Boris Johnson: Wane zargi ake yi wa firaministan Birtaniya kuma mece ce makomarsa?

Boris Johnson

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Darajar Firaiministan Birtaniya Boris Johnson na lilo a idon jama'a, a daidai lokacin da ake shirin wallafa wani rahoto kan zargin dabdalar da aka shirya a gidan firaministan da ke lamba 10, titin downing a daidai lokacin da ake tsakiyar annobar korona.

Tuni ƴan sanda suka ƙaddamar da bincike kan zargin saɓa dokokin korona, haka kuma akwai yiwuwar za a iya tilasta wa firaiministan ya yi murabus daga muƙaminsa idan aka gano ya yi wa majalisa ƙarya.

Tun bayan da Mista Johnson ya zama firaiministan Birtaniya, an ga abubuwa iri-iri.

A mulkinsa na sama da shekara biyu, ya jagoranci fitar ƙasar daga Tarayyar Turai - ya jagoranci ƙasar kuma a lokacin annobar korona da ta addabi duniya haka kuma ya fuskanci tawaye daga muƙarrabansa na kusa wasu kuma suka yi murabus.

A yanzu abu na baya-bayan nan da ake magana a kai shi ne batun shirya dabdalar da ya yi wanda hakan ya yi sanadin tsohon magajin garin Birtaniya ya kusa rasa muƙaminsa.

Amma mene ne takamaimai ake zarginsa da aikatawa?

.

Asalin hoton, PA Media

Wace dabdala ce?

Kamar yadda rahotanni suka bayyana, aƙalla sau 17 aka yi taro ko dai a Titin Downing wanda a nan ne firaiminista yake zama kuma yake aiki - ko kuma a wasu sassan ma'aikatun gwamnati a lokacin da ake tsakiyar annobar korona.

Birtaniya na cikin dokar kulle a matakai daban-daban a lokacin da aka yi waɗannan shagulgula, inda a lokacin gwamnatin ta haramta taruwar sama da mutum biyu tare da hana tarurruka.

Kusan mutum 100 aka gayyata a wata dabdala da ake bayar da tazara wadda kowa ya yi guzurin barasarsa inda aka yi shagalin a Titin Downing a Mayun 2020.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa Boris Johnson da masoyiyarsa, Carrie Symonds na daga cikin mutum 30 waɗanda suka halarci bikin. Firaiministan ya bayyana cewa ya halarci bikin na mintuna 25, sai dai a fakaice ya ɗauka dabdalar ta aiki ce.

Murnar zagayowar ranar haihuwa

Bayan wata ɗaya, an bayar da rahoton cewa an yi bikin murnar zagayowar ranar haihuwar firaiminista a Titin Downing inda aka yanka kek. Ma'aikatan ofishin firaiministan sun bayyana cewa ba a shafe mintuna goma ba a wajen bikin ba.

..

Asalin hoton, Andrew Parsons / No 10 Downing Street

A lokacin da Landan ta shiga cikin doka mafi tsanani ta korona a Disambar 2020, an yi zargin cewa an gudanar da bukukuwa daban-daban ciki har da wani taro da aka yi ba bisa ƙa'ida ba a hedikwatar jam'iyyar masu ra'ayin ƴan mazan jiya.

A baya-bayan nan, an bayyana cewa ma'aikatan fadar ofishin firaiministan sun gudanar da dabdala har sau biyu a ranar 16 ga watan Afrilu a jajibirin jana'izar Yarima Philip. A lokacin jana'izar, an nuna sarauniya na zaune ita kaɗai inda take bin dokokin korona.

Ƙasar na cikin jimami a lokacin inda har aka rage tsawon tutocin ƙasar.

Johnson bai halarci duka dabdalolin da aka yi zargin yi ba a ranar 16 ga watan Afrilu.

.

Asalin hoton, PA Media

Me jama'a ke cewa kan wannan lamari?

Firaiminista ya sha caccaka matuƙa kan zargin dabdalolin da aka shirya kuma shugaban ƴan adawa a majalisa Sir Keir Starmer na yawan caccakarsa.

Wadda wannan lamari ya soma shafa ita ce sakatariyar watsa labarai ta gwamnatin wato Allegra Stratton.

A lokacin da aka soma samun waɗannan rahotannin a watan Disamba, bayan mako guda da ofishin firaiminista ya musanta cewa babu dabdalar da aka yi, an saki wani bidiyo da ke nuna yadda Stratton ke bitar yadda za ta amsa tambayoyi daga ƴan jarida.

Ta ajiye aikinta tare da fitar da sanarwa cikin baƙin ciki washe gari.

A dai cikin watan da ta yti murabus, jam'iyyar masu ra'ayin ƴan mazan jiya sun rasa kujera mai muihimmanci a North Shropshire inda masu sassaucin ra'ayi suka karɓi kujerar a yayin wani zaɓe da ya jawo ce-ce-ku-ce.

A farkon wannan wata ne wani ɗan majalisa mai ra'ayin ƴan mazan jiya Christian Wakeford ya sanar da komawarsa Jam'iyyar Labour, duk da cewa komawar tasa wurin ƴan adawa tun kafin dabdalar ne.

..

Asalin hoton, PA Media

Kira ga firaiminista ya tafi

Ƴan majalisa da dama daga ciki da wajen jam'iyyar ƴan mazan jiya na kira ga firaiminista da ya yi murabus, inda caccakar mafi girma ta fi fitowa daga David Davis wanda shi ma mai ra'ayin ƴan mazan jiya ne.

Ya bayar da misali da wani ɗan majalisa daga 1940 wanda ya yi kira ga firaiminista Neville Chamberlain da ya yi murabus bayan rashin nasara da aka samu sau biyu a lokacin yaƙin duniya na biyu.

Davis ya bayyana cewa: " Ka zauna kan wannan kujera lokaci mai tsawo. don Allah ka tafi."

Duka kallo ya koma kan Westminster a daidai lokacin da kowa yake jiran a wallafa rahoto kan binciken da ake yi na zargin saɓa wasu ƙa'idoji, wanda wata babbar ma'aikaciyar gwamnati Sue Gray ke yi.

Wace ce Sue Gray?

Sue Gray

Asalin hoton, PA Media

Sue Gray a halin yanzu ita ce babbar sakatariyar gwamnati ta biyu a majalisar ministoci inda take ƙarƙashin babban jami'in gwamnati na Birtaniya Simon Case.

Tun da farko dai Mista Case ne jagora a wajen binciken. Sai dai ya ceci kansa inda ya miƙa wa Gray ragamar binciken bayan an gano cewa ɗaya daga cikin dabdalar Kirisimetin da aka yi, an yi ta ne a ofishinsa a 2020.

Gray za ta yi duba kan yanayin waɗannan taruka, ciki har da gano waɗanda suka halarce su.

Ana sa ran rahoton zai bayar da bayanai dalla-dalla kan abin da ya faru. Ba hakan na nufin ko lallai za ta ce an saɓa dokoki ba.

Bincike ne na cikin gida, ba wai mai zaman kansa ba. Ofishin firaiminista ne ya bayar da umarnin yin hakan tare da fayyace me za a yi. Ana buƙatar Gray kada ta saka son rai a binciken.