ASUU reshen jihar Zamfara sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Jihar Zamfara ta fara yajin aiki na sai baba-ta-gani, bayan da gwamnatin jihar ta gaza cika bukatun da kungiyar ta gabatar.
Daga cikin bukatun akwai aiwatar da yarjejeniyar albashi tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU, tare da biyan hakkokin malamai da suka rage a baya.
Kungiyar ta sanar da fara yajin aikin ne bayan taron majalisar ta da aka gudanar ranar Talata a harabar jami’ar ta wucin gadi da ke Talata Mafara.
Mukaddashin shugaban reshen kungiyar, Kwamared Anas Abubakar Dogo, ya ce an dauki wannan mataki ne bayan wa’adin da kungiyar ta bai wa gwamnati ya kare, da kuma bayan yajin aikin gargadi da ta gudanar a baya ba tare da samun wata gamsasshiyar amsa daga gwamnatin jihar ba.
Ya bayyana cewa kungiyar ba za ta iya ci gaba da ba da ayyukan koyarwa yadda ya kamata ba a karkashin halin da ake ciki yanzu.
Dogo ya ce bukatun malaman sun hada da aiwatar da yarjejeniyar albashi ta FG-ASUU ta watan Disamban 2025, biyan bashin karin girma da sauran hakkokin kudi da gwamnatin jihar ke binsu.
Ya kara da cewa reshen kungiyar ya gudanar da tarurruka da dama da majalisar gudanarwar jami’ar, shugabannin jami’ar da sauran masu ruwa da tsaki kafin daukar matakin yajin aikin.
A cewarsa, yunkurin samun ganawa da Kwamishinan Ilimi, Shugaban Ma’aikatan Jiha da kuma Sakataren Gwamnatin Jihar bai haifar da sakamakon da ake bukata ba.