Diego Maradona: Fitaccen ɗan ƙwallon Argentina cikin hotuna

Diego Maradona
Bayanan hoto, Diego Maradona - riƙe da kofin duniya da ya lashe a 1986, lokacin atisaye, tare da tsohuwar matarsa Claudia da ƴaƴansu mata Dalma da Gianina
An wallafa

Diego Maradona shahararre ne a filin ƙwallon ƙafa kuma mai janyo ce-ce-ku-ce a bayan fili.

Daga Argentina zuwa samun nasarori a Italiya, kofin duniya da kuma badaƙalar ƙwaya, ga rayuwar Maradona cikin hotuna.

Diego Maradona a 1982
Bayanan hoto, A 1982 Maradona ya fara buga wa Argentina gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Spain.
Diega Maradona da Peter Shilton Mexico 86
Bayanan hoto, Maradona na gaisawa da golan Ingila Peter Shilton kafin fafatawa a zagayen kusa da dab da ƙarshe a gasar cin kofin duniya a Mexico a 1986
Kwallon da Diego Maradona ya ci Ingila a gasar cin kofin duniya a 1986
Bayanan hoto, Ƙwallon da Maradona ya ci da hannu a ragar Ingila, kafin zura 'ƙwallon ƙarni' a Mexico 86
Diego Maradona ɗauke da kofin duniya
Bayanan hoto, An bayyana Maradona gwarzon ɗan wasa a gasar bayan taimakawa Argentina lashe kofin 1986, tare da taimakawa ƙasarsa sake zuwa zagayen ƙarshe bayan shekaru huɗu.
Diego Maradona
Bayanan hoto, Maradona ya yi suna a Napoli inda ya lashe kofin Turai na Uefa a 1989, da kofin lig guda biyu. An jingine amfani da lamba 10 domin karrama shi.
Diego Maradona a 2001
Bayanan hoto, Maradona an manyanta, hotonsa a 2001, yana fama da ƙiba da kuma tu'ammali da ƙwaya.
Lionel Messi da Diego Maradona
Bayanan hoto, Tawagar Maradona, lokacin da yana kocin Argentina yana tattaunawa da Lionel Messi a gasar cin kofin duniya a 2010 inda suka sha kashi 4-0 hannun Jamus
Diego Maradona in Russia
Bayanan hoto, Maradona riƙe da wata tuta mai ɗauke da hotonsa a wasa tsakanin Argentina da Nigeria a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha a 2018