassun malamai, da ajujuwa, da yadda rashin samun kuɗin tafi da harkokin koyarwa, sai dai ya ce sun fi samun tallafi daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, ko wasu ɗai-ɗai ku maimakon daga gwamnati.
Wani ƙarin ƙalubale da suka fuskanta shi ne matsalar ƴan bindiga. Inda ya cea baya sun taɓa kawo hari makarantar haye a kan babura, inda suka yi ta harbi sama, sai dai babu wanda suka yi wa rauni, amma iyaye da yawa sun tsorata, inda suka cire ƴaƴansu daga makarantar. Hakan shi ne matakin da iyaye ke ɗauka a duk inda aka ce ƴan bindigar sun kai hari makarantun da ƴaƴansu ke karatu suma.
Dukkan wani yaro a Najeriya ya kamata a ce ya na samun ilimi kyauta na tsawo shekaru 9, a tsarin ilimi tilas, wato shekaru shida a Firamare, sai uku a makarantar sakandare. A na raba ɗawainiyar karatun tsakanin gwamantin tarayya, da jiha, da na ƙananan hukumomi.
Sai dai makarantu masu ya wa na fama da matsaloli, kama daga na iyayen marasa ƙarfi da ba za su iya ɗaukar ɗawainiyar makaranta ba, da jigilar siyen kayan makaranta, da littatafai da kudin tafiya makarantar.
Wannan matsala dai ta jima, inda gwamantoci daban-daban na ɗaukar matakan da za su magance matsalar ta rashin zuba kuɗaɗen da suka kamata, da rashin sa ido yadda ya kamata kan dukiyar da ake zubawa a ɓangaren.
Ƙari shi ne, yara masu yawa da ke zuwa makarantun Almajirai, da ake koyar da ilimin adinin musulunci, ba a koyar da su darusan lissafi da Kimiyya, kuma majalisar ɗinkin duniya na yi musu kallon yaran da basa zuwa makaranta.
Ƙaramar ministan harkokin ilimi a Najeirya Farfesa Suwaiba Sa'id ta ce adadin da ake ambatawa na yaran da basa zuwa makaranta bai kai yadda ake zuzutawa ba, sai dai ta amince da yadda ake samun ƙaruwar al'umma a Najeriya, sannan har yanzu ba a ɗauki matakan da suka kamata ba. ............."Ba zan kama suna ba, amma akwai jihohi guda biyu da ba su ɗauki ko da malami ɗaya ba a tsawon shekaru 8 ba".
Ta ce Ilimi shi ne abun da gwamnati ya kamata ta fi "baiwa fifiko" sannan akwai shiri Lumina da zai taimaka wajen magance matsalar da aka yi "watsi da ɓangaren ilimin na tsawon shekaru". Manufar shirin na Lumina shi ne taimakawa ƴaƴa mata miliyan ɗaya samu ilimin boko nan da shekara 2030.
Ta kuma cewa "gwamnati na yin ƙoƙari "wajen ɗakile mastalar ƴan bindiga, saboda "yadda yaran da ya kamata su ringa zuwa makaranta ke shiga laifin garkuwa da mutanen".
Yanzu dai, yara irinsu Hadiza da Rukayya wanna sabon shirin na BBC Hausa Dars zai mayar da hankali wajen taimakawa. Hadiza ta ce har yanzu ta na fatan ganin ta cimma burinta na zama likita "don taimakawa mata ƴan uwanta".
Za a ringa gabatar da shirin na Dars Hausa a sashen Hausa na BBC a dukkan ranakun Lahadi a shirin mu na ƙarfe 06:45 agogon Najeriya da NIjar, inda za a maimaita shi a shirin mu na dare 20:45. Za kuma a ringa dora shi a dukkan kafafen mu sada zumunta na BBC Hausa, da suka haɗa da YouTube, da Facebook, da X sai kuma Instagram.