Hotunan yadda aka yi yunkurin kashe Donald Trump a wurin yakin neman zabe

An wallafa

An fitar da tsohon shugaban Amurka, Donald Trump daga wurin da yake gabatar da jawabi a wani taron yakin neman zabe a garin Butler na jihar Pensylvania da ke kasar Amurka.

Wani dan bindiga ne ya bude wa tsohon shugaban wuta daga kan rufin wani gini da ke kusa da wurin taron.

Yadda jami’an tsaron farin kaya na Amurka suka zagaye Donald Trump a lokacin yakin neman zabe a garin Butler na jihar Pensylvania, ranar Asabar 13 ga watan Yulin 2024
Bayanan hoto, Yadda jami’an tsaron farin kaya na Amurka suka zagaye Donald Trump a lokacin yakin neman zabe a garin Butler na jihar Pensylvania, ranar Asabar 13 ga watan Yulin 2024
An fitar da dan takarar na Jam’iyyar Republican daga wajen taron na ranar Asabar
Bayanan hoto, An fitar da dan takarar na Jam’iyyar Republican daga wajen taron na ranar Asabar
Za a iya ganin jini a gefen fuskar Donald Trump bayan harbin
Bayanan hoto, Za a iya ganin jini a gefen fuskar Donald Trump bayan harbin

Dan takarar shugaban kasar na Jam’iyyar Republican ya duka zuwa kasa, yayin da za a iya ganin jini na zuba ta gefen fuskarsa.

Daga baya ya bayyana cewa ya ji gittawar harsashi ta kusa da fuskarsa, wanda ya shafi fatar kunnensa.

Lokacin da ake kokarin fitar da Trump daga wurin yakin neman zabe
Bayanan hoto, Lokacin da ake kokarin fitar da Trump daga wurin yakin neman zabe
Lokacin da jami’an tsaro suka zagaye Donald Trump domin ba shi kariya
Bayanan hoto, Lokacin da jami’an tsaro suka zagaye Donald Trump domin ba shi kariya
Trump ya rika daga hannunsa a lokacin da ake fitar da shi
Bayanan hoto, Trump ya rika daga hannunsa a lokacin da ake fitar da shi

Lokacin da jami’an tsaron farin kaya suka mamaye dandamalin, Trump ya daga hannunsa sama yayin da ake sauka da shi daga kan dandamali.

Dan takarar shugaban Amurna na Jam’iyyar Republican, Donald Trump
Bayanan hoto, Dan takarar shugaban Amurna na Jam’iyyar Republican, Donald Trump
Donald Trump
Donald Trump
Donald Trump

Mahalarta taron su rika kwantawa a kasa yayin da karar bindiga ke tashi, yayin da wasu suka tsere.

Wani mutum da ke wurin ya shaida wa BBC cewa ya ga wani mutum a saman rufin wani gini dauke da bindiga jim kadan kafin ya fara harbi kan tsohon shugaban kasar.

Donald Trump
Donald Trump
Wurin taron yakin neman zaben Donald Trump a Butler, Pensylvania jim kadan bayan harin da aka kai wa dan takarar shugaban kasar da bindiga
Bayanan hoto, Wurin taron yakin neman zaben Donald Trump a Butler, Pensylvania jim kadan bayan harin da aka kai wa dan takarar shugaban kasar da bindiga