Yayin da nasarar da Moroko ta samu na kaiwa zagayen kusa da na ƙarshe a
Qatar abin mamaki ne, wannan tawagar da ke fafatawa a Amurka ta fi ƙarfin a yi
mata kallon ta ƴan wasa marasa ƙarfi.
A ranar Asabar da ta gabata, zakarun gasar ƙasashen Afirka (wanda
Senegal ke jiran ɗaukaka ƙara bayan wasan ƙarshe mai cike da ce-ce-ku-ce a
watan Janairu), sun sanya ƴan wasa huɗu ne kacal daga cikin waɗanda suka sha
kashi a wasan kusa da na ƙarshe da suka kara da Faransa shekaru huɗu da suka
gabata.
Suna wasa da kuzari da kuma ƙarfin hali, kuma za su zama ƙalubale mafi
tsanani da Faransa ta fuskanta zuwa yanzu a gasar bana.
A ɓangaren ƙasar da ta zo ta biyu a gasar 2022, uku ne kawai daga cikin
ƴan wasan da suka buga wasan kusa da na ƙarshe suka fara wasan da Faransar ta
yi nasara kan Paraguay a ranar Asabar. Fitowar William Saliba, ɗan wasan
tsakiya kuma gwarzon ɗan wasa Michael Olise, suna daga cikin sabbin abubuwan da
Didier Deschamps ya yi tun daga lokacin.
Kylian Mbappe har yanzu shi ne gwarzon ɗan wasa kuma zai ci gaba da
ƙoƙarinsa na doke Lionel Messi na Argentina wajen samun kyautar takalmin zinare
da kuma lambar gwarzon ɗan wasan da ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar cin
kofin duniya.
Abin la'akari a nan shi ne rabin
adadin rashin nasarar da Faransa ta yi a gasar cin kofin duniya a cikin wannan
ƙarnin sun zo ne a hannun ƙasashen Afrika (Uku daga cikin shida).
Moroko ba ta yi rashin nasara ba cikin wasanni 34 a jere da ta fafata a
baya ba, amma ba ta taɓa nasara kan Faransa ba wadda ta lashe wasannin bakwai a
jere, yayin da ta yi nasara a wasanni 11 cikin 12 da ta buga.