An shiga kwana 100 kafin babban zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya
Najeriya ta shiga kwanaki 100 kafin babban zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana sabon kundin masu zaɓe da aka faɗaɗa, tare da shirye-shiryen amfani da sabbin fasahohi domin ƙara inganta sahihancin zaɓen.
A wani taron masu ruwa da tsaki na ƙasa da taron manema labarai da aka gudanar a Abuja yau Talata, shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya sanar cewa adadin mutanen da ke cikin Kundin Masu Zaɓen ya haura miliyan 103, bayan kammala aikin rajistar masu zaɓen mai mataki uku da kuma tantance bayanan masu zaɓen.
Wannan adadi ya nuna ƙarin masu zaɓe kusan miliyan 10, idan aka kwatanta da sama da mutum miliyan 93 da suka yi rajista a babban zaɓen 2023. A aikin rajistar baya-bayan nan kaɗai, sabbin masu zaɓe 10,772,421 ne suka yi rajista, waɗanda ke jiran tantancewar ƙarshe ta tsarin tantance bayanan masu zaɓe daga INEC.
Jihar Lagos ce ke da mafi yawan masu rajistar zaɓen inda take da kimanin miliyan bakwai, sai Kano mai miliyan shida. Kaduna na da kimanin miliyan huɗu, yayin da jihohin Katsina, Rivers, Oyo, Delta, Benue, Ogun da Bauchi ke da kimanin masu zaɓe miliyan uku kowannensu, a cewar alkaluman INEC.
A ranar Juma’a 9 ga watan da muke ciki na Oktoba ne za a fara rabon katunan zaɓe na dindindin (PVC) a faɗin ƙasar inda hukumar ke kira ga masu zaɓe su karɓi katunansu a kan lokaci.
Domin tafiyar da zaɓen da yawan masu kaɗa ƙuri’a ya ƙaru, Amupitan ya ce INEC ta sayi sabbin na’urorin tantance masu zaɓe 57,000. Haka kuma, an inganta manhajojin da ake da su.
Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa jam’iyyun siyasa 18 ne za su fafata a zaɓen shugaban ƙasar, inda hukumar ta sanya ’yan takarar shugaban ƙasa 18 a jerin ƴantakarar da ta amincewa su shiga zaɓen da ke ƙunshe da, maza 16 da mata biyu.
Ya ce hukumar ta kuma wallafa sunayen ’yan takarar gwamna da mataimakansu domin zaɓen gwamnoni da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairun 2027.
Hukumar za ta kuma fara amfani da wani ingantaccen tsarin aika sakamakon zaɓe ta intanet, wanda zai mayar da takardun sakamakon zaɓe zuwa tsarin dijital, ya tabbatar da sahihancinsu, sannan ya tura su zuwa shafin tattara sakamakon zaɓe na IReV.
INEC ta ce tana aiki tare da ƙwararrun kamfanonin fasaha na ƙasashen waje kan amfani da fasahar AI wajen gano kurakurai ko abubuwan da ba su dace ba, da kuma inganta tsaron intanet.
A cewar hukumar, manufar ita ce ƙarfafa tantance masu zaɓe da aika sakamakon zaɓe, rage damar yin maguɗi, da kuma hanzarta sanar da sakamakon zaɓe. Hukumar tana kuma son tabbatar da cewa an fara kaɗa ƙuri’a a rumfunan zaɓe a lokaci guda.
Sai dai burin amfani da waɗannan fasahohi na haifar da shakku, musamman ganin cewa zaɓen zai shafi masu rajista sama da miliyan 100.
’Yan Najeriya da dama na son sanin yadda INEC za ta rarraba dubban na’urorin BVAS da tura ma’aikatan zaɓe a faɗin ƙasar, tare da tabbatar da cewa an buɗe rumfunan zaɓe a kan lokaci.
Babban abin damuwa kuma shi ne yadda za a gudanar da zaɓen a yankunan da ke fama da rashin tsaro, Rashin kyawun hanyoyi, ƙarancin wutar lantarki ko raunin hanyoyin sadarwa. Akwai kuma tambayar matakan da hukumar za ta ɗauka idan sabbin tsare-tsaren dijital suka samu matsala a ranar zaɓe.

























