''Za mu karrama mutane a gagarumin taron dambe na Kudawa''

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ƙungiyar damben gargajiya ta Kudawa ta Najeriya za ta karrama mutanen da suka taka rawar gani a fannin haɓɓaka da ci gaban ƴan wasanta.

A taron da ta tsara yi ranar Asabar 25 zuwa 26 ga watan Janairu a gidan wasan Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Najeriya, za ta fara da gudanar da dambe.

Hakan ne ya sa ta gayyaci fitattun ƴan wasan Kudu, domin dambatawa da na Arewa da kuma Guramada da nufin karfafa zumunta a tsakaninsu.

Daga nan za ta yi taro tsakanin mambobinta, domin karrama waɗanda suka bayar da gudunmuwa a ƙungiyar da kuma ƴan dambenta.

Kamar yadda mai magana da yawun ƙungiyar Alhaji Aminu Mai Unguwa ya sanar cewar ''Za mu gudanar da gagarumin taron da ba a taba yinsa ba a fannin dambe.

''Tuni mun tsara hanyoyin da za a gudanar da wasannin dambe da kuma gabatar da taron cikin tsari.''

Alhaji Tanko Daraktan magina shi ne shugaban ƙungiya, an kuma gayyaci mutanen da za a bai wa lambobin yabo wajen ci gaban wasan damben gargajiya.